ALKALI NE Page 61 to 70

3⃣8️⃣
Hannu Nabeel yasa yana share hawayen da suka jik’a masa fuska na tausayin labarin da Adnan ya gama bashi, Adnan ma kukan yakeyi, jiyake kamar ayanzu abun ya faru.
Girgiza kai Nabeel yayi yana fad’in na sani dama Abbana yana da masaniya akan wannan abun, tun d’azu da mukayi magana naga halin da yashiga hankalina bai kwanta ba, hakan yasa nace ka fad’a mani gaskiya.
Adnan yace wallahi Nabeel tunda Yaya Sameer yazo mani da maganar hankali na yake tashe, duk da abaya ina d’an tuna abun amma ba kamar da Yaya yazo mani da maganar ba, tun daga ranar komai ya canza mani, wallahi jiya har mafarkin Naseer da Farouk nayi, shiyasa na kudirta araina ko zan rasa raina sai na bayar da sheda akan shari’ar da za’a gabatar, gaba d’aya laifin mu ne, da ace mun fad’i gaskiya duk haka bazata faru ba.
Nabeel yace dole a tabbatar da wannan gaskiyar, koda ace dasa hannun Abbah akayi kisan wallahi sai an tona komai, sai kuma Allah yasa babushi aciki, laifinsa d’aya daya taimaka ma masu laifi wajen b’oye gaskiya, nasan shima dole ayi masa hukunci.
Jinjina kai Adnan yayi yana fad’in nagode Nabeel, hakika kai d’in abokine nagari, na d’auka zansha wahala kafin ka bani had’in kai sai gashi kaima zaka bada taka gudummuwar, tabbas ka dace da yanayin aikin ka, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi.
Nabeel yace amin, sai dai kuma banso kayima Fawwaz wannan maganar ba, domin nasan duk inda yake maganar tana masa yawo akai, duk lokacin da yaji an shigar da k’ara kaine zaka fad’o masa arai, zai iya yin duk abinda zeyi wajen ganin bakaje kotu ba.
Adnan yace ka barshi Allah ya fishi, gara da nayi masa maganar na tabbata bazai sake kwanciyar hankali ba. Nabeel yace haka ne, Allah ya bamu ikon tabbatar da gaskiya. Adnan yace amin. Sallama yayi mashi yawuce cike da farin ciki.
**** ****
Tsaye Rafeek yake a bakin k’ofar asibitin Dr. Aliyu Sani sai kallon agogo yakeyi, wani ma’aikacin wajen ne yazo wucewa, da sauri Rafeek ya k’arasa yayi masa sallama.
Murmushi mutumin yayi yana amsawa dan ya gane Rafeek saboda ba b’oyayye bane kasancewarsa ma’aikacin gidan babbar redio.
Hannu Rafeek ya bashi suka gaisa. Mutumin yace yau muna da babban bako, shine kuma kake tsaye a waje Malan Rafeek. Murmushi Rafeek yayi yana fad’in ai ban dad’e da zuwa ba dama ina jiran naga wani ne.
Mutumin yace barka da zuwa ni sunana *Dr. Sageer Isah*, kai kam nasan naka domin sananne ne a wajen kowa. Murmushi Rafeek yayi yana fad’in nagode sosai Dr. Sageer.
Shiru yayi kafin yace dan Allah Dr. Aliyu fa? Dr. Sageer yace aikuwa yau zaishigo dan yau ranar zuwansa ne, kasan Dr. Ba kasafai yake shigowa ba akwai wasu aiyukan da suke gabansa, amma yau munyi waya yace zaishigo, sai dai ban sani ba ko da wuri zai shigo.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad’in ina jin labarinsa gaskiya babban likita ne, gashi har ya bud’e asibitinshi, ga na gwamnati da yake aiki, ga sauran wajaje da yaje gudanar da aiyukansa, hakan yasa nakeso mu d’an gana dashi.
Murmushi Dr. Sageer yayi yana fad’in ai Dr. Ba sauki, mutum ne mai matuk’ar son kud’i, shiyasa gaba d’aya rayuwarsa beda lokacin kanshi, duk wani abu indai zai kawo kud’i to Dr. yana gaba wajen nemoshi, shiyasa asibitin nan muke da abubuwa da yawa, ba dai muje waje muyi wani abu ba sai dai ma azo wajen mu ayi.
Rafeek yace Allah sarki, gaskiya yasan kanshi, ai duniyar sai da neman kud’i. Dr. Sageer yace muje daga ciki ka jirashi ai bazamu bar babban bako a waje ba. Rafeek yace shikenan muje, amma idan naga bezo ba zan tafi saboda na baro aiki.
****
Ra’eez Yaya fa yace mu fara shirya yanda za’a shigar da k’arar su Naseer, dan sunyi waya da Adnan ya fad’a masa an samu Nabeel zai taimaka, tunda ba’a gano Iyayen Farouk ba gara ashigar da shari’ar Naseer hakan ne zai tono ta Farouk.
Ajiyar zuciya Ra’eez yayi yana fad’in nima so nake zuwa litinin afara shari’ar dan bana so murasa damar da muke da ita. Jabeer yace sai dai Yaya yace beyi magana da Baffansa ba, yafiso sai anshigar da k’arar kafin yayi masu magana.
Ra’eez yace ina tsoron kada suce basu amince ba. Jabeer yace zasu amince, domin babu wanda zaiji labarinka be tausaya maka ba, kuma ta shari’ar su ce za’a tado taka.
Ra’eez yace Allah yasa. Jabeer yace amin, wai ina mutuniyar? Tsaki Ra’eez yayi yana fad’in ko jiya tamun waya muka gaisa. Jabeer yace baiwar Allah. Tashi Ra’eez yayi yana fad’in muje ni kada ka fara kawo mani maganar wata Raheena. Dariya Jabeer yayi yana fad’in daga fad’in gaskiya.
**** ***
Dr. Sageer ya aiki ina fatan komai yana tafiya dai-dai? Jinjina kai Dr. Sageer yayi yana fad’in aiki lafiya lau babu matsalar komai, sai dai kana da babban bako.
Glass ya cire yana fad’in bako kuma? Ai babu wada yace mun zai zo. Dr. Sageer yace wannan ma’aikacin babban gidan redion ne *Rafeek Sambo Jarmai*.
Jinjina kai yayi yana fad’in meya kawo d’an jarida waje na kuma? Dr. Sageer yace yanda kake cigaba ‘Yallab’ai ai dole ‘yan jarida surika son ganinka, shima d’azu ya gama yabonka.
Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad’in ka shigo dashi to. Dr. Sageer yace yanzu kuwa.
Bayan Rafeek yashigo suka gaisa sai Dr. Sageer ya basu waje. Dr. Aliyu yace yau kaine da kan ka? Rafeek yace wallahi kuwa, jiya nashiga babban asibiti wajen wani abokina shine ake maganar irin kwazonka shine nace ni kuma zanzo naga asibitinka kuma mugaisa.
Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad’in amma nagode, ai mutum baya zama gwarzo dole saiya jajirce, kafin na kawo wannan matsayin nasha gwagwarmaya sosai, da haka dai ina hak’uri har Allah ya d’aga ni.
Rafeek yace wannan haka yake, ai kamar babban Alkali ne Alhaji Barau, duk wanda yasanshi yasan yanda yake da jajircewa awajen aiki, saboda kok’arinsa sai da sunanshi yayi fice a gidan redion mu, sannan ga tsohon Alkali, su duka biyun mutane suna alfahari dasu.
Gyara zama Dr. Aliyu yayi yana fad’in Allah sarki Brr. Barau, ai mutumina ne sosai, yanzu ma aiki ne yamun yawa shiyasa muka rage gaisawa, ai ta silarsu na samu alkhairi sosai, zan iya cewa ta silarsu na kai wannan matsayin da nake ayanzu, domin sun taka rawar gani arayuwata.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad’in da alama kayi masu abinda sukaji dad’i hakan yasa suka tsaya maka. Dr. Aliyu yace sosai kuwa, domin nine na fara taimaka mashi ya kai wannan matsayin da yake kai kafin shima yasa tsohon Alkali da wasu manya suka dafa mani, tabbas nine na fara taimaka masu.
Rafeek yace idan haka ne kaine ka tsaya masu ba sune suka tsaya maka ba, domin duk wanda zai maka wani taimako har kaci nasara arayuwa to baka da kamarsa, duk da bansan abinda kayi masu ba amma nasan amatsayinka na babban likita nasan ka cece rayuwar wani daga cikinsu.
Girgiza kai Dr. Aliyu yayi yana fad’in ko d’aya, kawai nayi masu…. Gyaran murya yayi yana fad’in haka ne, kasan mu likitoci akwai mu da taimako, idan kuma mutum yasan alkhairi to baya mantawa damu, wannan shine abinda ya had’ani dasu har muke abota.
Rafeek yace gaskiya kai d’in na daban ne, gashi dai kaine mai taimakon amma duk da haka kana ganin sune suka taimaka maka, Allah ne zai iya biyanka.