ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 61 to 70

Hannu Ra’eez yasa ya goge hawayen da suka zubo mashi, duk’ar da kai yayi yana fad’in babu komai Kawu, Allah ya rubuta dole sai hakan ta kasance, ko ka bada hujjar baza tayi tasiri ba alokacin tunda Allah ya tsara haka, amma ayanzu zamu samota Kawu. 

Jinjina kai yayi yana fad’in dole amaido da shari’ar baya, domin ita shari’a bata tsufa, koda ta kai shekaru hamsin za’a iya maidota, kuma awannan kotu za’a gabatar da ita, dan haka zan shirya yanda komai zai kasance, koda Alkali Barau yace bazai amshi shari’ar ba za’ayi masa magana kuma dole ya amsheta. 

Rafeek yace mungode Kawu, kuma zamu k’arasa nemo sauran mutanan da suka tsaya a waccan shari’ar matuk’ar suna raye. Kawu yace gashi kusa mani lambar ku, daga yau inaso ku kasance ashirye, domin zaku fara aiki mai had’ari, dan mutanan da zaku kara dasu azzalumai ne, zasu iya komai saboda rufin asirin su. 

Bayan sun saka mashi lambar sukayi masa sallama suna ta godiya suka tafi. A can suka rabu da Rafeek yayi gida suma suka wuce gida saboda dare yayi. 

***

Ina jinka Lucky. Gyara tsayuwa Lucky yayi hannunshi nad’e a kirji yana fad’in ‘Yallab’ai gobe ne za’a kawo kayan Alhaji Marusan, kuma nasa yarana su ankare baza’a samu matsala ba. 

Ruwa Alhaji Barau yasha yana fad’in Lucky na sanka da son kud’i, bana so ka fad’ama Alhaji Marusa komai dan nasan zakayi tunanin zai iya k’ara maka kud’i idan ka fad’a masa, mu ba kud’in bane suka dame mu, yaudara da cin amanar da yayi mana muke so mu nuna masa iyakarsa, kasan dai daga ni har Mr. Kallah bamu da zalamar kud’i, wannan aikin idan har ka yishi yanda ya kamata kana da kaso mai tsoka, kaga dai yanzu ka manyanta, aiki da yawa sai dai kasa yaranka suyi, dan haka ina so wannan ya zama sirri, kamar yanda nace ku kwace kayan kuma ku kashe masu d’aukar kayan zakaga abinda zan saka maka dashi. 

Murmushi Lucky yayi yana fad’in Alhaji baka da matsala, wannan harka mun dad’e muna yinta daku, kuma ka dena tunanin zan koma wajen Alhaji Marusa domin shi d’in ba mai alk’awari bane, kanshi kawai ya sani, kafin ku shi muka sani ni da abokina Peter, amma saboda cin amana da son kud’i irin na Alhaji Marusa daga abokina yayi masa kuskure d’aya yasa aka kashe shi, har yanzu ina da haushin wannan abun, dan haka zanyi maku aiki koda bazaku biya ni ba, domin nasan Alhaji Marusa ya zuba makudan kud’i a wannan harkar, matuk’ar ya rasa wad’an nan kayan zai shiga tashin hankali, sannan hukuncina na farko da zanyi mashi nasa babban yarona yaje cikin dare ya kona mani babban store d’inshi. 

Dariya Alhaji Barau yasa yana fad’in Mr. Kallah kaji mutumin ka ko? Mr. Kallah yace lallai Lucky ka d’ebo da zafi, ayi masa hakuri yaji da wannan asarar ma. Alhaji Barau yace aifa kai har yanzu bazaka canza hali ba, kada kamanta amanar mu yaci, tare muke kashewa mu rufe amma yau saboda harkar k’aruwa tazo shine yaci amanar mu, dan haka ka bari shima anuna masa iyakarsa, ganin yana da kud’i yasa yake abinda yaga dama, idan ya fara shin-shino karayar arziki kaga dole ya dawo k’asan mu. 

Mr. Kallah yace shikenan yanda kace babban Alkali. Dariya sukasa Alhaji Barau yace zaka iya tafiya Lucky sai munji daga gareka. Lucky yace nagode Alhaji. 

Yana fita Mr. Kallah yace yanzu kai ka yarda dashi? Alhaji Barau yace shiyasa ai na zab’eshi saboda nasan yana da haushin Alhaji Marusa akan kisan abokinsa, kaga kuwa bazai tab’a komawa bayanshi ba.

 Mr. Kallah yace zaiji idan cin amana tana da dad’i, kuma zamu nuna mashi munshiga tashin hankali. Alhaji Barau yace da masu ilimi fa yake tare wad’an da suka goga da mutane, duka nawa iliminshi yake, meya sani a harkar duniya, kabarshi zamu nuna mashi muma munyi asara. Mr. Kallah yace Alhaji Barau a kiyaye ka. Dariya sukasa. 

**** ***

Wai Adnan kayi shiru bayan kuma akwai magana abakin ka. Murmushi Adnan yayi yana fad’in bakomai kawai wani abu na gani d’azu daya tada mani wani tsohon ciwo da yake zuciyata shekaru masu yawa da suka wuce. 

Nabeel yace lallai agaisheka, taya zan iya aje abu araina har na wasu shekaru masu yawa, kaganni nan ko b’ata mani rai akayi baya wuce kwana biyu yawuce, amma kuma bansan wane irin ciwo bane aranka, kasan wani ciwon sai mutum ya mutu dashi be manta ba. 

Adnan yace d’azu muka had’u da Yayan wani abokin mu da aka kashe lokacin muna aji shidda a secondary, rabona dashi tunda mukaje masu gaisuwa, saboda yasan nine babban abokinsa yasa da muka had’u d’azu muka zauna muna ta fira hada firar abokina mukayi bakaji yanda jikina ya mutu ba, gaba d’aya sai mutuwar ta dawo mani sabuwa musamman da naga yana kuka, kuma yake fad’a mani har yanzu Mahaifiyarsu bata warke ba akan ciwon daya sameta alokacin da aka kawo mata gawar d’anta, wannan abun shine ya tada mani hankali sosai. 

Nabeel yace Allah sarki, amma basu shigar da k’ara ba ne? Adnan yace basu shigar ba. Nabeel yace da sun sani sun shigar da k’ara, kasan wani lokacin idan aka kashe maka naka matuk’ar an yanke ma wanda yayi kisan hukunci kana jin sauki a zuciyarka domin ka rage wani abun. 

Adnan yace taya zasu shigar da k’ara bayan an juyar da abun, kasan fa ita shari’a sai da shedu take amfani, domin kisan a makarantar mu akayi ta amma sai aka gano gawar abokina a wajen gari, alokacin ma Abban ka ne shugaban makarantar. 

 Nabeel yace a kings college ko? Adnan yace nan fa. Nabeel yace tabbas acan Abbah yayi aiki ashe kayi karatu ak’asanshi? Adnan yace sosai kuwa, ai Abbanka beda wasa, nayi mamaki alokacin da aka kashe Farouk da aka fita da gawarsa kuma be tsananta bincike ba. Nabeel yace dan Allah bani labarin abinda ya faru. 

Adnan yace abinda na sani ance a makaranta aka kashe shi, domin akwai wanda yaga lokacin da akayi kisan kuma har d’auka yayi, sai dai kuma daga baya aka samu gawarsa a wajen gari sannan yaron daya d’auki shedar shima aka kashe shi, kuma shedar ta b’ace, mamakin da nayi duk zafin Abbanka da iya aikinsa amma beyi komai ba, daga baya kuma nayi tunanin kila besan a makaranta aka kashe shi ba. 

Girgiza kai Nabeel yayi yana fad’in duk da haka Adnan ya kamata ace anyi bincike koda da gaske ba’a makarantar aka kashe shi ba amatsayin Abbah na shugaban makaranta ya kamata ace yayi ruwa da tsaki wajen nemawa Farouk hakkinsa. 

Murmushi Adnan yayi yana fad’in Nabeel kenan, kaida kayi wannan tunanin zaka fad’i haka, ka rabu da duniya idan akace akwai azzaluman shuwagabanni, talaka beda ikon aiwatar da komai matuk’ar ta had’oshi da mai kud’i, ko d’azu Yayan Farouk ya fad’a mani da zai samu sheda koya take saiya maido da shari’ar Farouk kotu, sai anyi bincike koda wanda ya kashe shi baya duniya. 

Jinjina kai Nabeel yayi yana fad’in amma Abbah bazai iya taimakawa ba? Adnan yace a wajen me kenan? Gyara zama Nabeel yayi yana fad’in dole yasan duk wasu masu gadi da sukayi aiki dashi a waccan shekarar, ina zargin kamar an had’a baki da masu gadi wajen fitar da gawar Farouk, kaga idan aka tabbatar da haka dole za’a gano wanda yasa suka aikata haka, daga nan kuma zai kai agano wanda yayi kisan, danni ina tunanin kamar a cikin yaran makarantar ne aka samu wani ya kashe shi, kaga makarantar yaran masu kud’i ce dole asan yanda za’a rufe maganar. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button