ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 61 to 70

Murmushi Dr. Aliyu ya saki yana fad’in maganar ka gaskiya ce Rafeek, ya kamata ace har yanzu suna bani girma, sai dai kuma nine nake nemansu ba sune suke nemana ba, akwai Alhaji Marusa da Mr. Kallah duk mutane na ne. 

Rafeek yace saboda ka gama masu amfani shiyasa suka kyale ka, kasan suna hud’d’a da mutane da yawa dole surik’a samun masu yi masu alfarma da yawa shiyasa bazasu rik’a neman wad’an da suka taimakesu ba. 

Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad’in aiko be kamata ace sun manta dani ba musamman shi Brr. Barau, domin na bada gudummuwa wajen hayewarsa wannan kujera, gaskiya ka sosa mani inda yake mani kaikayi ma, maganar ka gaskiya ce, bekamata ace nine nake binsu ba domin nine nayi masu rana. 

Murmushi Rafeek yayi ya mik’e yana fad’in ‘Yallab’ai zan koma, dama nace zanzo mugaisa ne. Hannu Dr. Aliyu ya bashi yana fad’in nagode Rafeek, ga katina sai murik’a gaisawa ko. 

Rafeek yace nike da godiya. Sallama yayi mashi ya fice ya barshi yana juyi a kujera cike da tunani. Murmushi ya saki yana fad’in Allah yayi maka albarka Rafeek, ka sosa mani inda yake mani kaikayi, ga babban Lab can zan fara ginawa dama ina tunanin gininshi bara nayi amfani da wannan damar, Allah ma yaso banyi sub’utar baki ba dana fad’a masa tsohon sirrin mu. 

Waya ya ciro ya fara neman Alhaji Barau. Bugu biyu ya d’auka, bayan sun gaisa Alhaji Barau yace babban likita kwana da yawa, ka ganni nan nazo asibiti an kawo Alhaji Marusa. 

Dr. Aliyu yace kunki dai dawowa asibitina duk da kunsan nima ina da kayan aiki. Alhaji Barau yace ba haka bane, kasan asibitin mu hada turawa kai kuma naka babu wasu kwararrun likitoci, kasan ni kuma bana son wasa da rayuwa shiyasa na rik’e asibitin Dr. James. 

Jinjina kai Dr. yayi yana fad’in idan da amana ai ruwa bazaici gwani ba. Alhaji Barau yace me kake nufi? Gyara zama Dr. yayi yana fad’in manta kawai, dama wasu ‘yan kud’i nake so zan fara gina parmanent side na Lab d’ina kuma babu kud’i masu yawa a hannuna shine nace bara na maka magana. 

Shiru Alhaji Barau yayi kafin yace haba likita, taya zaka zo mani da maganar kud’i da rana tsaka haka. Murmushi Dr yayi yana fad’in ko bashi ne ai zan samu ko? Alhaji Barau yace amma kaji nace ankawo Alhaji Marusa asibiti ko? Kuma ni yanzu banida kud’in da zan iya baka aro dan bikin d’iyata za’ayi, wai Likita meyasa kake son tambayata kud’i ne. 

Dr yace yanzu dan nace ka bani bashi shikenan ya zama laifi, haba Alhaji kada ka mance da alkhairin da nayi maka fa, ko shekaru dubu za’ayi bekamata kamance da abinda nayi maku ba, domin nayi maku babbar rana kaima kasani, kuma har yanzu da bazata kake rawa. 

Tsaki Alhaji Barau yayi yana fad’in ni bangane abinda kake magana akai ba danni bani da lokacin tunawa da rayuwar baya, koma menene bani da kud’i sai dai kajira Alhaji Marusa ya warke, ka gaishe da iyalin ka sai anjima. 

Kallon wayar yayi jin an katse. Murmushi yayi yana fad’in maganar ka gaskiya ce Rafeek, dama nayi haka ne dan na gwadasu, lallai Brr. Barau ya cika butulu, amma bakomai indai nine bazan sake nemanshi ba, nagode Allah nima ina da kud’i, ko ba komai naci daga jikinsu da kud’in su ma nayi wannan ginin. 

*** ***

Wai *Marwan* meya faru ne? Wanda aka kira da Marwan ya yamutsa fuska yana fad’in nima bansani ba, nazo zan amshi wasu kud’i ina shiga falon kawai na ganshi ya mik’e daga zaunan da yake, kafin na shiga kawai naga ya zube k’asa, gashi can dai ana dubashi. 

Alhaji Barau yace shima Alhaji Marusa sai da nace mashi ya zauna nazo amma ya tashi, ba’a son idan tashin hankali ya same ka ka tashi. Marwan yace kamar ya ban gane ba? Labarin abinda ya faru ya fad’a masa. 

Yamutse fuska yayi yana fad’in amma ai babu abinda zai tab’a dukiyarshi dan ya rasa d’an wannan abun dan nasan Dad yana da mak’udan kud’i, meye nashi nashiga damuwa gashinan zai jama kanshi, da kyar idan bai samu mutuwar b’arin jiki ba, yanzu ko kula dashi ai aiki ne, sai dai ya biya kud’i a fiddashi waje yayi jinyarsa acan danni cikin satin nan zan koma India. 

Ido Alhaji Barau ya tsura ma Marwan har ya gama maganarshi. Ajiyar zuciya ya saki yana fad’in yanzu ina K’anin naka? Marwan yace kasan baya son zaman k’asar nan, dama kuma Dad baya son muna zuwa gida, Mom kuma taje Dubai sai jibi zata dawo. 

Alhaji Barau yace to Allah ya kyauta, sai ka tsaida tafiyarka ka kula dashi kafin asan abunyi. Waro ido yayi yana mik’ewa, kallon agogo yayi yana fad’in yanzu ni ina da wajen zuwa, dama kai na tsaya jira da naji kace kana hanya, zanje kafin anjima na dawo. 

Bai jira amsar Alhaji Barau ba yayi gaba. Baki Alhaji Barau ya saki yana kallon Marwan, a hankali yake fad’in Allah nagode maka da baka bani namiji ba, tabbas yanzu Alhaji Marusa zaiyi nadamar rashin kula da yaranshi da yayi, koba komai ita tarbiya wani abu ce, saboda baka son takura ka tura yara waje sai dai ka aika masu kud’i, lallai Alhaji Marusa taka tazo k’arshe, nima ba zama zanyi ba ina da aikinyi. 

Fitowar likita yasa yayi saurin binshi zuwa ofis. Bayan sun gaisa yake fad’a masa sanadiyar fad’uwar da yayi ya samu mutuwar b’arin jiki, dole abashi gado saboda za’a fara masa gashi, anci sa’a ma akwai sauran kud’inshi da yawa a asusun asibitin da ya zuba ana juyawa saboda rashin lafiyarshi data iyalinshi, dan haka yanzu kulawa kawai zasu bashi, sannan jininsa ya hau dole ya samu hutu. 

Alhaji Barau yace lallai tashi ta sameshi, tunda akwai kud’i ai damuwar da sauki, yanzu acigaba da bashi kulawa zamu rik’a waya. Likita yace ba komai zamu kula dashi. Sallama yayi mashi ya fita. 

**** ***

Wai Rafeek lafiya kwana biyu ka canza ba kamar yanda kake ba? Murmushi yayi yana fad’in lafiya lau Baffa kawai wani aiki ne ya tasoni gaba shine yasa bana zama. 

Gyara zama Baffa yayi yana fad’in bana so kana matsama kanka, nasha fad’a maka aikin ku yana da had’ari, shiyasa kaji ina yawan tambayarka dan bana so kajefa kanka cikin damuwa kazo kaja mana, dan Allah Rafeek kada kajawo mana abinda zamu rasaka kamar yanda muka rasa d’an uwanka, kome zakayi arayuwa yana da kyau karika sanar mana domin addu’ar mu agareka kariya ce. 

Jinjina kai Rafeek yayi yana fad’in Baffa banyi niyar sanar da ku komai ba har sai na kammala abinda nakeyi, amma wannan maganar da kayi tasa jikina yayi sanyi, tabbas akwai abinda nake shirinyi, kuma ina da niyar sanar daku nan gaba kad’an, amma dole yanzu na fad’a maku. 

Dama shari’ar marigayi Naseer ce nakeso zan dawo da ita domin abi masa hakkin sa sabo…. Dakata Rafeek! Ummansu ta fad’a cikin karaji, da sauri ya d’ago kai yana kallonta. 

Hawaye ne suka gangaro a fuskarta tacigaba da fad’in ban amince maka ka tado wannan maganar ba, abinda yawuce shekara da shekaru meye amfanin tadoshi, wato acan baya k’arfin ka be kawo ba shiyasa da mukace abarshi ka hak’ura, yanzu kuma kana ganin kayi kwari ka isa tsayawa da k’afafuwanka shine zaka tado mana da tashin hankalin da muka manta dashi, wallahi Rafeek ka fita a idona, zan sab’a maka akan wannan maganar, babu wanda ya isa ya maido da wannan maganar baya, domin nasan ruhin Naseer yana can cikin salama. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button