ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 71 to 80

Gaba d’ayan su sukayi hamdala. Alhaji Mansur yace Jabeer kira Nabeel ka fad’a mashi dan hankalinsu ya kwanta, kai ma kira Sameer ka fad’a masa. 

Bayan sun kirasu Rafeek yace d’auko flash d’in mu duba. Lek’awa Ra’eez yayi sai yaga ya shige ciki, tasowa yayi yana fad’in sai kazo ka d’aga katifar a d’auko. Murmushi Jabeer yayi yana fad’in Ra go kawai. 

Alhaji Mansur yace Rafeek kama masu naga yau shiriritar tasu ta motsa. Tashi Rafeek yayi yana murmushi ya kama mashi suka d’age katifar. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

4⃣4⃣

Bayan ya d’auko flash d’in har za’a maida katifar Ra’eez yace wallahi Abbah mutanan Da akwai su da dabara, tun kwanaki dana d’aga katifar nan naga wata loka a jiki amma ban bud’eta ba. 

Da sauri Alhaji Mansur ya taso yana fad’in ina lokar take? Ra’eez yace gata nan ajikin gadon hada mukullinta ajiki da gani babu komai ciki tunda ba’a cire makullin ba. 

Saurin lek’awa Alhaji Mansur yayi yana fad’in ku k’ara d’age katifar. Hannu yasa ya bud’e, jawowa yayi saiga ajiyar da Abbu yayi ta flash daya adana sirrikanshi. 

Da sauri ya d’auko yana fad’in ikon Allah, lallai yau muna da sa’a, garinya da ka ga lokar baka d’aga ba? Ra’eez yace wallahi lokacin sauri nakeyi shiyasa ban bud’e ba, tun daga lokacin kuma ban sake tunawa da ita ba. 

Sakin katifar sukayi gaba d’aya suka zo domin ganin abinda yake ciki. Jabeer yace wanne za’a fara sawa? Alhaji Mansur yace ku fara saka mana wanda aka samu yanzu kamar zamufi samun abinda muke so. Sakawa sukayi gaba d’aya suka natsu. 

***

Ajiyar zuciya suka saki lokacin da ya k’are. Hawaye ne suka saukoma Ra’eez a lokacin daya gama jin bayanin Abbunsa, dan daga k’arshe Abbu ya d’auki kanshi yana fad’in wannan sheda ce ta haramtattun kaya da Alhaji Marusa yake shigowa dasu, ko da bana raye ina fatan wannan sheda zata riski adalin Alkali domin a yanke ma masu laifi hukunci dai-dai da abinda sukayi. 

Jinjina kai Alhaji Mansur yayi yana fad’in wato wannan shine abinda ya jawo suka kashe Alhaji Maiwada, domin Abubakar ya fad’a mani sun gano abinda Malan Hassan yasa a gidan Alhaji Marusa shine suka kashe shi, jin yace Alhaji Maiwada yaga komai shine dalilin da yasa suka kashe shi suka d’auke kamfutarsa atunaninsu sun b’atar da kowace sheda basu san Allah yafisu ba. 

Rafeek yace su hud’u ne manyan cikinsu kuma manyan masu laifi, Adebayo da Umar sune k’ananan masu laifi, sai sauran ‘yan dabarsu. 

Jabeer yace wato sun had’a kai an kashe Abbu sai suka d’ora Adebayo amatsayinsa, shi kuma Alhaji Barau bayan tsohon Alkali ya sauka sai ya d’orashi amatsayinsa, shi kuma Umar ya hau matsayin Adebayo, haba shiyasa yanzu ake shigo da abinda akaga dama saboda sune keda abun. 

Alhaji Mansur yace kunna d’ayan mu gani……. 

Bayan ya k’are suka kashe, mayar da flash d’in sukayi cikin jaka. Hamdala sukayi Alhaji Mansur yace shari’a tazo k’arshe, wannan karon mune masu matsayi domin mune masu abun nunawa, Allah sarki Naseer, Allah yaji k’ansa ya kyautata makwancinsa, domin yayi abinda akeso, dan wannan shedar tashi tafi komai muhimmanci, ko ita kad’ai muke da ita basu da hanyar da zasu iya k’aryata zargin da ake masu, ko da kotun da tafi kowace kotu shiririta da rashin iya aiki za’a kai shari’arsu ina mai tabbatar maku dole a yanke masu hukunci, haka zalika ko akwai shugaban k’asa acikinsu k’arewar kud’i da matsayi dole hukunci ya hau kansu, dan haka dole muyi magana da Alhaji Kamal a daren nan kafin gobe. 

Rafeek yace gaskiya Naseer yayi jarumta, amma Abbah a shawarata a fara gabatar da shedar Naseer, bayan da kowa yasan masu laifi idan za’ayi shari’ar su sai agabatar data Abbu. 

Alhaji Mansur yace wannan haka yake, Ra’eez wannan aikin ka ne, dole ka saka wad’annan shedun a mizanin da kowa zai k’ayatu da shari’ar, dan haka kasa tunani irin naku na lauyoyi ka tafiyar da shari’ar yanda zata k’awatu. 

Ra’eez yace insha Allahu Abbah. Tashi yayi yana fad’in Malan Sani komai yazo k’arshe, domin daga gobe ya gama kwanan gidan yari insha Allah, zan kwanta Rafeek ka gaishe da mutanan gidan. 

Tashi Rafeek yayi yana fad’in zasuji Abbah, nima tafiya zanyi ina so naje wajen Hamza kafin nawuce. Alhaji Mansur yace ka masa godiya. Sallama yayi masu ya wuce d’akin da yake kwana. 

Tashi sukayi suka raka Rafeek, bayan ya tafi suka kulle gidan suka dawo ciki. Wanka Ra’eez yayi kafin ya kwanta, bayan Jabeer ya fito ya kwanta yana kallon Ra’eez da yake waya k’asa-k’asa. 

Murmushi yayi ya juya baya yana fad’in gulmamme wayar ma baza’ayi da k’arfi ba. Kyaleshi Ra’eez yayi yana fad’in Pretty kikace Raheena tazo? Rumaisa tace ai naji dad’i da kace bazaka zo cin abincin rana ba Yaya Jabeer yazo ya kai maku asibiti kai da Ummu zakuci, bakaga yanda ta b’ata rai ba, abincin ma kasa ci tayi dole ta tafi. 

Murmushi yayi tana fad’in daga gobe ai zata gane dalilin da yasa naki karb’ar soyayyar ta, idan tana da hankali bazata sake nemana ba. Rumaisa tace wallahi na kosa a gama wannan shari’ar mubar garin nan. 

Ra’eez yace kinsan gobe Kawu a gida zai kwana fa. Rumaisa tace da gaske? Ra’eez yace insha Allahu, domin a gobe zamu nemi ayi shari’arsa dasu Alhaji Barau. 

Rumaisa tace Allah ya tabbatar, aikuwa gobe azumi zanyi. Ra’eez yace muna tare kenan, nima azumin zanyi, kinga zamuyi shan ruwa mai dad’i. Murmushi tayi suka cigaba da firar su. 

Bayan daya kashe wayar ya lek’a fuskar Jabeer yana fad’in kayi hak’uri na hanaka bacci abokina. Tsaki Jabeer yayi ya tureshi yana fad’in dalla matsamun marar kunya. 

Dariya Ra’eez yasa yana fad’i. Haushi kakeji kai baka da abokiyar fira. Jabeer yace Allah tausayin Raheena nake, ina tunanin yanda zataji idan tasan asalin kalar Mahaifinta. Ra’eez yace hakuri zatayi, shiyasa nace ka aureta hakan zai rage mata zafi, kaga…. Saurin juya masa baya Jabeer yayi ya rufe kunnuwanshi yana fad’in sai da safe. Dariya Ra’eez yasa yana fad’in Allah ya kaimu. 

***** *****

*Safiyar alhamis a kotu*

Duk da kasancewar shari’ar ta bama mutane haushi amma hakan be hana suka dawo ba domin suji yanda za’a k’are. A sannu kowa ya shiga kotun suna jiran zuwan Alkali. 

Bayan da Alkali yazo kowa ya samu nutsuwa, sai dai Alkali sam baya cikin natsuwarsa, tunda Lucky ya fad’a masa an kama yaranshi kuma an tafi dasu Adnan hankalinsa yake tashe, gashi Lucky yace bazai zauna ba shima guduwa zaiyi, hakan ne yayi masifar tada mashi hankali, dan ko sauran abokansa bai fad’amawa ba dan yasan suna iya barinshi tunda shine ya zamar ma dole yazo kotu. 

Magatakarda ne ya tashi ya sake karanto shari’ar da za’a gabatar. Bayan ya zauna Alkali ya d’ago kai yana fad’in Brr. Ra’eez muna jiranka, da fatan wannan karon kazo da cikakkar sheda.  

Fitowa Ra’eez yayi yana fad’in nazo dasu ya mai shari’a, kamar yanda kowa ya sani a ranar talata an buk’aci kotu da ta kawo Fawwaz M. Sanda domin ya amsa wasu tambayoyi wad’an da suka shafi wannan shari’ar da akeyi, sai dai bayan da aka je kiransa sai akace baya k’asar wanda na ja da hakan sai aka buk’aci dana tabbatar da shedar yana cikin k’asar nan, alokacin bani da wannan shedar, amma ayanzu ina so kotu ta bani dama domin na gabatar da ita…. Kotu ta baka dama. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button