ALKALI NE Page 71 to 80

Murmushi Rumaisa tayi tana fad’in sosai kuwa. Mama ce tashigo da sallama, saurin risnawa Raheena tayi tana gaisheta. Amsawa Mama tayi cikin sakin fuska, fita tayi ta basu waje.
Ganin sunyi shiru Rumaisa tace Aunty bara naje na d’ora abincin rana kada na bar Mama da aiki, kiyi kallo kafin na gama. Tashi Raheena tayi tana murmushi tace haba muje muyi aikin tare. Rumaisa tace ki barshi zanyi. Wucewa tayi tana fad’in Allah tare zamuyi. Fita Rumaisa tayi tana mamkin karfin halin Raheena, dole haka suka had’u sukayi aikin, Mama kuwa tausayin Raheenar ma takeji.
**** ****
Shiru sukayi suna jiran fitowar likita daga d’akin gwajin da aka shigar da Ummu, Ra’eez addu’a kawai yake Allah yasa Ummunsa ta samu sauki. Jabeer ne ya dafashi yana fad’in insha Allahu zata samu sauki.
Fitowar likita yasa su saurin tashi. Hannu ya mik’a ma Alhaji Mansur suka gaisa. Kasa hakuri Ra’eez yayi yana fad’in an dace likita? Zama yayi yana murmushi, gaba d’aya suka zauna suna kallonshi.
Takardar da take hannunsa ya kalla yana fad’in da farko zan fara da godema Allah, domin shine mai kwantarwa kuma ya tayar, Alhamdulillahi Allah shine abin godiya, yau kam Allah ya kawo mana saukin al’amauran da suka shige mana gaba, acikin mutane goma da aka d’aukesu a wannan asibitin a shekarar 2008 tare da Hajiya yau Allah ya nufa itama ta samu lafiya kamar yanda biyar daga cikinsu tuni an sallamesu.
Cikin farin ciki Ra’eez ya zube k’asa, goshinsa ya kai yana mai sujudar godiya ga ubangiji. Gaba d’ayansu kallonshi sukayi cike da tausayi. ‘Dagowa yayi yaje ya rungume likita yana hawaye.
Alhaji Mansur yace ai babu sauran kuka kuma sai farin ciki, gaskiya nayi matuk’ar farin ciki, likita babu abinda zamuce maka sai godiya kai da Alhaji Usman, hakika kun bada gudummuwa akan Hajiya Bilkisu, Allah ya saka maku da alkhairi.
Zama Ra’eez yayi yana fad’in amin Abbah, wallahi na rasa bakin godiyar ma. Likita yace ai kayi abinda akeso, domin wannan sujadar da kayi ta wadatar, sai kuma aje ayi sadaka.
Jabeer yace wannan kam kullun cikin yinta akeyi, amma dole ta yau ta zama ta musamman. Alhaji Mansur yace ya jikin nata yanzu? Likita yace babu abinda yake damunta yanzu sai rashin kwarin jiki, ina ganin nan da juma’a zaku iya tafiya da ita, dalilin da yasa nace zan riketa anan nafison ku kammala wannan shari’a hankalin ku zaifi kwanciya, kafin nan ta k’ara warwarewa.
Ra’eez yace yanzu zamu iya ganinta? Kai likita ya d’aga yana fad’in kaje ka ganta idonta biyu. Hannun Jabeer yaja sukayi waje da sauri. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad’in bawan Allah, koba komai yanzu zaiji sanyi a ziciyarshi. Likita yace sosai ma.
A hankali ya tura k’ofar d’akin, Ummu tana kwance tayi saurin tashi tana kallon Ra’eez, cikin sauri yaje ya shige jikinta yana sakin kuka. Rungumeshi tayi itama hawaye suka zubo mata, duk da iya abinda ya faru alokacin da Malan Sani yazo kawai zata iya tunawa amma tasan tabbas wani abu marar dad’i ya faru da Abbun Ra’eez.
Shigowar Alhaji Mansur yasa suka nutsu. Zama yayi yana fad’in Ra’eez kai da zaka kwantar mata da hankali shine zakasa mata kuka. Murmushi yayi yana goge idonshi.
Kallon Ummu yayi yana fad’in sannu Hajiya Bilkisu, Allah ya k’ara lafiya yasa iya wahalar kenan. Murmushi tayi tana amsawa, tana son ta tambayeshi amma kawaici ya hanata.
Kamar yasan abinda take tunani yace abinda nakeso dake kisa aranki kome ya faru muk’addari ne daga Allah, nasan akwai tarin tambayoyi a zuciyar ki, amma ki sani yanzu ne kika warke daga ciwo, kuma ciwonki yana buk’atar natsuwa domin abu ne daya had’a da kwakwalwa, dan haka ki adana tambayoyinki insha Allahu ranar juma’a idan muka koma gida zakiji komai, amma inaso kisa jarumta aranki, sannan ki godema Allah bisa baiwar da yayi maki na baki lafiya da yayi.
Kai ta jinjina tana kok’arin maida kwallar idonta. Tashi yayi yana fad’in bara naje Alhaji Kamal yana jira na, Ra’eez ku dawo gida dawuri saboda an kawo wannan sakon na Kano ina so mu bincikeshi. Kai Ra’eez ya d’aga.
Tashi Jabeer yayi yana fad’in bara na koma wajen aiki kai ka zauna anan. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in nagode. Haka suka fita suka barsu, gyara zama Ra’eez yayi yashiga bama Ummu labarin karatunshi.
**** ****
Yauwa kana ji na ko, kada ka bari su b’ace maka gani nan zuwa, inaso kayi amfani da hankali kasan manyan ‘yan fashi ne zasu iya gane kana binsu, shikenan gani nan zuwa.
Cikin mintuna ashirin Hamza ya isa bayan gari, da sauri d’an sandan ya fito daga inda ya b’oye. Hamza yace yauwa sannu Hassan ina ne suka shiga? Hassan yace cikin wancan lungun naga sun shige, sai dai su biyu ne kawai.
Hamza yace kai da sauran ku biyo ta baya, ni kuma zan shiga ta gaba amma kuyi ahankali. Su ukku suka zagaya ta baya yayin da Hamza yawuce ta gaba.
Ruwa suka watsama Adnan wanda yake a sume saboda tsab’ar kishir ruwa da wahalar d’aurin da akayi masa, Abban Nabeel yana d’aure a saman kujera cike da tausayin Adnan, saboda sunfi bashi wahala shi a zaune yake kan kujera yayin da Adnan yake d’aure atsaye, sannan shi Abbah ana bashi abinci da ruwa amma basa bama Adnan.
A firgice Adnan ya farka yana sakin ajiyar zuciya. Abbah yace haba bayin Allah wace irin zuciya ce da ku, idanshi Ogan ku beda d’igon Imani da hasken musulunci ai ku musulmai ne, meyasa zaku biye mashi bazaku bama wannan Yaron ruwa yasha ba, ko babu abinci ai zai iya rayuwa da ruwa.
Dariya d’aya daga cikinsu yasa yana fad’in idan baka sani ba kome mukeyi Oga Lucky yana kallon mu a gidanshi, ko baya zaune yana zuwa zai kunna yaga abinda ya faru, idan ma mun kashe kemarar zai gane, dan haka bazamu b’ata aikin mu ba saboda kud’i muke so.
‘Dayan zeyi magana yaji saukar k’asan bindiga akanshi, k’ara ya saki ya zube a sume, rarumar bindiga d’ayan yayi amma Hamza yarigashi kwad’a masa sanda, fad’uwa yayi yana nishi, saurin shigowa su Hassan sukayi, kama su sukayi suka d’aure suka fita dasu.
Saurin kwance Adnan da Abbah Hamza yayi, sai dai tuni Adnan ya faad’i saboda babu kwari ajikinshi. Ruwa Hamza ya d’auko ya kamoshi, saurin amsa yayi ya fara sha, yana gama sha ya fara amai. Abbah yace muyi saurin barin wajen nan domin Ogansu zai iya zuwa dan yana ganin duk abinda akeyi. ‘Daukar Adnan Hamza yayi sukayi saurin barin wajen.
**** ****
Ra’eez goge flash d’in kafin ka saka shi nasan yayi kura, Ra’eez yace Jabeer wurgomun gashinan gefen ka, d’aukowa Jabeer yayi yana fad’in bara muga ka iya kwallo.
Murmushi Rafeek yayi yana fad’in duk wanda yayi makaranta ai ya iya buga kwallo sai dai matsoraci. Wurga masa Jabeer yayi yana dariya, hannu Ra’eez yasa zai cab’e sai dai bezo a dai-dai ba sai ya fad’a k’asan gado.
Alhaji Mansur yace lallai Ra’eez beyi kwallo ba. Ra’eez yace Allah mugunta yamun. Jabeer zeyi magana wayar Rafeek tayi k’ara, saurin d’auka yayi ganin Hamza.
Saurin tashi yayi yana fad’in amma mungode Hamza, shikenan kayi yanda kace, bana so akaishi asibiti subi bayanshi, shikenan nagode sai mun had’u goben.
Zama yayi yana fad’in Allah maji rokon bawansa, su Hamza sun samu kama b’arayin da suka sace Adnan da Abban Nabeel, yanzu haka Adnan da Abban suna gidanshi ana bama Adnan taimako dan yaji jiki.