ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 61 to 70

Mekake fad’a ne haka Alhaji Marusa? Sun takaita ni Alhaji Barau, kayan da nayi oda jiya an d’auko mani su cikin dare aka tare masu motar aka kwace sannan aka kashe su, kaya ne masu tsadar gaske, na saka dukiyata mai yawa wajen d’aukosu, sannan babbar ma’ajiyata itama yau da asuba akamun waya ta kone kurmus, shikenan nashiga ukku. 

Murmushin gefen baki Alhaji Barau yayi kafin ya canza fuska yana fad’in yaushe ka bada odar kaya Alhaji Marusa? Ai na d’auka mun yanke shawarar had’a guiwa mu d’auko wasu kaya gaba d’aya, tun daga lokacin kuma babu wanda ya sake shigo da kaya amma gashi kace an kawo maka kaya jiya? Daburcewa Alhaji Marusa yayi yana fad’in ba su bane, wad’annan wasu ne daban abokin harkallarmu yamun tayinsu shine na tura masa kud’i, dan Allah kazo inaji dole muje asibiti dan numfashina baya tafiya dai-dai. 

Alhaji Barau yace shikenan kazauna kada ka tashi gani nan. Godiya yayi masa ya kashe wayar. Wata irin dariya Alhaji Barau yasa yana fad’in damu kake magana, Allah yasa ma kasheka mu huta. Jakarsa ya d’auka ya saukko. 

A falo ya iske su Momy, kallonta yayi yana fad’in direba zaizo ya amsar mani kayan kari sauri nake Alhaji Marusa beda lafiya. Momy tace ikon Allah, meya sameshi kuma? Alhaji Barau yace idan na dawo zakiji amma dai bala’i ne ya afka masa. 

Momy tace to Allah ya kyauta, ince dai babu komai naka a cikin bala’in? Murmushi yayi yana fad’in babu. Kai ta jinjina tana fad’in to mun gode Allah, sai ka dawo. 

Yana fita direbanshi yazo ya amshi jakar hannunsa ya bud’e masa mota yashiga suka bar gidan. A hanya aka kirashi da wata lamba, yana d’auka aka fad’a masa babban ‘Dan Alhaji Marusa ne. Alhaji Barau yace naji dai, lafiya ko? Daga can aka fad’a masa Alhaji Marusa ne ya fad’i an wuce dashi asibiti. Cike da jimami yace gashinan zuwa.Murmushi yayi ya kalli direba yana fad’a masa su wuce asibitin su. Mr. Kallah ya kira ya fad’a masa yace gashinan zuwa. 

**** ***

Fawwaz meya had’a ka da wannan maganin mai k’arfi haka? Kauda kai yayi yana fad’in Dady mura nakeyi shine nasha. Ammi tace murar ce tasa ka shanye kwalba d’aya? Saurin kallonta yayi yana fad’in Ammi wace irin kwalba d’aya kuma, ya dad’e fa iya yanda akace asha nake sha kawai jiya ne ya k’are. 

To meya saka dogon bacci haka? Dady yace isa haka Ammi tunda yace ba duka yasha ba abar maganar. Tab’e baki tayi tana fad’in kaje kaci abincin ka. Dady yace sa akawo masa nan. 

Tashi tayi tana fad’in wallahi Alhaji kana shagwab’ar da yaron nan, ya girma amma ka hanashi ya fahimci haka. Dady yace e naji bakomai. Murmushi Fawwaz yayi yana fad’in Dady da Ammi nah. 

**** ****

Abbah ina kwana ya gidan? Lafiya lau jiki yayi sauki ai. Alhaji Mansur yace to madalla, sai ka k’ara kula, bana so kana saka damuwa aranka, sai jiya Maman ku take fad’a mani baka da lafiya. 

Ra’eez yace ai na warke Abbah. Alhaji Mansur yace ta fad’a mani kokarin da kukeyi kai da abokan ka, kayi masu godiya, insha Allahu komai ya kusa zuwa k’arshe. 

Ra’eez ya fad’a masa yanda sukayi da Kawun Jabeer. Alhaji Mansur yace Allah sarki Brr. Kamal, kaga kuwa na rasa lambarshi ka turo mani sai muyi magana dashi, Abubakar ma zan kirashi na fad’a masa shari’ar ta kusa zuwa dan ya shirya. 

Ra’eez yace yanzu zan turo maka. Alhaji Mansur yace maganar motarka ban manta ba, wannan satin zai dawo zai zo ya dubata. Ra’eez yace to Abbah nagode, agaishe dasu Umma. 

**** ***

Yes, shigo. *Malan Dauda* lafiya dai,,? Risnawa yayi yana fad’in ‘Yallab’ai kana da bako. Bako kuma, waye ne? E to ya nuna mani katinshi ma’aikacin gidan babban redion ne. 

Shikenan kace yashigo. Da sallama Rafeek yashigo ofis d’in Kwamishna, amsawa yayi yana nuna mashi wajen zama. Hannu Kwamishna ya mik’a masa suka gaisa. Murmushi yayi yana fad’in lallai yau muna da manyan baki. 

Murmushi Rafeek yayi yana fad’in ‘Yallab’ai barka da aiki. Kwamishna yace yauwa kaima sannun ka da aiki, ai kune masu aiki domin kuna nishad’antar damu da labaruka masu gamsarwa, musamman kai, dan ina kallon labaranka. 

Ruwan da masinjan ya aje ya d’auka yasha yana fad’in ai abun ba sauki ‘Yallab’ai. Kwamishna yace to Allah yasa mudace. Rafeek yace amin. 

Wato dama nazo ne ina so naroki alfarmar fira da kai agidan redion mu idan babu damuwa. Murmushi Kwamishna yayi yana fad’in haba babu damuwar komai, ai gidan redion ku babba ne, kunsan abinda kukeyi shiyasa nake matuk’ar son sauraren abinda ya fito daga can, babu komai yaushe ne lokacin firar? Rafeek yace ‘Yallab’ai kaine zaka sa mana lokaci ai. 

Murmushi Kwamishna yayi yana fad’in ko gobe ma yayi. Rafeek yace to mungode Allah ya k’ara girma. Kwamishna yace amin. Kati Rafeek ya mik’a masa shima ya bashi nashi. Godiya yayi masa ya baro ofis d’in cike da farin ciki, kai tsaye asibitin da akayi masa kwatance mallakin Dr. Aliyu Sani ya nufa. 

Kwamishna kuwa farin ciki ne ya rufeshi jin za’ayi fira dashi a babban gidan redio, yasan tunda suka gayyaceshi sun yaba da aikinsa shiyasa suke son fira dashi, yasan kilama ya samu lambar yabo idan aka ga karramawar da ‘yan gidan redion zasuyi mashi. 

**** ****

Adnan maganar daka fad’a mani gaskiya ce kuwa? Kallon Nabeel Adnan yayi yana fad’in baka yarda dani bane? Girgiza kai yayi yana fad’in na yarda da kai, sai dai acikin labarin daka bani baka fad’a mani gaskiyar yanda abun ya faru ba, da alama kasan komai tunda makarantar kuce, kuma Yaron ajinku d’aya, kawai dai kana b’oye mani ne saboda kana jin kunyar ka tona asirin mahaifina. 

Adnan yace ya kake fad’in haka, waye ya fad’a maka Abbanka yana da hannu acikin abinda ya faru? Idan beda hannu ka fad’a mani waye yake bayanshi to? Ajiyar zuciya Adnan ya saki yana fad’in wai Nabeel lafiya kake kuwa, yanda ka d’auki wannan abun kamar wani naka ne haka ta faru dashi. 

Murmushi Nabeel yayi yana fad’in kada kamanta aikina ne, Allah ya bani ilimin sanin yanayin da mutum yake ciki, gashi kuma ina aiki a k’arkashin masu kare hakkin d’an Adam (Human right), tun daka fad’a mani wannan labarin nasan dole Abbah yana da alak’a dashi, kaima kana neman wani abu ne shiyasa kazo mani da maganar, domin bani da had’i da labarinka amma gashi kazo mani dashi, shekarar mu nawa tare baka tab’a bani wannan labarin ba sai jiya. Uhmm Adnan ko baka fad’a mani ba dole Abbah yana da masaniya akan wannan abun, kuma ka sani idan baka fad’a mani ba zanje nayi bincike da kaina, domin tunda ka bani labarin nan ya tab’a zuciyata, kuma naji ina da sha’awar taimakawa. 

Jinjina kai Adnan yayi yana fad’in kayi hak’uri zan baka labari, abun ne babu dad’in ji dan bansan yanda zaka kalleshi ba tunda ya shafi ahalin ka, amma tunda kace na fad’a maka zan fad’a maka, sai dai ina rokon ka koda kaji labarin idan har bazaka taimaka ba saboda Mahaifinka dan Allah kada ka fad’ama kowa. 

Nabeel yace wallahi koda Abbah ne ya kashe Farouk sai na tabbatar da gaskiya, dan haka ina jinka…. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button