ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 71 to 80

Hannu Alhaji Mansur yasa ya ciroshi yana fad’in Alhaji ina ganin ka tafi dashi wajenka hakan zaifi, duk da mun rarraba shi a wayoyin mu amma nafison a k’ara samun wani awajen ka. 

Alhaji Kamal yace shikenan Allah ya bamu ikon tabbatar dashi, ya kuma kare kowa daga sharrinsu. Alhaji Mansur yace amin ya Allah. 

*** ***

Daga duba Adnan wajen Ummu suka wuce, ganin yanda jikinta yayi sauki yasa Ra’eez yace abarshi su tafi da ita, Alhaji Mansur ya kira ya fad’a mawa hakan yasa yace su taho da ita. Sosai sukayima matar da take kula da ita alkhairi da godiya, haka sukabi duk ‘yan wajen da akhairi, har bakin mota likita ya rakosu suka tafi cike da murna. 

Gaba d’aya gidan ya hargitse da murna, Maman Labiba da Mama sun saka Ummu a tsakiya kamar zasu goyata, bayan koke-koke suka zauna akaci abinci, aranar kamar ana biki haka gidan ya kasance. 

Madu kasa zaman waje yayi haka yashigo ciki akayi murnar dashi. Suna zaune saiga Ladi dan Madu ya aika yaro ya fad’a mata, zama tayi tana ta farin cikin samun lafiyar Uwar d’akinta. 

Gaba d’aya sai abun ya dawo ma Ummu sabo, sosai tayi kuka. Bayan da suka dawo sallar isha’i suka zauna a falo Ummu tayi wanka tasa kaya sai ta fito tamkar ba itace tayi hauka ba, sosai tayi kyau, sai dai har yanzu akwai damuwa a fuskarta, duk ta kosa a fad’a mata abinda ya faru. 

Gyara zama Alhaji Mansur yayi yana fad’in Bilkisu inaso ki bani aron hankalinki, na lura idan ba’a sanar dake abubuwan da suka faru ba bazaki tab’a samun nutsuwa ba amma ki dubi girman Allah kada kiyi abinda zai dawo da ciwonki, nasan dai zuwa yanzu kinsan cewar Allah ya amshi Alhaji Maiwada, sai dai bakisan sauran abubuwan ba, dan haka yanzu zan sanar da ke komai…… 

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button