ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 61 to 70

Dady yace bana son haka fa, da Raheena da Fawwaz duk d’aya ne a wajena, domin Alhaji Barau na hannun dama ta ne, kuma Fawwaz kamar Yaya yake agareta, ko kinji yace maki yana sonta? Girgiza kai Ammi tayi tana fad’in kasan halin zuciya. 

Dady yace to ki bashi suyi zumunci, yace maki ba aure zeyi yanzu ba damme zakisa zargi akanshi. Murmushi Ammi tayi tace ayi hak’uri baza’a sake ba. 

Kamo hannun Fawwaz Dady yayi yana fad’in akwai abinda yake damunka dan nasan baka saba dawowa kamar haka ba. Yamutsa fuska Fawwaz yayi yana fad’in Dad babu komai kawai gajiya nayi zan kwanta. 

Tashi Dadyn yayi yana fad’in shikenan ka kwanta, Ammi muje kada mu hanasa bacci. Tashi tayi tana fad’in Allah ya tashemu lafiya. Fawwaz yace amin. 

Kwanciya yayi sai dai daya juya maganganun Adnan ne suke dawo masa, tsaki yayi yana fad’in wallahi Adnan ka b’atamun rai, banda jahilci taya zaka tado abinda yawuce shekaru kusan sha biyu, gashi nan nima abun ya dawo mani. 

Tashi yayi ya d’auko wata kwalba a cikin durowarsa, bud’ewa yayi ya shanye abinda yake ciki duka, wurgar da ita yayi ya haye gado yana jin jikinsa yana saki, a hankali idanuwansa suka fara rufewa tamkar wanda ake yawo dashi asama, da haka bacci yayi gaba dashi. 

****

Washe gari har wajen k’arfe goma be fito ba, Dady ne ya kalli Ammi yana fad’in wai yau lafiyar Fawwaz kuwa, nasan baya tashi da wuri amma kuma yana fita motsa jiki idan ya gama ya sake kwanciya yau banji motsinshi ba? Ammi tace nima abinda nake tunani kenan. Dady yace muje mu dubashi. 

Da mamaki Dady yake kallon kwalbar da take hannunshi, kallon Ammi yayi yana fad’in dama Fawwaz yana shan syrup ne? Ammi tace wallahi nima sai yau na gani. 

Girgiza kai Dady yayi yana fad’in wannan syrup d’in mai k’arfin ne, shiyasa be tashi ba har yanzu, da alama kuma be had’ashi da komai ba haka kawai ya sha dan banga robar lemu ba. 

Hannu Ammi tasa ta fara tadashi, girgizashi tayi kafin ya farka a firgice yana kiran sunan Farouk. Da mamaki suka bishi da kallo. Zama Dady yayi yana fad’in Fawwaz waye kuma Farouk? Hannu yasa ya dafe kanshi yana goge zufar datake goshinsa. 

Sake tambayarsa yayi kafin ya kallesu yana fad’in bakowa. Ammi tace banyarda ba, taya zaka farka da sunan mutum abakin ka da alamu mafarkinsa kayi, kuma da tunaninshi ka kwanta. 

‘Bata fuska yayi yana kokarin sauka yace Ammi nace bakowa wani abokina ne. Dady yace shikenan tashi kaje kayi wanka kayi sallah kazo ina da magana da kai. 

**** ****

Wai Nabeel lafiya kake kuwa? Jiya da dare ina kallo kazo ka zauna kayi shiru kamar da magana abakin ka, na tambayeka kace bakomai ka tafi, yauma gashi kazo mun gaisa kuma kazauna kamar zaka fad’i wata magana amma kayi shiru. 

Gyara zama Nabeel yayi yana fad’in Abbah dama wata tambaya zanyi maka to jiya naga hankalin ka yana wajen kallon news shiyasa na tafi. 

Kofin shayin Abbah ya aje yana fad’in ina jinka. Duk’ar da kai Nabeel yayi yana fad’in d’azu ne da ana gyara wancan tsohon d’akin na kaya shine naga wata tsohuwar jarida, har na barta sai kuma naga sunan makarantar da kayi aiki a jiki ga hoton wani yaro a kwance da kayan makarantar jikinsa duk jini, hakan ne yaja hankalina na karanta shafin, kuma hada hotonka na gani a kasan shafin a matsayin ka na shugaban makarantar, to shine labarin yaja hankalina nakeso naji yanda abun ya faru. 

Saurin zare glass d’in idonshi yayi yana kallon Nabeel, ido Nabeel ya d’ago yana karantar mahaifinsa. Kayi hak’uri Abbah idan maganar ta b’ata maka rai. 

Ajiyar zuciya Abbah yayi yana fad’in waye ya baka wannan labarin? Nabeel yace a jarida na gani. Jinjina kai Abbah yayi yana fad’in dama ba’a kone duk wasu jaridun d’akin ba? To yaushe ma aka fiddo da kayan d’akin tunda nasan babu abinda za’ayi a d’akin, ko dai kaine kaje kayi mani bincike? Saurin girgiza kai Nabeel yayi yana fad’in da gaske gyaran d’akin nasa ayi, gashi can ma suna k’arasawa. 

Ina jaridar take? Abbah ya fad’a jiki a sanyaye. Hannu Nabeel yasa a aljihu ya cirota ya mik’a masa. Shiru Abbah yayi yana kallon hoton Farouk da yake kwance cikin jini ga wuyansa da shatin wuka. 

Wasu hawaye ne suka taho masa, da sauri ya maida glass d’inshi ya aje jaridar. Kallon Nabeel yayi cikin dakiya yana fad’in wannan ai tsohon abu ne, kanaga tun 2008 fa, ni harna manta da abun ma, muma haka muka samu labari dan abun ya faru ne bayan an tashi daga makaranta. 

Nabeel yace to Abbah bakuyi bincike ba? Girgiza kai yayi yana fad’in duk abinda ya faru bayan makaranta to bamu da hakki akansa, sannan kuma abun ba’a makaranta ya faru ba, kaga bamu da ikon yin wani abu, kayan makarantar da suke jikinsa ne yasa kaga ansa hotona saboda ‘Dalibina ne, da ace Iyayenshi sun nuna zasu shigar da k’ara da amatsayin mu na shuwagabannin makarantar Yaron mun taimaka wajen ganin a kwato masa hakkinsa, amma koda mukaje gaisuwa Mahaifin Yaron yace abar maganar. 

Amma Abbah…. Kaga Nabeel bana son yawan tambaya, kana son jin abinda ya faru kuma na fad’a maka, bansan ta yanda aka kashe shi ba tunda ba’a makaranta ya mutu ba, dan haka bana so ka tado mani da abinda yawuce shekaru da yawa, ka maida hankali wajen aikin ka zaifi maka. Tashi kaje, kuma bana so naji ka sake tada maganar dan nasanka da son kwato ma mutane hakkinsu, shiyasa ma ka zab’i kayi aiki a hukumar kwato ma d’an Adam hakkinsa. 

Jiki a sanyaye Nabeel ya fice, kai tsaye wajen masu gyaran d’akin ya nufa, yana zuwa ya iske har sun gama sun rufe d’akin an kwashe dattin. Zama yayi yana murmushi, dama yasan za’a iya samun tsohuwar jarida a wannan d’akin, shiyasa tunda Adnan ya fad’a masa an buga labarin ajarida a daren jiya yayi tunanin yazo ya bincika dan yasan Abbanshi akwai aje tsofaffin kaya, hakan yasa yau tunda safe yashiga d’akin, cikin ikon Allah yaga jaridar, shiyasa yasa masu aiki su gyara d’akin gudun kada ya kaima Abbah jaridar yace da niya ya bincikota. 

Ajiyar zuciya yayi yana tuna yanayin da yaga Abbansa aciki, tabbas akwai wani b’oyayyan lamari, akwai abinda Abbansa ya sani yake b’oyewa, haka ma Adnan ba gaskiyar labarin ya bashi ba. Dole yasan gaskiyar labarin kodan ya taimaki Abbansa kada mutuwa ta riskeshi da hakkin wasu.

 Waya ya ciro ya kira Adnan, bayan sun gaisa yace mashi yana so su had’u anjima. Adnan yace shikenan. Kashe wayar yayi ya koma cikin gida. 

**** ***

Hello Alhaji Marusa lafiya kuwa naji kamar kana cikin damuwa? Alhaji Barau ya fad’a cikin tashin hankali. Alhaji Marusa yace nima tambayar da zan maka kenan najika cikin tashin hankali, yanzu nake shirin kiranka sai gashi ka kirani. 

Narke murya Alhaji Barau yayi yana fad’in store d’in kayana akazo cikin dare aka yashe ni, komai basu bar mani ba, da asuba Mr. Kallah yamun waya babban shagonshi na garinsu cikin dare ya kama da wuta ko tsinke ba’a fitar ba, shine nace bara na kiraka na fad’a maka halin da muke ciki. 

Hawaye ne suka zubo ma Alhaji Marusa yana fad’in naku me sauki ne, tun jiya na kira ku amma wayar ku bata shiga, wallahi jiya banyi bacci ba, gaba d’aya tashin hankali yamun yawa ko abinci na kasaci, shikenan talauci ya fara mani sallama Alhaji Barau. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button