ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 71 to 80

Alhaji Marusa yace meya sameta ne? Wallahi ina aiki kawai naji ihunta, kafin nazo na iske ta suma, haka na kira sauran muka kaita asibiti, sai dai lokacin data farfad’o tasa kuka tana fad’in wayyo kud’inta tana kuma kiran sunan Nuress. 

Alhaji Marusa yace to Allah ya kyauta, idan na huta na shiga. Da sauri Alhaji Barau yace ba haka za’ayi ba, kana ji fa tace tana ambaton kud’i hada sunan namiji, ke wanene Nuress? Wiki wiki mai aikin tayi da ido. 

Alhaji Barau yace magana zakiyi dan musan abinda yake faruwa, domin daga bayanin ki na fara fahimtar bakin zaren gara ma ki fad’i abinda kika sani ko nasa a kulle ki. 

Mr. Kallah yace wai Alhaji Barau ina ruwanka, wannan fa maganar cikin gida ce. Alhaji Marusa yace barshi yacigaba nima naji ina son naji komai. Mr. Kallah yace kasan fa ba wata lafiya kake da ita ba meyasa zaka damu kanka. 

Alhaji Marusa yace muna jinki. Kai a k’asa ta fad’a masu waye Nuress har zamanshi a gidan bayan tafiyarsu da irin alak’ar da sukeyi da Hajiya, sai dai batasan abinda ya had’asu ba. 

Mamaki sosai ya kamasu Alhaji Barau, Alhaji Marusa kuwa murmushi ya saki yana fad’in ashe dai maganganun da ake fad’a mani gaskiya ne nine ban yarda ba, lallai Karimatu kin cika butulu, koda yake dama ai nasan za’a rina dama can butulu ce ita, shikenan tayima kanta domin ni mace bata isa ta sani damuwa ba, abu d’aya ne zan rasa nashiga tashin hankali shine kud’i domin sune nasa araina fiye da komai, ko Marwan da naji yaki tsayawa yayi jinyata banji haushi ba, domin dama can ban sasu araina ba dan nasan zasu iya sani ciwon kai. 

Mr. Kallah yace baza’ayi haka ba Alhaji, yakamata kaji abinda ya faru domin ka taimaka mata, muna can fa take fada maka kayanta sun salwanta, kaga kila shima yaron yaudararta yayi. 

Tsaki Alhaji Marusa yayi yana fad’in wallahi babu abinda zan mata, kai na saketa ma saki ukku tazo ta barmin gidana bana buk’atar ta ayanzu. 

Alhaji Barau zeyi magana sukaji an saki kuka, ganin Hajiya sukayi ta shigo tana takawa da kyar, dama daurewa tayi jin ya dawo tazo tayi masa sannu da zuwa. 

Cikin sauri ta shigo tana fad’in Alhaji ka rufa mani asiri, wallahi zan shiga damuwa idan ka rabu dani, duk tarin kud’in da kake bani ban tab’a tunanin siyen kadara ba, abu d’aya nasan ina tarawa sune gwalagwalai, sai kuma kud’ad’e da nake ajewa a banki suma na kwashe su na saro kaya gashi nayi asara, sauran kud’in kuma an sace su da gwalagwalai na, ga Marwan jami’an Madina sun kamashi da kayan kwayoyi yana can dama jiran dawowar ka nakeyi, dan Allah ka rufa mani asiri wallahi sharrin shed’an ne, gaba d’aya Nuress ya takaitani. 

Shiru sukayi suna kallonta da jin irin abinda take fad’a. Alhaji Barau yace to a ina za’a samu shi Nuress d’in? Cikin kuka take fad’in nima ga sakon daya rubuto mani nan, ashe d’aukar fansa ce ta kawoshi waje na…… 

Tsab ta fad’a masu abinda ya faru. Shiru wajen yayi sai sautin kukanta. Alhaji Marusa ne yayi gyaran murya yana fad’in wallahi da zanga wannan yaron sai nayi masa babbar kyauta, wannan yaro shi ake kira da d’an halak, kuma yayi dai-dai, to bari kiji, wallahi babu wanda zai b’ata lokacinsa wajen tayaki nemoshi, kema yanzu ba anjima ba zaki bar mani gidana, suturarki kad’ai zaki d’auka amma ko mota bazaki d’auka ba wallahi, taimako d’aya zansa direba ya kaiki tasha zan baki kud’in mota kitafi, dama bakizo da komai ba. 

Ihu tasa tana fad’in Alhaji kodan Yaranmu da suka girma kada kamun haka wallahi zan gyara, idan ma ka sake ni naji ka barni nayi zaman yarana. 

Tsaki yayi yana fad’in ni yanzu yaro d’aya nake dashi domin nasan Marwan tashi ta k’are dan saudiya hukuncin kisa suke ma duk wanda suka kama yana siyarda miyagun kaya, ni ko wallahi bazan b’ata kwabo na wajen amsoshi ba, shima Khalil idan ya dawo to, idan kuma ya zauna acan zan cigaba da kula dashi. 

Alhaji Barau zeyi magana yayi saurin tashi yana kwalama direba kira, kallonta yayi yana fad’in na baki mintuna ashirin, idan baki shirya ba zaki tafi haka. Jiki na rawa tayi saurin tashi dan tasan halinshi. 

Haka taje ta had’a kayanta kusan akwati bakwai, sai kuka takeyi, Nuress ya cuceta, amma tasan alhakin Hambali ne, ashe dama irin wannan rayuwar zata risketa, yau kusan shekaru talatin da wani abu tana cikin jin dad’i amma rana d’aya komai ya tafi, sam bata tab’a tunanin ta gyara gidansu ba, batayi tunanin ta taimaki wani nata ba, asalima bata cika zuwa gida ba, sai tayi shekara bata leka ba, idan taje ma bata wuce kwana biyu, shima har ta baro gidan bata cin komai na gidan, gashi yanzu zata koma can da zama. 

Haka ta fito masu aiki suka d’aukar mata kaya sai kuka takeyi. Dubu hamsin Alhaji Marusa ya bata, Mr. Kallah ya ciro tubu talatin ya k’ara mata yana bata hakuri, Alhaji Barau kuwa wajen ya bari yana yamutsa fuska. 

Bayan sun tafi Mr. Kallah yace Alhaji ya za’ayi da Marwan? Alhaji Marusa yace Allah yaji k’ansa, yanzu ta Khalil nake kuma kada ku sake tuna mani dashi. Mr. Kallah yace kada kace haka…. Hannu ya d’aga mashi yana fad’in dan Allah. 

Kai Mr. Kallah ya jinjina yana fad’in muje ciki kayi wanka ka huta zamu wuce. Hannu ya mik’a masu yana masu godiya. Alhaji Barau yace zan wuce dan tun d’azu Alhaji M. Sanda yamun waya yana nemana sai munyi waya. Godiya yayi masu suka wuce. 

**** ****

Ido awaje Alhaji Barau yake kallon Alhaji M. Sanda jin abinda yake fad’a. Hannu yasa ya goge zufar data zubo mashi yana fad’in Lucky d’in yace basu ganshi ba? Alhaji yace har yanzu babu labari. 

Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad’in ana wata ga wata, nasan dole su Ra’eez ne zasu sa a d’aukeshi, yanzu ya zamuyi? Alhaji yace nasan Fawwaz bazai tab’a amsa laifinsa ba, kai kuma ina so kayi saurin yanke hukunci da zaran Fawwaz yaki amsa laifinsa shikenan magana ta wuce, domin dole jawabinshi ne kad’ai zai tabbatar da gaskiya, nasan kuma bazai fad’i gaskiya ba, kaga babu Adnan, babu Alhaji Sulaiman, kuma su kad’ai ne suka san gaskiya, kai ko suna nan basu da hujja ahannu iyakarta abaki, kotu kuma da hujjar zahiri take amfani, sannan kuma basu kai su ukku ba. 

Ajiyar zuciya Alhaji Barau yayi yana fad’in hakan ma yayi kuma yasa naji sauki, gara ma Fawwaz d’in yaje kotun hakan zaisa kowa ya yarda dashi tunda bazai fad’i gaskiya ba. 

Alhaji yace magana ta wuce, anjima zanje na duba Alhaji Marusa, bazan sake damuwa akan a nemoshi ba, mubarshi yaje kotun ba shikenan ba. Alhaji Barau yace haka ne. Sallama yayi mashi ya fita. 

**** ****

Rumaisa leka naji ana sallama. Fitowa Rumaisa tayi tana amsawa, cike da mamaki take kallonta. Murmushi Raheena tayi tana fad’in K’anwarmu ko na koma? Murmushi Rumaisa ta saki tana fad’in kishigo mana. 

A falo ta zauna, fita tayi ta kawo mata ruwa tana fad’in sannu da zuwa. Raheena tace kin ganni ko azahar ban bari tayi ba, dole tasani fitowa tun d’azu ma naso zuwa naga safiya tayi da yawa shiyasa na daure har shabiyu tayi. 

Rumaisa tace amma Yaya besan zaki zo ba ko? Raheena tace shine ma silar zuwana, kwana biyu idan nakirashi baya d’auka, duk da nasan yana kan aiki ne amma ko beje ba ai sai muyi waya ko.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button