ALKALI NE Page 71 to 80

Sunanshi ta kira hakan yasa ya juyo. Nuress yace Baby kije kiyi wanka naga jikin ki duk yayi sanyi. Murmushi tayi tana fad’in zanyi amma kad’an zo ka sakani nishad’ani sai nayi wankan da hujja. Murmushi yayi yana fad’in yanzu kuwa, ai gara nayi na bankwana tunda anjima zan bar gidanki zuwa gobe na wuce.
**** ****
Wai abokina dan zaka koma waje shine ake kullen ka? Fawwaz yace wallahi ba haka bane, kasan na fad’a maka abinda ya faru lokacin muna sacondary, to ashe munafuki Adnan yaje ya fad’ama Iyayen yaron da nake fad’a maka na yanka da wuka, shine fa aka maido shari’ar babbar kotu, yanzu haka nemana akeyi shi ne fa Dady yace komawa zanyi bazan sake zuwa Nija ba.
Milo yace yana da gaskiya, domin idan ka tsaya nan dole a kama ka, amma haka zaka zauna har lokacin tafiyar ka yayi bazaka d’an shana da budurwarka ba? Fawwaz yace gobe ne fa tafiyar kuma inaji jirgin safe zanbi.
Milo yace gaskiya zanyi kewa, amma ya kamata kazo muje kayi na bankwana. Fawwaz yace gaskiya Dady yace kada naje ko ina, kuma idan na fita dole zai gane.
Milo yace motata bakin glass ne, ka fara fita kashige zan biyoka daga baya kaga babu wanda zai san tare muka fita. Fawwaz yace shikenan, amma dole zaka k’ara mani wannan kayan. Milo yace baka da matsala. Dariya sukayi ya tashi, wayarsa ya aje yana fad’in nan zan barta kada Dady ya kira.
**** ****
Wallaji Oga munyi iya binciken mu bamu samu komai ba, har mun wuce inda wayarsu ta dena aiki amma babu abinda muka samu, kuma bamuga kowa wanda zamu iya zargin wani abu ba, shiyasa muka dawo ko zuwa gobe sai mu canza waje.
Gyara zama Hamza yayi yana fad’in ba sai kun canza waje ba, dole suna nan inda kukaje, ba k’ananan b’arayi bane shiyasa basu bar wata alama da za’a iya ganesu ba, dole sai munsa basira a aikin kafin mu kamosu, dan haka ku barshi sai gobe sannan mu koma.
Sara mashi yayi kafin yayi waje. Wayarsa ya d’auka yana fad’in ina jinka Milo, toshikenan kayi yanda nace dan bana so ya zargeka, gamu nan zuwa kawai ka nuna baka san komai ba. Nagode.
**** ***
Ra’eez tashi muci abinci kaji. Tashi Ra’eez yayi yana dafe kai. Jabeer yace jarumta zakasa aranka insha Allahu komai zaizo da sauki, idan suna tunanin wannan abun da sukayi sunyi nasara to hakan zai jawo masu fitina, domin Allah baya barin azzalumai, idan ka bari damuwa ta kaika k’asa shikenan zasuyi galaba akan mu.
Kallonshi Ra’eez yayi yana fad’in wallahi aikin shari’a ya fitar mun akai, dama can saboda d’aukar fansa na tsaya na karanceshi, amma ina kammala wannan shari’a to zan kammala ta tare da aikina, wallahi Jabeer bazan iya ba, aikin lauya aikine na halaka.
Kada ka sare Ra’eez. Saurin juyowa sukayi jin magana daga bakin k’ofa. Alhaji Mansur ne tsaye yana kallonsu. Duk’ar da kai Ra’eez yayi.
Shigowa yayi yana fad’in wannan fa somin tab’i ne, duk da ma shine mai wahalar domin kafin akai k’arshen shari’ar kowa zaisan matsayinsa, dan haka kadena damuwa yanzu haka Fawwaz yana hannun Inspector Hamza.
Cike da farin ciki Ra’eez ya d’ago kai yana kallonshi. Kai ya jinjina yana fad’in Rafeek ya kirani ya tabbatar mani da haka, kaga komai zaizo da sauki. Jabeer yace amma naji dad’i, sai ka matso muci abincin yanzu.
Murmushi Ra’eez yayi ya matso yana fad’in ko yanzu ma akoma kotu. Dariya Alhaji Mansur yayi yana fad’in banda cika baki fa. Ra’eez yace Allah Abbah naji sauki yanzu, sai dai hankalina yana wajen su Adnan da Abban Nabeel, bana so ta silata su rasa rayukansu.
Alhaji Mansur yace Hamza ya tura amintattun yaranshi, duk da sunje basu samu komai ba amma gobe zasu koma, bazasu tab’a kashe su yanzu ba, nasan zasu jira zuwa jibi kafin nan kuma insha Allahu an kwatosu. Ra’eez yace Allah yasa.
Wayar Alhaji Mansur ce tayi k’ara, yana dubawa yaga Bala bakanike, murmushi yayi yana fad’in ko har an kammal gyaran motar? ‘Daga wayar yayi. Bayan sun gaisa Alhaji Mansur yace Bala an kammala ne? Daga can Bala yace wallahi yanzu haka aikin nakeyi, kasan motar ta dad’e a aje dole sai da na fiddo komai dan tayi kura sosai, amma kuma injinta lafiya lau yake, to bayan da na fito da kujerun motar sai na samu wani tsohon flash, shine nace bara na kiraka na fad’a maka.
Alhaji Mansur yace flash kuma? Saurin gyara zama yayi yana fad’in Bala kana ji na ko, ina so ka samu abinda zaka saka mani shi, ka jira ni nan da mintuna zan kira ka, ina so yazo lagos daga nan zuwa gobe. Kashe waya yayi yana fad’in Allah amin.
Ra’eez yace Abbah lafiya? Murmushi yayi yana fad’in Ra’eez gaskiya tana ta kok’arin bayyana kanta, kasan Bala ya tafi da motar Alhaji zai dubata, shine yace mun a k’asan kujera ya tsinci wani tsohon flash, duk yanda akayi ajiyar Marigayi ce, Alhamdulillahi Allah mungode maka, dole nayi waya a samu wanda zai taho lagos ya kawo manashi, badan ma bana so wani abu ya faru ba da ko amotar haya sai a d’oroshi, amma bari nayi waya da abokina shine shugana ‘yan Union.
*** ****
Ka kwantar da hankalin ka Mr. Kallah babu abinda zai faru, ina fatan baka fad’ama Alhaji Marusa komai ba dan kaga daga ciwo ya tashi? Mr. Kallah yace ban fad’a masa ba amma dole na damu Alhaji Barau, tsohon sirrin mu da yayi shekara da shekaru fa akeson bankwad’owa taya hankalina zai kwanta.
Alhaji Barau yace kada kamanta fa mune kotu, Alhaji M. Sanda bazai tab’a bari asirinmu ya tonu ba, kai tun daga can sama muna da k’afa taya kake tunanin asirin mu zai tonu, kai dai kawai sai kun dawo goben, ka gaishe mani da ‘Yallab’ai Marusa. Dariya sukasa ya kashe wayar.
**** ****
A zabure ta tashi daga kwancen da take ganin sakon daya shigo wayarta, hannu tasa ta murtsike idonta ta d’auka ko bacci takeyi amma tabbas zahiri ne.
Gaba d’aya ta rikice, taya aka amsar mata makudan kud’i har haka, gashi kuma acikin bankin aka amshe su, dole tasan a volk room ne kad’ai za’a iya amsar wad’annan kud’in domin tasan acan take amsar kud’i masu yawa. Suman zaune tayi, wasu hawayen tashin hankali ne suka zubo mata lokacin data kalli balance d’inta, ita da take da kusan million takwas dan d’azu ta turama Khalil kud’i amma yanzu itace take da dubu d’ari biyar.
K’arar sakon daya shigo mata ne yasa tayi saurin dubawa. Ido ta tsura ma sakon tana karantawa a hankali.
*Nasan da ciwo aci amanarka, amma ciwon mai sauki ne idan akayi duba da abinda mutum ya aikata, nasan baki san koni waye ba shiyasa kika fara tarayya dani, ni kuma sanin da nayi maki ne yasa nashigo rayuwar ki, ina fatan hakan zai zama darasi agareki idan kina da sauran Imanin da zaki iya koyon darasin. Nuradden Hambali, ‘Dah ga Shehu Hambali Rigacukum zariya, ko ahaka na barki nasan ya isheki ki tuna komai, kinci amanar mahaifina wanda hakan ya jawo ajalinsa, kin wulak’antani akan nazo neman taimakon kud’in da zan kai Mahaifina asibiti, duk da kece silar jefashi halin da yake amma kika tozartani, tun daga ranar na d’auki alk’awarin tozartaki, na tausaya maki shiyasa na rage maki na cefane, kada kiyi tunanin nemana domin zakisha wahala kuma hakan zai kaiki ga mutuwa ma, ki gode Allah daya baki basirar zab’en akwati mai kyau na ajiyar gwalagwalai, na barki lafiya. Ur’s Nuress.*