ALKALI NE Page 71 to 80

Brr. Ra’eez ya kake gani akan shari’ar da za’ayi ranar litinin? Insha Allahu itama muna saran nasara. Nagode. Saurin wucewa yayi dan a matuk’ar gajiye yake.
****
Wai Alhaji wane hali ake ciki naga tunda ka dawo kotu wajen Alhaji Barau kake kwance anan baka sake cewa komai ba. Ajiyar zuciya Alhaji M. Sanda ya sauke yana fad’in ko dai muyi nasara ko kuma suyi nasara, yanzu haka an tabbatar cewa Fawwaz shine ya kashe Farouk.
A zabure Ammi ta mik’e tana dafe kirji idanuwanta awaje, kallon Alhaji tayi tana fad’in amma ba haka kuka fad’a mani ba. Runtse idanuwanshi yayi ya bud’e, sosai sukayi ja. Kallonta yayi yana fad’in ban d’auka abun zai kai haka ba shiyasa na b’oye maki, amma yanzu dole kiji komai…..
Kuka kawai Ammi takeyi da tagama jin abinda ya faru, kallon Alhaji tayi tana fad’in yanzu shima kashe shi zasuyi? Garinya saboda b’oye laifin Fawwaz zaku kashe wani, haba Alhaji.
Saurin tashi zaune yayi yana fad’in saboda irin haka yasa na b’oye maki, ki sani zan iya yin komai domin farin cikin Fawwaz, dan haka ban fad’a maki dan kiyi mani wa’azi ba, na fad’a maki ne dan naga babu amfanin b’oyewar. Tashi yayi ya shige d’aki.
Zubewa Ammi tayi hawayen bakin ciki yana zubo mata, ashe dama Alhaji zai iya kisan kai akan son da yake ma Fawwaz? Lallai biri yayi kama da mutum, gashinan Fawwaz yayi kisa an kamashi, idan bincike ya tsananta shima dole akamashi, lallai wannan shine abun kunya Uba da ‘Dah sunyi kisan kai.
Yana shiga d’aki wayarsa tayi k’ara, saurin d’auka yayi ganin Brr. Bajinta……..
Salati kawai Alhaji M. Sanda yake bayan da ya gama jin yanda shari’ar ta kasance, zubewa yayi saman gado jikinsa yana rawa, a sanyaye yace yanzu shikenan an tafi dashi? Brr. Bajinta yace wallahi dole ne tasa Alkali ya yanke wannan hukuncin, domin idon mutane suna kanshi, ga bak’i da nagani a kotun, Alhaji sai dai hakuri kawai, idan kuma zaka d’aukaka k’ara shikenan.
Jinjina kai yayi yana fad’in shikenan, amma bazan iya zaman gidan yari kona wuni d’aya bane bare har wata ukku, kawai zan biya tara nagode. Kashe wayar yayi ya fara neman Alhaji Barau, tsaki yayi jin wayar a kashe. Hannu yasa ya dafe kanshi yana jin d’akin yana juya masa, tabbas idan har suka bari aka gabatar da shari’ar Naseer asirin su zai tonu, tunda har suka iya gabatar da wannan vedion dole suna tare da d’ayar. Kwanciya yayi hawayen bakin ciki suka zubo mashi.
**** ***
Sannu da zuwa Alhaji bansan ka dawo ba sai da Raheena take fad’a mun kana kwance a falo taga kamar baka jin dad’i. Tashi zaune yayi yana fad’in Hajiya ina cikin tashin hankali kawai kitayani da addu’a.
Zama tayi tana fad’in menene ya faru kuma? Hukuncin kisa ya tabbata akan Fawwaz, domin an tabbatar da shine yayi kisan da nake fad’a maki, yanzu haka na yanke masa hukuncin d’aurin rai da rai agidan yari, wallahi kunyar Alhaji M. Sanda nakeyi shiyasa ma na kashe wayata domin shima hukunci ya hau kanshi.
Jinjina kai Momy tayi tana fad’in gaskiya akwai tausayi, amma kadena damuwa, shima fa tsohon Alkali ne, waya san yawan mutanan daya yanke ma hukuncin kisa, wasu ma ratayesu akeyi wasu a jefesu wasu kuma a harbesu, damme zaka damu kanka kamar ka aikata wani babban laifi, abune a fili, dole sai da kowa yaga hujja kafin ka yanke hukunci, kuma ma wannan hukuncin arabuce yake, kana tunanin da ace shine a matsayinka akace d’anka yayi kisa zaice kai abokinsa ne bazai yanke masa hukunci ba? Kada kamanta nasan awajen hada ‘Yan Jarida, da ace baka yanke hukuncin daya dace ba ina mai tabbatar maka da yanzu ka amsa kira daga sama, dan haka ka kwantar da hankalin ka bana so wani abu ya same ka, Allah ya basu hak’urin rashinsa.
Murmushin takaici yayi yana kallon Momy, batasan sirrin da yake k’asa ba da bata fad’i haka ba, amma zai bita ahakan dan baya so ya tashi hankalinsu. Jinjina kai yayi yana fad’in nagode Hajiya, muje ki had’a mun ruwan wanka.
*** ***
Ai na d’auka bazai iya yanke ma Fawwaz hukunci ba, domin naga lokacin da Alhaji M. Sanda yazo wajenshi lokacin da aka fito hutun rabin awa, na tabbata alokacin ya shirya masa abinda ya fad’a.
Ra’eez yace ai Abbah shiyasa muka dage sai da aka binciko mana takardar haihuwarsa, domin nasan irin haka zata iya kasancewa, ajiya Yaya yayi magana da Abban Nabeel, shine yayi mana jagora domin samo takardar, duk da ansha wuya saboda shekarun da yawa, amma kasancewar ana adana duk wasu takardu na ‘yan makarantar yasa aka sameta.
Alhaji Kamal yace dole a gobe zanje Abuja domin ranar litinin za’a k’aro mutane, kafin nan dole asa masu ido gudun karsu gudu, hatta shi shugaban Kwastam d’in da mataimakinsa duk asa masu ido saboda suma sai an hukuntasu.
Alhaji Mansur yace ai naso ya tsaya yayi shari’ar Naseer da ayau sai dai suyi kwanan takura dan dole a akamasu, amma bakomai Allah ya kaimu litinin d’in.
Alhaji Kamal yace amin. Wato abinda ya bani mamaki da kace mani an samu flash d’in a motar Alhaji Maiwada, abun tambaya nan shin dama Naseer ya kai mashi flash d’in ne ko kuma ya akayi?
Alhaji Mansur yace kasan a labarin da Malan Sani ya bamu, a daren da za’a kashe Naseer da Alhaji Maiwada sun had’u da Naseer yana kokarin shiga wajen aikinsu da gudu har suka kusa tureshi, anan ya tsaidasu yace biyoshi akayi, hakan yasa suka taimaka mashi, dalilin da yasa Malan Sani yace wannan yaron shine Naseer saboda ya fad’a masu sunanshi, kuma da suna maganar kisan Farouk da akayi sai Naseer yace masu abokinsa ne, kaji dalilin da yasa Malan Sani yace wannan yaron shine Naseer, kuma da aka samu flash d’in a motar na fad’ama Malan Sani sai yace tabbas aranar da suka d’auki Naseer a kujerar baya ya zauna saboda Alhaji Maiwada baya zama baya.
Alhaji Kamal yace bara mugani idan zan iya had’a kan labarin….. A hasashe na, bayan da Naseer yaje gidan su Fawwaz sai ya iske su Alhaji Marusa suna tattaunawa akan kashe Alhaji Maiwada, bayan daya gano shugaban kwastam suke nufi shine dalilin da yasa Naseer ya nufi ofishin su domin ya bashi wannan d’auka da yayi, kafin ya kai sai aka tura mashi mutane kamar yanda Adnan ya baku labari yaji ance aje a kashe shi har an anshi hotonshi, ganin an biyoshi sai tsoro ya kamashi, bayan da suka taimaka mashi sai yayi tunanin kada ya bada flash d’in a inda be kamata ba domin kaga ai dare ne bazaiyuwu ya iya gane Alhaji Maiwada ba, bayan da suka ajeshi sai yaga dacewar ya b’oye flash d’in a motarsu saboda ya tsorata kada abiyo bayanshi bayan tafiyarsu, ina ganin wannan shine dalilin samuwar flash a motar Alhaji Maiwada.
Jinjina Alhaji Mansur yayi mashi yana fad’in aiki ga mai k’areka, wani abun sai ku tsofaffin lauyoyi, wannan hasashen naka tamkar kana wajen akayi, domin ya tafi dai-dai, tabbas babu ja hakan ce zata kasance, kuma ba kowa bane yasa hakan ta kasance sai Allah, domin ya riga daya tsara komai, kuma Alhamdulillahi gashi nan yau yayi mana rana.
Alhaji Kamal yace Allah yajik’ansu da rahma, mu kuma yasa mucika da imani kuma yasa a kammala wannn shari’ar lafiya, amma fa Alhaji sai kace ma su Ra’eez su kula, domin ayanzu suna gab’ar rikici domin zasu faraucesu tamkar tsohon zakin daya shekara babu abinci, abinda nake gani kada Ra’eez ya aje wannan flash d’in a wajenshi.