ALKALI NE Page 71 to 80

Mamaki ne ya kama mutane, gashi dai Brr. Ra’eez be kammala tambayoyinsa ba amma an bama wani dama. Ra’eez kuwa murmushi yayi ya koma gefe yana kallonshi.
Matsowa Brr. Bajinta yayi yana fad’in Alhaji Sulaiman naji bayanin ka, sai dai kada ka manta kotu tana amfani ne da hujjar zahiri ba ta baki ba, shin ko zaka iya nuna ma kotu hujja akan cewa Alhaji M. Sanda ne ya saka aikata abinda ka fad’a.
Alhaki Sulaiman… Gaskiya bani da wata hujja domin lokaci ne mai tsawo, kuma banyi tunanin d’aukar wata sheda ba saboda nasan bazata mun amfani ba, amma tabbas shine yasani wannan aikin.
Brr. Bajinta… Baka da hujja Alhaji Sulaiman, domin duk wanda yake cikin kotun nan da wanda yasan tsohon Alkali da wanda besanshi ba kowa yasan irin adalcinsa, kuma wannan abun daka fad’a zai iya yuwuwa wasu ne suka biyaka domin kazo ka b’ata masa suna tunda gashi ka kasa gabatar da hujjar abinda ka fad’a, ina rokon wannan kotun da kada tayi amfani da abinda Alhaji Sulaiman ya fad’a. Nagode.
Matsowa Ra’eez yayi yana fad’in Alhaji zaka iya tafiya, ya mai shari’a ina so kotu ta bani dama domin na gabatar da mutanan da suka sace Adnan da Alhaji domin nayi masu tambayoyi.
Dammm gaban Alkali ya fad’i, hannu yasa ya sake d’aukar ruwa yasha, abun goge fuska ya ciro ya goge zufar data sauko masa, da kyar ya sauke ajiyar zuciya yace kotu ta baka dama.
Zuwa yanzu mutane sun fara mamakin Alkali, domin gaba d’aya ya fara rasa nutsuwarshi sai gyaren zama yake ga ruwa da yake yawan sha yana goge fuska.
Bayan da suka tsaya agaban kotu kowa ya natsu yana kallon su.
Ra’eez… Kotu zata so taji sunan ku.
Sunana Gali Haruna… Ni kuma sunana Zubairu Garba.
Ra’eez… Gali ko zaka iya fad’ama kotu dalilin dayasa kuka kamasu Adnan da Alhaji?
Gali… Hakanan muka kamasu domin muna so a bamu kud’i amma babu wanda yasa mu.
Ra’eez… Ai ban tambayeka waya saka ba, kawai dalilin sace su na tambayeka, kenan kaine shugaban ku ko?
Gali gaskiya ba nine shugaba ba bansan inda yake ba dan babu wanda yasan gidanshi a cikin mu iya abinda na sani kenan.
Ra’eez… Zubairu zaka iya fad’ama kotu wanda kuke ma aiki?
Zubairu… Babu wanda muke ma aiki kawai muna neman kud’i ne.
Ra’eez… Shikenan zaku iya tafiya. Ina so kotu ta bani dama domin na gabatar da sheda ta k’arshe…. Kotu ta baka dama.
Jabeer ne ya tashi ya fara had’a kayan da zasu haska domin kowa ya gani. Tunda Alkali ya fahimci abinda suke shirinyi hankalinsa ya tashi, kafin su gama yasha ruwa kusan kofi ukku, sai goge zufa yake yayin da cikinsa yake buk’atar agajin zuwan band’aki, haka ya daure gudun kada ya tona kanshi.
Shiru kotun tayi yayin da kowa ya zuba ido yana jiran a kunna. Hannu Ra’eez yasa ya kunna nan take aka hasko fuskar Fawwaz alokacin da suke fad’a da Farouk. A zabure Fawwaz ya mik’e yana shirin barin kotun, da sauri jami’an tsaro suka cafkoshi, ladabtar dashi sukayi kafin yayi shiru.
Dede lokacin da ya yanki Farouk da wuka da zuwan su Adnan har suka bar wajen. Hannu Ra’eez yasa ya kashe kallon.
Salati akasa gaba d’aya kotun. Wani babban mutum da yake zaune a baya yasa hannu ya goge hawayen da suka zubo masa, tun ranar Talata da yaronshi yaje masa da labarin shari’ar su Farouk yayi alkawarin zuwa domin yaji yanda shari’ar zata kasance danshi ya cire rai da neman adalci a mutuwar Farouk saboda afarko ma beyi niyar neman hakkinsa ba bare kuma yanzu, kawai yazo ne domin yaga wad’an suka tado da wannan shari’ar, sai gashi zuwanshi yayi amfani domin Allah ya nuna mashi wanda ya kashe mashi babban ‘Danshi da idonshi.
Bayan kowa yayi shiru Ra’eez yace ya mai shari’a iyakar abinda zan gabatar kenan, ba sai nace wani abu ba, domin nasan adalcin wannan kotun ne, saboda duk abinda zan fad’a idanuwan kowa sun gani, ina fatan wannan kotu zata bima Farouk hakkinsa, sai magana ta gaba akan shari’ar Naseer Sambo Jarmai. Nagode.
Duk yanda Alkali yaso ya daure kasawa yayi domin jikinsa ya jik’e da zufa, gashi cikinsa yariga ya kad’a bazai iya daurewa ba dole sai yaje band’aki.
Cije baki yayi cikin dauriya yace kotu zataje hutun rabin awa, kafin nan kotu tana buk’atar da a killace Fawwaz da sauran masu laifi. Kottt!!!
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣5️⃣
A sanyaye mutumin yabi bayan d’ansa suka fita, kai tsaye wajen Ra’eez wanda yake tare dasu Alhaji Mansur suna magana ya nufa.
Sallama yayi tare da mik’a ma Alhaji Mansur hannu suka gaisa. Kallonshi sukayi dan basu fahimceshi ba. Kallon Ra’eez yayi yana fad’in barka dai Brr, nasan baka sanni ba, sunana Alhaji Ahmad Ringim, Asalina d’an kano ne, kuma nine mahaifin marigayi Farouk, agaskiya nayi farin ciki da wannan shari’a, na dad’e da fidda ran nemawa Farouk adalci, sai gashi ranar talata Yaro na yazo mani da maganar shari’ar hakan yasa nace zanzo wajenka domin naji wanda yayi silar tado da shari’ar.
Alhaji Mansur yace Allah sarki, ashe dai wad’an da aka zalunta suna da yawa, sannu Alhaji insha Allahu komai yazo k’arshe, kuma ayau zakaga yanda za’a yanke ma azzalumai hukunci, muje can mu zauna na fad’a maka yanda akayi.
****
K’arar burkin mota yasa mutane suka maida hankalinsu inda ya fito, tsayawa sukayi suna kallon Alhaji M. Sanda ganin ya fito daga mota tamkar wanda aka wurgo, ganin yanda mutane suke kallonshi yasa yayi kok’arin dai-daita kanshi.
‘Yan jarida ne sukayo kanshi hakan yasa yayi saurin shigewa kafin su k’araso, dole tasa suka hakura kowa yana jiran d’aukar rahoto.
Alhaji Barau ne ya fito yana sharce zufa yana kok’arin d’aure wandonshi. Cak ya tsaya yana kallon Alhaji M. Sanda yayin da gabanshi yayi wani irin fad’uwa.
Jiki a sanyaye ya samu waje ya zauna yana kokarin shan ruwa, sai da ya gama sha kafin ya goge fuskarshi yana fad’in Alhaji sannu da zuwa.
Ajiyar zuciya ya saki yana fad’in Alhaji Barau me nake shirin ji haka? Brr. Bajinta ya kirani ya fad’a mani halin da ake ciki, duk yanda naso abun ya kasance amma naji ana niyar kai bango, a jiya na shiryama Brr. Bajinta duk yanda zaiyi sai gashi yana fad’a mani wai an kawo irin shedar da muka k’ona a wayar wannan yaron, Alhaji Barau lokacin mu fa yayi, inaji ajikina bamu da sauran mafita matuk’ar aka samu d’ayar shedar da yaron ya d’auka.
Ajiyar zuciya Alhaji Barau ya sauke yana fad’in wallahi Alhaji kaina ya d’aure, yanzu haka saura mintuna a koma kowa yana jiran ayanke hukunci, babban abinda yafi d’aga mani hankali ganin Alhaji Kamal tare da wasu mutane wad’an da nake kyautata zaton daga chamber suke, kasan kuwa abinda yasa Alhaji Kamal ya iya baro ofishinsa kasan babban dalili ne.
Gyara zama Alhaji M. Sanda yayi hankali tashe yace ba dai an kai maganar sama ba? Alhaji Barau yace wallahi bansani ba, amma idan zaka tuna Alhaji Kamal shine Baristan Alhaji Maiwada, sannan acikin wannan vedion da muka kona ta wayar Naseer akwai maganar da mukayi ta yanda za’a kashe Alhaji Maiwada, gaskiya jikina yayi sanyi.