ALKALI NE Page 71 to 80

Hamza ne yayi ma su Hassan alamu hakan yasa suka fita, ba’a jima ba sai ga Fawwaz sun taso shi agaba duk ya fita hankalinsa, duk da babu wanda ya tab’ashi amma tashin hankali ya hanashi sakat.
Gyara zama Alkali yayi kirjinsa yana dukan ukku-ukku, gaba d’aya zufa ce take zubo masa, amma duk wanda ya kalleshi sai ya d’auka yayi murna da hakan, saboda ba’a gane komai ta fuskarshi.
Bayan da Fawwaz ya shiga ya tsaya sai Ra’eez ya tako kusa dashi.
Ra’eez… Kotu zata so taji cikekken sunan ka.
Sunana Fawwaz Muhammad Sanda.
Ra’eez… Malan Fawwaz ko zaka fad’a mana yaushe ka dawo k’asar nan.
Fawwaz… Zanyi wata d’aya dana dawo.
Ra’eez…. kenan dai baka sake komawa ba? Kai Fawwaz ya d’aga yana fad’in E.
Ra’eez… Malan Fawwaz ko zaka iya fad’a mana sunan makarantar da kayi wato secondary da shekarar da ka gama, da kuma abokan ka wad’an da bazaka iya mantawa ba.
Fawwaz… Kings college nayi, na kammalata a 2008, manyan abokaina kuma guda biyu ne, Sufwan da Adnan, sai dai Sufwan ya rasu.
Ra’eez… A cikin ‘yan ajinku ko zaka iya tuna *Farouk Ahmad Ringim*?
Fawwaz… Shiru yayi yana mazurai, can kuma yace gaskiya na mantashi domin shekarun da yawa.
Ra’eez… Naseer Sambo Jarmai fa?
Fawwaz… Nifa mutane biyu kad’ai na iya rik’ewa saboda sune manyan abokai na, sauran kawai ana gaisawa wasu ma ko magana bamayi.
Ra’eez… Murmushi yayi yana fad’in shikenan bara na tuna maka su, Farouk shine abokin fad’an ka lokacin kuna aji shidda, a binciken da nayi hakan ta faru ne silar wata yarinya mai suna Minal wacce ta kasance budurwa a wajen Farouk, bayan ka ganta kaji kana sonta hakan yasa ka nemi daya bar maka ita, shi kuma ya nuna besan haka ba, wannan shine silar rikicin ku dashi, shin ko zaka fad’ama kotu abinda ya faru a ranar da kukayi fad’a na k’arshe wanda Adnan ne ya raba ku?
Fawwaz… Zufa ce ta fara keto mashi, kallon mutanan kotun ya farayi ko zaiga Dadynsa. Runtse ido yayi yana tuna maganar da sukayi da Dady ana gobe za’a saceshi.
*Fawwaz abinda nakeso da kai ka sani, koda Allah yasa dole sai kaje kotu ina so ka tsaya akan maganar da zan fad’a maka, duk yanda za’ayi kada ka sake ka amsa laifinka, domin ita kotu da hujja ukku take amfani, na farko idan aka samu shedu mutum ukku, na biyu idan aka sami hujjar zahiri kamar ace hujja ta vedio, na ukku idan wanda ake zargi ya amsa laifinsa. Ina so ka sani ayanzu Adnan da Alhaji Sulaiman ne kawai suka. san abinda ya faru kaga kuwa su biyu ne, sannan basu da shedar da zasu iya nunawa saboda mun konata, kai ka d’ai ne zaka iya bada k’ofar a kamaka da laifi, dan haka ina so duk yanda Brr. zai maka tambaya ka nuna baka san komai ba.*
Ajiyar zuciya Fawwaz ya saki yana kokarin tattaro jarumta, kallon Ra’eez yayi yana fad’in gaskiya ni bani da wani abokin fad’a a makaranta, duk wanda yasan mu yasan mu ukku ne, bama shiga harkar kowa bare har muyi fad’a da wani, kuma ni bana soyayya a makaranta.
Ra’eez… Jinjina kai yayi yana fad’in shikenan zaka iya tafiya. Ajiyar zuciya Fawwaz ya saki shida Alkali kafin ya koma ya zauna.
Ra’eez… Ya mai shari’ar ina so kotu ta bani dama domin nayima Alhaji Sulaiman tsohon shugaban makarantar kings college tambaya…. Kotu ta baka dama.
Ra’eez…. Kotu zata so taji sunan ka da kuma bayani akan tsohuwar makarantar ka.
Sunana Alhaji Sulaiman, na rik’e matsayin shugaba amakarantar kings college wanda tuni na aje aiki.
Ra’eez… A shekarar 2008 an samu gawar d’aya daga cikin d’alibanka a bayan gari, shin ko zaka iya fad’a ma kotu abinda ka sani.
Alhaji Sulaiman…. Ajiyar zuciya yayi yana jin wata irin kunya, kallon yawan mutanan kotun yayi kafin ya duk’ar da kai yana fad’in da farko ina so na fara neman yafiyar Iyayen Farouk Ahmad, domin na aikata masu laifi mai girma, duk da bani da hannu cikin kisan da akayi masa amma ina da sa hannu a wajen lullub’e gaskiya.
A shekarar 2008 a ranar alhamis da misalin k’arfe 5:15 na yamma, a ranar ina zaune a ofis na samu waya daga Alhaji Muhammad Sanda wato tsohon Alkalin kotun nan wanda ya kasance Mahaifin Fawwaz, bayan mun gaisa yake fad’a mani yana so nayi masa alfarma, idan har nayi masa haka zai bani mak’udan kud’i, to alokacin kunsan zuciya da kwad’ai, jin yawan kud’in da za’a bani yasa na amince da abinda ya fad’a.
Anan yake fad’a mani Yaronshi Fawwaz yayi fad’a da Farouk tsautsayi yasa ya yankeshi da wuk’a har hakan ya jawo ajalinsa, ayanzu haka yana bayan makarantar wajen band’akuna yana so nayi kok’ari kafin kowa yaga gawar a fitar da ita, hakan ne zaisa babu wanda zai zargi komai tunda ba’a makarantar aka ga gawar ba, kuma lokacin tashi yayi.
Duk da na jinjina abun amma tuna yawan kud’in yasa banyi tunanin komai ba kawai na amince, haka naje da mota ta dan bana so nasa wani ya tayani aje a tona asiri, koda aka ganni nayi cikin makaranta babu wanda ya damu acikin masu aiki saboda sun san nine sunyi tunani zagaye nakeyi.
Haka naje na d’auki gawar nasata a mota na bar makarantar, sai da gari yayi duhu kafin naje na wurgar da ita na bar wajen, tabbas zuciyata taji babu dad’i domin na aikata babban laifi, amma tunda na amshi kud’i a hannu sai na manta da komai, tabbas nayi nadamar abinda na aikata, kuma ina neman alfarmar wannan kotu data sassauta mani akan hukuncina.
Ina da ja ya mai shari’a. Brr. Bajinta ne yayi saurin tashi, risnawa yayi yana fad’in ya mai shari’a nine lauyan Alhaji M. Sanda, ina so kotu ta bani dama domin na kareshi abisa sharrin da Alhaji Sulaiman yake son yayi masa.
Ajiyar zuciya Alkali ya saki dan besan Alhaji M. Sanda yayi magana da Brr. Bajinta ba. kai ya jin jina yana fad’in kotu ta baka dama, amma zaka iya jira Brr. Ra’eez ya kammala tambayoyinsa.
Komawa yayi ya zauna yana fatan nasara. Gaba d’aya kotun ta d’auki hayaniya. Bubbuga tebur Alkali yayi kafin akayi shiru. Hannu yasa yana gyara glass d’insa ganin abinda yake faruwa a cikin kotu. Alhaji Kamal ne ya shigo shida wasu mutane guda biyu, hakan yasa wasu daga cikin kotun suka tashi domin su basu wajen zama.
Ajiyar zuciya ya saki yayin da cikinsa ya fara kad’awa, meya kawo Alhaji Kamal kotu kuma bayan shima Alkali ne? Hannu yasa ya d’auki kofin ruwan da yake kusa dashi yasha, gyara zama yayi yana fad’in Brr. Ra’eez kacigaba.
Ra’eez… Murmushi yayi yana fad’in Alhaji ko zaka iya fad’ama kotu dalilin da ya hanaka halartar kotu a ranar talata bayan kuma kace zaka zo?
Alhaji Sulaiman… Tabbas nayi niyar zuwa kotu domin nazo na fad’i gaskiya, kuma aranar na shirya na fito daga gida domin halartar kotu, sai dai ina barin gida wasu mutane suka tare ni, tunda na tsaya suka fiddo ni ban sake sanin abinda yake faruwa ba sai da na farka na ganni a d’aure ni da wani yaro wanda shima yana da alak’a da wannan shari’ar domin shine abokin Fawwaz da yake magana wato Adnan, tun alokacin na gane dalilin kamo mu, an azabtar da Adnan yanzu haka yana can ana masa magani dan cikin ikon Allah ‘Yan sanda suka ceto mu yayin da suka samu sa’ar cafke mutane biyu daga cikin b’arayin.
Ra’eez… Mungode Alhaji zaka iya tafiya, ya mai…. Saurin tashi Brr. Bajinta yayi yana fad’in ya mai shari’a ina so kotu ta bani dama domin nayi magana akan abinda Alhaji Sulaiman ya fad’a. Da sauri Alkali yace kotu ta baka dama.