ALKALI NE Page 61 to 70

Adnan yace abu ne me wuya Abbanka ya saurari wannan maganar, domin shekarun da yawa, idan aka tado mashi da maganar zaiga kamar anaso asashi wani babban aiki ne, tunda ya jima da aje aiki kaga abu ne mai wuya ya koma binciken abinda ya faru abaya.
Nabeel yace wallahi duk naji jikina yayi sanyi, kasanni Adnan bana son zalunci, haka Allah yayi ni, matukar naga anyi zalunci bana kyalewa, shiyasa a secondary d’in mu nine Ameer dan gaskiya bana goyon bayan zalunci, shiyasa fa ban zab’i makarantar ku ba dan bana son irin makarantun yaran masu kud’i, dan haka ka barni da Abbah zanyi magana dashi cikin sanyi, kuma zamuyi nasara.
Adnan yace Nabeel sai kayi ahankali kaga Mahaifinka ne. Nabeel yace koda shine ya aikata laifin bazanji kunyar tonashi ba, domin Allah ya hana zalunci.
Ajiyar zuciya Adnan yayi cike da farin ciki, yana masa godiya. Shiru Nabeel yayi can ya kalli Adnan yana fad’in akwai abinda ka b’oye mani Adnan.
Saurin kallonshi Adnan yayi yana fad’in kamar mefa? Murmushi Nabeel yayi yana fad’in wasa nake, kome kenan zamuyi magana. Adnan yace nagode sosai abokina. Nabeel yace bakomai.
Sallama yayi mashi ya rakoshi. Sai da ya tafi kafin ya nufi d’akin Mahaifinshi cike da fatan dacewa dan yasan yanzu yana kallon news.
****
Sai da Adnan ya tsaya wata super market yayi siyayya kafin ya fito zai wuce gida. Adnan Abdurrazak Matawalle! Saurin juyowa yayi jin ankirashi da cikekken sunanshi.
Gabanshi ne ya faad’i ganin wanda yake gabanshi. Matsowa Fawwaz yayi yana ware hannu ya rungume Adnan yana dariya. Jiki a sanyaye Adnan ya rungumeshi zuciyarsa tana tsinkewa.
Kallonshi Fawwaz yayi yana dariya yace shegen kaya, kaganka kuwa? Lallai na yarda ka zama Baba. Murmushi Adnan yayi yana fad’in Fawwaz dama da gaske ka dawo, Yaya Sameer yake fad’a mani shine ko kaneme ni.
Fawwaz yace taya zanki nemanka kawai abubuwa ne sukayi mani yawa, yanzu haka sauri nake zamuje wani party na abokin mu.
Adnan yace lallai dole bazaka nemeni ba saboda kazama d’an gayu ga sababbin abokai kayi. Fawwaz yace No ba haka bane, kasan yanzu kai ka girma, kana da Iyali bekamata narik’a sako ka cikin mu ba, gashi gaba d’aya ma naga kacanza daga yanda nasanka, duk da tun kafin mu rabu naga sabon canji daga gare ka.
Murmushi Adnan yayi yana fad’in dole nake canzawa, domin mun aikata babban laifin da har mu mutu yana bin mu, naga kamar kai kamanta, duk da ba nine na aikata laifin ba kullum cikin nadama nake da istigfari, amma kai gashinan kana morewar ka yanzu ma party zakaje.
Canza fuska Fawwaz yayi yana fad’in bangane ka aikata laifi ba? Adnan yace ka aikata dai, mu kam ai taimaka maka kawai mukayi nida marigayi.
Ja da baya Fawwaz yayi yana k’ank’ance idanu yana kallon Adnan. Murmushi Adnan yayi yana fad’in kada ka damu kawai na tuna maka ne saboda inaso ka fara neman yafiyar Allah, amma tabbas har yanzu ina kallon lokacin da ka yanki Farouk da wuk’a.
Sosai Fawwaz ya canza fuska tamkar wanda be tab’a dariya ba, jijiyoyin kanshi suka tashi idanuwanshi sukayi ja, hannu yasa aljihu ya ciro kwalin sigari, abaki yasa kafin ya bata wuta, sai da yayi mata kyakkyawar zuk’a ya fesar kafin ya kalli Adnan yana fad’in ban d’auka zaka iya tuna wannan abun ba, kamar yanda kasa ma bakin ka kwad’o a wancan karon to inaso kacigaba da zama ahaka, bazan d’auki wannan maganar ba, idan kuma ka san zaka rik’a mani ita to ka d’auka bamu tab’a sanin juna ba.
Jinjina kai Adnan yayi yana murmushi yace haba abokina, kada ka manta da amintakar mu, ada ma banyi magana ba bare yanzu, kawai shawara na baka tunda baka so baza’a sake ba.
Murmushi Fawwaz yayi yana fad’in nasanka ai bazaka iya tona asiri na ba, nagode ka gaishe da Yaranka. Adnan yace zasuji tunda babu kara. Fawwaz yace zan wuce.
Mota Adnan ya shige ranshi fess, koba komai ya tado mashi da abinda yawuce, idan yana da hankali maganar bazata bar zuciyarshi ba.
Fawaaz har ya shiga mota ya d’auki hanyar wajen Partyn yayi saurin canza hanya, tsaki yayi yana zuk’ar sigari ranshi ab’ace, gaba d’aya Adnan ya b’ata masa shirinshi, ya tuno masa abinda ya dad’e da mantawa.
Wayarsa ce tayi k’ara, yana dubawa yaga abokinsa ne, d’auka yayi yana fad’in Guy bazan samu zuwa ba gida zanje kaina yana ciwo. Shiru yayi kafin ya kashe wayar, gudun motar ya k’ara zuwa gida.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣7️⃣
Fawwaz lafiyar ka kuwa? Kauda kai yayi yana fad’in Ammi normal. Zama tayi tana fad’in kace mun zakaje wajen Party amma kuma kadawo kana b’ata fuska ko partyn beyi maka ba? Ammi kawai b’ata mun rai akayi shiyasa.
Murmushi tayi tana fad’in Fawwaz nasha fad’a maka ka girma, yakamata karage wannan shirmen da kakeyi, zuwa yanzu yaci ace ka aje Iya…. Ammi dan Allah kada ki k’arasa, duka me nayi a duniyar da zan cutar da kaina ta hanyar aure har da tara wasu Iyali can, kina ganin Dady sai da ya more rayuwarsa kafin yayi aure, bayan aurensa ma sai da kuka dad’e kafin ya yarda kika haihu gashinan yanzu kowa yaganki bazaiyi tunanin kin haifeni ba, da ace kin haihu da yawa ko kinyi aure da wuri da yanzu kila hak’oranki sun fara fita.
Duka ta kaimashi yayi saurin kaucewa yana dariya. Dadynshi da yake jinsu ya shigo yana fad’in kada ki dokar mani yaro kinsan tunda ya taso besan me ake kira zafin duka ba.
Ammi tace ai duk kaine ka sangartashi, ba damar yaro yayi laifi a tab’ashi sai ka fara fad’a, idan bam manta ba har rabuwa mun tab’ayi akan zan dokeshi.
Dady yace sa’a kikaci baki kai ga dukansa ba shiyasa hukuncin ya tsaya a haka kikaje gida kikayo kwana biyu, da ace kin dokesa kila sai nayi babban hukunci.
Tab’e baki tayi tana fad’in dad’ina da gobe saurin zuwa, shima gashinan ya girma damma ka hanashi aure ai da yanzu shima ya fara jin yanda naji akan Yara.
Zama Dady yayi yana fad’in My Son wai kana son aure yanzu? Saurin girgiza kai yayi yana fad’in bana so Dady, gara abari na k’ara girma.
Ammi tace lallai kam zamu mutu bamuga auren ka ba. Dady yace aikuwa da ran mu zaiyi aure, kana ji na, kada ka damu da ita ka kwantar da hankalin ka babu me takura maka akan aure, duk lokacin daka shirya sai kayi abunka.
Gyara zama Fawwaz yayi yana fad’in Yawwa Dady d’azu daka aike ni gidan Abbah Barau na ga wata yarinya d’iyarsa ce? Dady yace Raheena kenan, itama waje tayi karatu lafiya? Ya mutsa fuska yayi yana fad’in ko gaishe ni batayi ba tana zaune a wajen lambu duk da taji shigowar mota kuma taji masu aiki suna gaishe ni.
Ammi tace dan me zata gaishe ka bayan ba kusa kuke ba, ina ma ruwanka da ita dan batayi maka magana ba? Kika sani ko Yaron nawa ya k’yasa. Dady ya fad’a.
Murmushi Ammi tayi tana fad’in to wannan dai anyi mata miji dan Hajiya Binta ta fad’a mani sunje Dubai siyo kayan aurenta kila ma bikin bazai wuce wata d’aya ba.
Kallonta Fawwaz yayi yana fad’in d’an bani lambarta mugaisa to. Harara Ammi ta banka masa tana fad’in bana son sakarci, meye zaka amshi wayarta bayan kaji aure zatayi.