ALKALI NE Page 61 to 70

Murmushi Momy ta saki tana fad’in yanzu naji batu, ai na d’auka ko wata matsala kuka samu, haba dan wannan ai bakomai, kaya ne an riga ansiyo su, idan ma baki son su zuwa lokacin auren za’a iya siyar dasu aje asiyo maki wasu dan bancika son amfani da tsofaffin yayi ba.
Murmushi Raheena tayi tana fad’in yanzu Momy zaku iya sake mani wasu kayan? Momy tace to me zamuyi da kud’in? Ke d’aya muke da ita shiyasa muke so muyi maki abinda ko d’iyar shugaban k’asa iya abinda za’a mata kenan, dan haka idan har aikin ya jashi dogon lokaci dole asiyar da kayan idan lokacin bikin yayi asiyo maki wasu.
Raheena tace nagode Momy, sai kiyi ma Dady bayani. Babu wani bayani da za’a mun domin naji komai. Alhaji Barau ya fad’a yana sakkowa daga bene. Murmushi Momy tayi tana fad’in ashe har ka gama shiryawa? Zama yayi yana fad’in tunda kin gudu wajen d’iyar ki dole na shirya ni d’aya.
Tashi Raheena tayi tana fad’in Dady ayi hak’uri bazata sake ba. Dariya sukasa gaba d’aya. Alhaji Barau yace bakomai naji duk abinda kuka fad’a, tunda dai yana sonta ai babu damuwa, ni dama ban matsa sai Raheena tayi aure da wuri ba dan nima bangaji da ita ba, dan haka zamu jirashi ya kammala abinda yakeyi.
Momy tace kila ma kaine ka bashi aiki mai wahala ko? Alhaji Barau yace babu ruwana, kila dai a wani wajen zaiyi aiki amma ni bana bashi aiki mai wahala. Momy tace to Allah ya nuna mana lokacin. Yace amin.
**** ***
Bayan sun tashi daga aiki Jabeer yace zaije wajen Kawu akan maganar su. Ra’eez yace bakomai zan wuce wajen Kawu daga can na biya wajen Ummu. Jabeer yace ka gaishe su mu had’e gidan Mama. Ra’eez yace ka gaishe dasu Mamy.
****
Hannu Kawun Jabeer yasa a hankali ya zare glass d’in idonshi, ido ya kurama Jabeer jin abinda yazo dashi. Kauda kai yayi yana jinjina kai.
Shiru Jabeer yayi yana addu’ar Allah yasa Kawun ya amince ya taimaka masu. Gyaran murya Kawu yayi yana fad’in Allah mai iko, lallai duniya da girma take, wai akace d’an hakkin daka raina wata rana zai iya tsone maka ido.
Kallon Jabeer yayi yana fad’in wai kana nufin tare kuke aiki da Yaron marigayi Alhaji Maiwada? Jabeer yace kwarai kuwa Kawu, yanzu haka shine babban gwarzo a kotun mu.
Kawu yace naga alama daga labarin shari’ar da kace yayi, wannan shine ikon Allah, ashe dama irin wannan ranar zata zo? Ashe jinin Alhaji Maiwada ba zai zuba abanza ba? Ashe Malan Sani zai samu adalci? Ashe wad’an can azzaluman zasu fuskanci hukunci dai-dai dasu? Lallai Jabeer ka zo da magana mai matuk’ar amfani, ayanzu ne zanyi ramuwar abinda na gazayi ashekarun baya, ayanzu ne zan nuna masu Brr. Barau bakomai ne kud’i yake badawa ba, tabbas anzo wajen, dan haka kaje ka fad’ama Ra’eez, da Rafeek ina son ganin su ko zuwa dare ne.
Cike da farin ciki Jabeer yace angama Kawu. Kawu yace bana son wannan maganar ta fita, shiyasa daka fara fad’a mani nace maka muzo mota, inaso komai ya tafi yanda ya kamata, insha Allahu zan shirya yanda komai zai kasance, sai Alhaji Barau yaji kunyar da bai tab’a jinta ba, sai ya gwammace k’asa ta tsage ya shige ya huta, kaje ka fad’a masu.
Godiya Jabeer yayi ma Kawu ya tashi ya tafi cike da farin ciki, tun alokacin yayi masu waya ya fad’a masu sakon Kawu, sosai sukayi murna.
****
Rafeek ne ya fito daga ofishin ‘yan sanda tare da wani d’an sanda, har bakin motarshi suka k’arasa. Hannu Rafeek ya bashi yana fad’in nagode *Usman* Allah ya bar zumunci.
Murmushi wanda aka kira da Usman yayi yana fad’in haba babu komai, ai wannan taimakon juna ne, duk da baka fad’a mani dalilin da yasa kake neman Alhaji Bello Kabeer ba.
Rafeek yace bakomai fa, akwai wani yaro da yake son shiga aikin d’an sanda shine nace masa zan taimaka masa, to da nayi bincike sai na gano a ofis d’in ku yayi aiki harya kai babban matsayin Kwamishina na ‘yan sanda ayanzu, shine nace zan fara zuwa wajen ka na fara jin labarinshi kafin nasan ta yanda zanje mashi.
Usman yace indai zaka bud’e masa bakin aljihu baka da matsala dan ‘Yallab’ai akwai son naira. Rafeek yace babu damuwa tunda dai kayi mani kwatancen gidanshi insha Allahu zan sameshi Allah yasa mudace.
Usman yace amin. Sallama sukayi yashiga mota. Tafiya yake yana tunanin ta yanda zai fara b’ulloma Alhaji Bello Kabir, amma tunda ya ganoshi zai shirya masu fira ta haka zai san yanda yayi ya tab’o mashi maganar wannan shari’ar.
Agogo ya duba sai yaga lokaci ya tafi, yaso ya biya asibitin da Dr. Aliyu Sani yayi aiki yaji ko yana wajen har yanzu ko kuma ya k’ara matsayi, ajiyar zuciya ya saki, dole ya bari sai gobe saboda neman da Kawu yake masu.
***
Daga wajen Ummunsa gidan Mama ya wuce, acan ya iske Jabeer suna ta fira da Mama. Bayan sun gaisa suka wuce masallaci, bayan sun idar da sallah suka zauna Rumaisa ta kawo masu abinci.
Kallon Jabeer yayi yana fad’in nifa jinake akoshe nake duk na k’osa muje wajen Kawu, ina son naji ana bani labarin Abbuna. Murmushi Jabeer yayi cike da tausayin Ra’eez.
Wayar Rafeek ce tashigo, yana d’auka ya fad’a mashi suna gidan Mama. Rafeek yace dama yanzu na fito bara na k’araso mugaisa da Mama. Ra’eez yace shikenan sai kazo.
Jabeer yace gaskiya Yaya yana da kirki. Ra’eez yace shiyasa nace maka tunda muka had’u naji ya kwanta mani, kasan bana saurin yarda da mutane amma akanshi naji na yarda dashi.
Jabeer yace wai jiya inaso na tambayeka ka d’auki bayanin Adnan kuwa? Dafe kai Ra’eez yayi yana fad’in wallahi na manta, kuma kasan nace maka daga yanzu duk wata sheda da zamu samu sai mun rik’a d’aukarta gudun yaudarar mutane.
Jabeer yace Allah yasa kada ya yaudare mu, duk da naga alamun gaskiya atare dashi amma kasan halin yau, zuciya bata da k’ashi babu ta yanda bazata iya canzawa ba, sai dai muyi fatan Allah yasa ya cika alk’awarinsa.
Ra’eez yace amin, amma da ya gama damu idan ya kasa zuwa ya bada shedar abinda ya sani. Jabeer yace kaga sai mu kiyaye. Wayar Ra’eez ce tayi k’ara, saurin tashi yayi ya fita yana fad’in Yaya ne.
Sosai Mama taji dad’in bayanin da Rafeek yayi masu akan gano Alhaji Bello Kabir wanda yake inspector a lokacin da akayi shari’ar su Malan Sani, godiya tashiga yimasa tana saka masa albarka.
Rafeek yace haba Mama babu komai, insha Allahu wannan karon mune da nasara. Mama tace Allah yasa. Abinci tasa akawo masa yace daga gida yake, kallonsu Jabeer yayi yace muje kada Kawu yajira mu. Sallama sukayi ma Mama suka fita.
**** ***
Ido Kawu ya tsurama Ra’eez, tabbas ga kamanninsa da Mahaifinsa a fuskarshi, amma sai wanda ya san Alhaji Maiwada zai iya sheda hakan, kuma sai ka k’arema Ra’eez kallo zaka gano kamannin su, lallai Alhaji Barau be yima Ra’eez kallon tsab ba da tuni ya gano kamannin Mahaifinsa.
Gyara zama yayi yana fad’in sannu kaji Ra’eez, tabbas kai d’in Kainuwa ne dashen Allah, domin Allah yasan dalilin da yasa ya bar su Alhaji Barau har yanzu araye, haka kuma ya barka kaida Malan Sani da Ummunka araye, domin ya tsara yanda ikonsa zai kasance, hakika Mahaifinka yayi mutuwar cutarwa, domin wad’an da suka kashe shi basu da imani ko kad’an, amma ayanzu zasu gane kuren su.
Kayi hak’uri na kasa tsayama Mahaifinka, duk da alokacin nasan su Alhaji Barau suna da sa hannu a kisanshi amma bani da ikon magana saboda bani da hujjar da zan nuna, ita kuma kotu hujja take so, amma ayanzu dana ganka sai naji gashi can mun cinye shari’ar, da izinin Allah zamu samo hujjar da zata ruguzasu gaba d’aya.