ALKALI NE Page 71 to 80

Wurgi tayi da wayar cikin tashin hankali ta bud’e durowa, ihu ta saki ta zube tana wani irin kuka, tabbas Nuress ya gama da ita, bayan da ya mayar da ita tamkar matsarsa, ta siya masa gida da mota, duk hakan be ishe shi ba sai da ya aikata mata cin amana.
Runtse ido tayi a hankali ta furta *Shehu Hambali*
****
Shine saurayinta na farko arayuwarta, tana kaduna yana zariya amma haka yake zuwa wajenta, sunyi soyayya sosai, kasancewarta mai idon cin naira yasa ta tasoshi gaba, shi kuma yana sonta shiyasa baya iya mata gardama, a hankali ta rik’a tatseshi, kafin asa masu rana duk wani abu nashi sai da ta cinye, bayan ansa masu rana akazo had’a lefe tace ga irin wanda takeso, beda kud’i sai gidanshi na gado, dole ta sashi ya raba gidan biyu ya siyar da rabi tace zatayi maleji tasan bayan aure zasuyi kud’i.
Ana saura sati d’aya bikinsu ta had’u da Alhaji Marusa, cikin k’ank’anin lokaci labari ya canza, aranar d’aurin aure Shehu da abokansa suna zaune sukaji an d’aura da wani bashi ba.
A asibiti ya kwana, kwananshi ukku aka sallamoshi, yana zuwa gida ya iske amaryarsa, domin tun acan Kawunsa yasa aka d’aura da diyarshi, ana dawowa kuma aka siya mata komai ta tare.
Yayi kuka har ya gaji, tun daga ranar ya kamu da ciwon zuciya, sau d’aya ya tara da matarsa rabon Nura yashiga, ga talauci, ana haka ya samu labarin inda Karimatu take a Lagos, haka ya wanke kafa yaje, sai dai wulakancin da tayi masa ko kare bazai d’auka ba, tunda ya dawo ya samu littafi ya rubuta tarihinsu, haka yacigaba da rayuwa cikin kunci, duk da matarsa tana kula dashi.
Bayan shekaru Nura ya tasa, tunda ya taso haka ya iske Mahaifinsa babu lafiya, zuwa lokacin basu da komai, ga ciwo, ganin zai mutu suka kaishi asibiti, makudan kud’in aikin da za’a mashi ya tada hankalinsu, haka yazo d’akin Mahaifinsa yana duba takardun gidan ya siyar ayi masa magani.
Littafin daya iske yaja hankalinsa ya karanta. Yayi kuka har ya gaji, a washe gari yaci bashin kud’i ya nufi Lagos, duk da bayanin da yayi mata besa ta tausaya mashi ba, haka ta wulakantashi tasa masu gadi suka masa duka suka wurgoshi waje.
Kafin ya dawo sai zaman makoki ya iske, ta silar haka Mahaifiyarsa ma ziwon zuciya ya kasheta, yasha wahala hakan yasa ya taso da niyar d’aukar fansa. Dole tasa ya siyar da gidan gadonshi yaje ya sayi kaya masu kyau ya koma Lagos da zama.
A hankali ya fara bibiyar Karimatu, wata rana ta fito daga wani Mall suka had’e, shine ya amsar mata kayan ya kai mata mota, tunda ta ganshi ta mace akanshi. Wannan ne silar had’uwarsu, yana sane ya maidata kamar matarsa duk da ba hakan yaso ba, zafin dake ranshi yasa ya biye mata, tayi masa hidima a ciki hada gida da mota, a yau daya kammala aikinsa sai yaji duk wani kunci ya bar zuciyarsa, haka yabar Lagos.
Ajiyar zuciya ta saki mai k’arfin gaske bayan data gama dogon tunani, wato shiyasa Nuress yashigo jikinta har haka kenan, ta aminta dashi hatta da aiken banki shi take turawa ko nawa ne zai karb’o mata kuma be tab’a mata sata ba, ma’aikatan bankin duk sun sanshi dan tace masu k’aninta ne shiyasa da ta aikeshi da check matuk’ar akwai sa hannunta suke bashi kud’i, to ya akayi ma tasa hannu a check d’in? Dole sai idan satar fasaha yayi mata.
Wani sako ne ya sake shigowa wayarta, saurin dubawa tayi… *Nasan zakayi mamakin yanda akayi aka bani kud’i ba tare da sa hannun ki ba, to idan baki sani ba yanda na iya sa hannun ki ko ke bazaki nuna mun iyawa ba, wannan dalilin ne yasa na iya saka hannunki, ada nayi tunanin na cira ta Atm, sai naga bazan ciresu alokaci guda ba, shiyasa na shirya tafiya da rana saboda na samu naje banki, sai kuma naci sa’a aka gama komai na bar bankin kafin kisan anyi, na barki lafiya.*
Wani irin ihu ta saki data tuna abinda yayi mata, da sauri Mai aikinta tashigo, ganin halin da take ciki yasa tayi saurin kiran masu aiki maza, kafin suzo ta sume, dole suka d’auketa zuwa asibitin su.
*** ***
Wai ina Fawwaz yaje ne? Ammi tace tun bayan da abokinsa yazo har ya tafi yana d’aki kwance dan naga lokacin da abokin ya tafi sai dai ban shiga d’akin ba dan nasan baya son takura.
Amma ai nakira wayarsa tana k’ara kuma be d’auka ba, jeki duba mani d’akin, ko kuma muje ma. Turuss sukayi ganin baya d’akin, saurin tura k’ofar band’aki yayi amma baya ciki, hankali tashe ya d’auki wayar Fawwaz yana duba sunan Milo, sai dai babu lambarshi babu alamunta.
Zama yayi zufa tana keto mashi. Ammi tace wai lafiya Alhaji? Kallonta yayi yana fad’in burinki ya cika kin barshi ya fita saboda akamashi dan bakiso yabar k’asar.
Ammi tace mekake fad’a haka, nice zan barshi ya fita? Tomeyayi ma da za’a kamashi? Tsaki yayi yafice daga d’akin.
Wayar Lucky ya kira, yana d’agawa yace Lucky Fawwaz ya fito, inaso ka kokarta ka dawo dashi gida tun kafin aganshi, ka duba gidan hutawarsa kuma ka bincika inda yake zuwa bana so asamu matsala.
Kashe wayar yayi yana huci.
Ur’s.
Nabeelert Lady????[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣3⃣
Haka Alhaji M. Sanda yayi ta zagaye a d’akinshi sam ya kasa kwanciya, duk bayan mintuna sai ya kira Lucky amma amsar d’aya ce ba’a dace ba, dole tasa ya hak’ura ya kwanta ranshi a b’ace.
**** ****
Milo kaga abinda nake fad’a maka ko, nace maka Dady yace kada na fita amma kace na fito gashinan an kama mu, gara kai nasan sakin ka za’ayi ni ko kamani zasuyi zuwa kotu kuma kashe ni za’ayi.
Milo yace yanzu meye amfanin b’oyewar, ko ka tafi idan aka gano kana da laifi ko birnin sin kaje kotu tana da ikon maido ka, shawarar da zan baka kawai kaje ka fad’i iya abinda ka sani zaifi maka.
Hawaye ne suka zubo ma Fawwaz yace yanzu Milo kaine kake bani shawarar naje akashe ni? Dafashi Milo yayi yana fad’in ka fahimce ni abokina, wallahi ban tab’a jin na tsani rayuwar da nakeyi ba sai yanzu, tunda ka bani wannan labarin hankalina ya tashi, ayanzu da ka fad’a mani shari’ar da za’ayi sai nayi nadamar abubuwan dana aikata, kuma insha Allahu daga yau na bar shirmen da nakeyi, shaye-shaye kuwa dole zan barshi domin shine yake samu aikata sauran laifukan.
Kwanciya Fawwaz yayi yasa kuka. Matsowa Milo yayi yana rarrashinsa tare da kwantar masa da hankali.
**** ****
Wajen k’arfe goma motar su Alhaji Marusa ta shigo cikin gidanshi, masu aikin gidan ne suka zo suna masa sannu da zuwa, Mr. Kallah ne ya bud’e mashi mota ya fito tare da sandar da yake dogarawa, duk ya rame sai dai yayi haske.
Har cikin falonshi suka rakashi shida Alhaji Barau dan shine ya d’auko su. Ruwa Mai aikin gidan ta kawo masu, bayan ta aje ta duk’a tana sake gaishe su tana tambayar mai jiki.
Alhaji Marusa yace ina Hajiya fa na kira wayarta akashe? Mai aikin tace ai Hajiya bata da lafiya jiya sai wajen k’arfe d’aya muka dawo daga asibiti dan tace bata son kwana acan shine aka sallameta amma tana can kwance tana cikin ciwo ko magana batayi sai kuka.