ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 61 to 70

Jabeer yace wannan haka yake, gobe zan samu Kawu da maganar abinda yace zakuji, Yaya dole mu fara bincike a b’oye, sai mun had’a komai kafin mu fara aiki. 

Ra’eez yace ina ganin shari’ar su Naseer zamu fara, itace zata tono waccan shari’ar. Rafeek yace haka ne, domin muna da d’an wani abu akan shari’ar Naseer, duk da itama ba mai kwari bace, domin d’ayan abokinsu ya mutu, ko yana nan su biyu bazasu bada sheda ba, ko sun bada baza tayi amfani ba saboda abaki take, kunga anan ma sai mun zurfafa bincike. 

Jabeer yace Adnan kana da hoton ku alokacin kuna makaranta? Adnan yace ina da su sosai ma. Jabeer yace Fawwaz bazai iya k’aryata abotar ku ba, kana da labarin shugaban makarantar ku? Adnan yace e amma yanzu baya makarantar ya aje aiki, sai dai nasan gidanshi dan d’anshi abokina ne. 

Rafeek yace turk’ashi, yanzu ya za’ayi musamu ganawa dashi bana so abokin ka yayi tunanin kayi masa rashin mutunci idan yaji kana dasa hannu wajen saka Babanshi cikin masu laifi. 

Adnan yace a wannan gab’ar babu batun abotaka, tunda har na amince zan tsaya a yanke ma babban aminina na da hukunci babu wanda zan iya rufa ma asiri, domin shi Nabeel jami’a mukayi dashi, shikuwa Fawwaz akwai shakuwa atsakanin mu, dan haka ku bani lokaci insha Allahu Nabeel zai bamu goyon baya, duk da Babanshi ya aikata laifi amma dole a hukuntashi. 

Rafeek yace mungode sosai, kuma zamu tafiyar da komai yanda ya kamata, idan komai ya kammala zasu san gata mukayi masu domin sun huta amsar hukunci a lahira.

Tashi Adnan yayi yana fad’in zan wuce gida dare yayi. Rafeek yace muje na aje ka zamuyi waya. Hannu ya bama su Jabeer suna ta masa godiya. Rafeek yace zuwa gobe zan fara binciken mutanan da sukayi tarayya a waccan shari’ar. 

Jabeer yace nima a goben zan samu Kawu da maganar. Ra’eez yace Allah ya kaimu, nima gobe zan koma aiki. Tashi sukayi suka rakasu kafin suka dawo. 

Bayan sun kwanta wayar Ra’eez tayi k’ara, yana dubawa yaga Raheena ce, duba agogo yayi yaga har sha biyu tayi, tsaki yaja yana fad’in bana son rashin hankali wallahi. 

Murmushi Jabeer yayi yana fad’in bacci ta kasayi shiyasa ta kira ka. Kashe wayar yayi gaba d’aya yana fad’in sai tayi da wani kuma. 

Jabeer yace Ra’eez na Raheena, wallahi kuna bani dariya, tun farko na fad’a maka ka rabu da ita gashinan tana baka ciwon kai. Tsaki Ra’eez yayi yana fad’in daga ita har Iyayen ta basu da kai, sufa a haukansu jiran yan gidan mu suke suje neman aure, har kayan d’aki fa sun siyo. 

Gyara kwanciya Jabeer yayi yana fad’in ka bari da Allah? Ra’eez yace wallahi kuwa, ba na fad’a maka zasuje Dubai ba a week end d’in da naje Kano ba. 

Jabeer yace haka ne. Ra’eez yace wallahi jiya take fad’a mun wai kayan suna hanya, nifa na fara tausaya mata ma. Jabeer yace da nace maka ina tausayinta meka fad’a mun? Nifa aganina bekamata kayi ramuwar gayya akanta ba, duk da an zalunceka amma bata da laifi, idan mukayi haka kamar Allah zai kama mu ko kuma ya hana mu samun wani abun da muke so. 

Ajiyar zuciya Ra’eez ya saki yana fad’in b’acin rai ne yaso ya jefani cikin damuwa, tabbas Raheena bata cancanci nayi mata haka ba, amma insha Allahu a yanzu zan fad’a mata tayi hakuri kawai. 

Jabeer yace baza’ayi haka ba, Raheena tana maka so mai yawa, idan ka fito fili ka fad’a mata abinda yake ranka zata iya fad’awa wani hali, ina ganin abi komai a hankali. 

Ra’eez yace shikenan nasan abinda zan rubuta mata. Wayarsa ya jawo ya kunna ya fara rubutu. Jabeer da yake gefenshi yace kafin ka tura ka bani na gani. Ra’eez yace sa ido. Jabeer yace gaskiya dai. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in bara na gama to. 

Mik’a masa wayar yayi yana fad’in bance kamun gyara ba. Amsa yayi yana fad’in sai dai idan baka kwafsaba, dan na lura da kai haushin Mahaifinta yasa ka tsani kowa. 

Jinjina kai yayi yana fad’in ba laifi kayi amfani da kalamai masu ma’ana, sai muce Allah yasa mata dangana. Ra’eez yace amin. 

Shuru sukayi gaba d’ayansu bayan sun tura sakon. Jabeer! Ra’eez ya kirashi a hankali, be amsa ba sai juyowa da yayi yana fuskantarshi. 

Mai zai hana ka nemi auren Ra… Kada ma ka k’arasa, Jabeer ya fad’a. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in wallahi tausayinta nakeji. 

To kayi ta biyu da ita mana. Jabeer yace yana harararshi. Dariya Ra’eez yayi yana fad’in haba abokina, yanzu da bakin ka kake fad’in nayima Pretty kishiya. 

Jabeer yace ai naji kana wani kilibibin kana tausayin ta, idan har bazaka iya aurenta ba damme zaka lak’aba mani ita? Ra’eez yace saboda naga babu soyayyar kowa a zuciyar ka. 

Tsaki Jabeer yayi yana fad’in to kama dena wannan maganar, babu abinda zanyi da ita, na fad’a maka bazan iya soyayya da wacce ta mutu akan wani ba, wanin ma kai, haka kawai idan na aureta data ganka sai tsohon tsumin soyayyarka ya tasar mata. 

Dariya Ra’eez yasa yana fad’in kawai kace kishi kake malan, bakomai Allah zai bata wani. Jabeer yace hakan ma yafi, amma kada ka janye mata lokaci guda kamar yanda ka rubuta kaga baka fito fili kace mata baka sonta ba. Ra’eez yace kada ka damu. 

*** ***

*Raheena ina so ki tsaida hankalin ki wajen karanta abinda na rubuta maki, bana so kiyi mani wata fassara, dalilin rubuta maki wannan sakon saboda naga kunyi nisa akan abinda zuciyar ku take tunani shiyasa naga ya dace nayi maki magana dan kada ku zurfafa, a tunanin ku ayi bikin ki nan da wani lokaci, domin naji kina fad’ar kunje siyayyar kayan d’aki, idan baki manta ba na fad’a maki ki jirani zanyi tunani akan soyayyar ki, kuma har yanzu ban gama yanke hukunci akai ba, domin ko Iyayena banyi maganar dasu ba, kuma ni gaskiya ba yanzu zanyi aure ba dan akwai abubuwa masu muhimmanci akaina, kuma bazan tab’a yin aure ba har sai na kammala su, shiyasa nace zan fad’a maki gaskiya dan naga kamar kina son yin aure da wuri, ina fatan zaki fahimce ni dan bana son a takura mani dan ban shirya aure yanzu ba, dan haka kudena maganar yin aure ayanzu. Nagode.*

Ta maimaita sakon yafi a kirga, zufa kawai take zubo mata, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, hannu tasa ta goge tana fad’in me D yake nufi da wannan sakon? Gashi dai bece mani baya sona ba, *Dama can kuma be tab’a fad’a maki kalmar so ba.* wata zuciyar ta kwab’eta. 

Gyara zama tayi tana zurfafa cikin tunani, tabbas sunyi gaggawa wajen aminta da maganar aurenta dashi, amma tunda yace akwai abinda yake gabansa zata mashi uzuri, kuma bazata fad’ama kowa wannan maganar ba, sai dai zata nuna masu abar maganar aurenta zuwa wani lokaci, idan ya kammala komai tasan zai dawo gareta. 

Murmushi ta saki tana fad’in zan jiraka, bazan tab’a bari naji kunya a wajen k’awaye na ba, bara naje muyi magana da Momy. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

3⃣6️⃣

Ban gane abar maganar auren ki sai zuwa gaba ba? Matsowa tayi tana fad’in Momy Ra’eez yace beyi magana da Iyayenshi ba saboda akwai wani aiki mai muhimmanci da yakeso ya kammala kuma baya so maganar aurenshi tasa yaki maida hankali akan aikin, kinga babban biki ne za’ayi dole yana buk’atar natsuwa, nima bana so ace za’ayi bikin mu kuma yana wani aikin sai kiga bikin beyi dad’i ba, kuma tunda yace aiki ne mai muhimmanci nasan ba k’aramun abu bane, kinsan kuma yanayin aikinsu dole yana buk’atar natsuwa da zurfafa tunani, shiyasa yace a bari harya kammala aikinsa kafin yazo ayi magana. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button