ALKALI NE Page 71 to 80

Ajiyar zuciya Alhaji M. Sanda ya sauke yana fad’in su Alhaji Marusa sun san da wannan maganar? Alhaji Barau yace babu wanda na fad’amawa, sun san dai maganar shari’ar Fawwaz kuma na fad’a masu komai zaiyi dai-dai tunda an kama su Alhaji Sulaiman.
Kallon agogo yayi yana fad’in yanzu dai lokaci ya tafi, abinda nakeso da kai kada ka yanke ma Fawwaz hukuncin kisa. Saurin kallo shi yayi. Kai ya jinjina yana fad’in nasan lokacin da yayi kisan shekarunsa sun kai ya amshi hukunci saboda alokacin zeyi shekara 18, kaga kuwa hukunci ya hau kanshi, amma za’a iya juya abun, kace shekarunsa 14 kawai ya shiga makaranta ne da wuri, kaga hukuncinsa bazaiyi dede dana baligin mutum ba, idan kayi mani haka zanji dad’i.
Alhaji Barau yace abu d’aya zakayi, sai dai ka b’oye takardar shedar haihuwarsa hakan ne zesa kowa ya yarda. Ajiyar zuciya ya saki yana fad’in babu damuwa dan bazasu tab’a gano inda take ba, kawai kayi yanda nace, su Alhaji Marusa kuma ka barsu a kammala wannan shari’ar sannan.
Kai ya jinjina yana fad’in bara na koma lokaci yayi. Alhaji M. Sanda yace zan zauna anan bazan iya fita ba, kome kenan idan kowa yashige zan fice dan bana son had’uwa da ‘yan jarida.
***
Hannu Alhaji Ahmad yasa ya goge hawayen da suka zubo masa, sosai ya jinjina rashin imani irin nasu Alhaji Barau. Kallon su yayi yana fad’in wannan shi ake cema Allura ta tono galma, lallai wannan shari’ar abun so ce, domin d’aya bayan d’aya za’a warware komai, nagode sosai Alhaji Allah ya biyaku da alkhairinsa.
Alhaji Mansur yace amin, ku tashi mu koma gashi can ana shiga. Tashi sukayi suka wuce. Rafeek ne ya fito daga mota, Jabeer yace yauwa gashinan ma ya dawo. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in kasan abinda nake tunani kenan hakan yasa kaji nayi shiru tun d’azu. Jabeer yace ai tunda Abban Nabeel yace za’a samu nasan za’a samu.
Mik’a mashi takardar Rafeek yayi yana fad’in sai da naje na tayasu kafin Allah yasa aka binciko file d’in, ai gaskiya Allah na sammu. Amsa yayi yana fad’in sannu Yaya. Murmushi yayi yace yauwa.
Sameer ne da Nabeel suka k’araso wajensu, gaisawa sukayi suna tambayarsu Adnan da jiki. Sameer yace da sauki dan ya farfad’o, muna ta sauri kada a kammala ashema yanzu za’a koma. Jabeer yace muje gashi can Babban Alkali ya shiga. Dariya sukasa kafin suka wuce.
***
Tsit kotun tayi kowa yana jiran hukuncin Alkali. Bayan daya gama rubuce-rubucenshi ya d’ago yana fad’in kotu taji duka bayanin da aka gabatar mata, bisa manyan hujjojin da aka gabatar ma wannan kotu ta gamsu da cewa Fawwaz Muhammad Sanda shine ya kashe Farouk Ahmad, wanda yayi amfani da wuk’a wajen kashe shi.
Sai dai anan kotu zatayi duba da abubuwa guda biyu, na farko kotu zatayi duba da yanayin shekarun Fawwaz alokacin da yayi kisan kafin ta yanke masa hukunci, na biyu kotu zata kalli yanayin yanda akayi kisan, domin kisa kala-kala ne, akwai kisan da akeyinsa da niya, akwai kuma kisan tsautsayi.
Idan akayi duba da yanayin yanda Fawwaz yayi wannan kisan zamuga cewar zuciya ce ta d’ebeshi, domin ba daga zuwanshi ya yankeshi da wuk’a ba, sai da suka fara kokowa kafin tsautsayi ya ratsa har ya yankeshi da wuk’a, sai na biyu, wannan kisan anyishi a shekarar 2008, alokacin Fawwaz yana da shekara 14, idan akayi duba da yanayin shekarunsa zamu ga cewar be kai shekarun girma ba, domin Mahaifinsa ya tabbatar ma kotu an sakashi makaranta da wuri shiyasa ya kammala ta a k’ananun shekaru, dan gaka kotu zata zartar da hukunci.
Saurin tashi Ra’eez yayi yana fad’in ya mai shari’a ina neman alfarma, inaso kotu ta bani dama domin akwai abinda zan gabatar ma kotu. Langwab’ar da kai Alkali yayi alamun k’osawa da maganganun Ra’eez, ganin kallon da ake masa yasa yayi saurin amincewa.
Murmushi Ra’eez yayi ya fito yana fad’in ya mai shari’a wannan takarda ce ta haihuwar Fawwaz wadda aka samo a cikin file d’insa na makarantar daya kammala secondary d’insa, idan akayi duba da wannan takardar haihuwar za’aga cewar alokacin da Fawwaz yake aji shidda yana da shekaru 18 ne, hakan kuma yayi dai-dai da lokacin daya kashe Farouk, abisa tsarin addinin musulunci duk namiji mai wannan shekarun ya isa ya d’auki hukunci domin yashiga shekarun baligi, sannan kuma ba a wajen da sukayi fad’an ya samu wuk’ar ba, dama can yazo da ita, kunga kenan dama yazo da niyar kashe shi, zamu iya cewa wannan kisa bana ganganci bane, kisa ne da aka shiryashi kafin ayi, bisa wannan hujjar nake so kotu tayi amfani da ita wajen yanke ma Fawwaz hukunci dai-dai da laifinsa. Nagode.
Mik’ama Magatakarda yayi shi kuma ya mik’ama Alkali. Jiki a sanyaye ya amshi takardar yana dubawa. Tabbas takardar haihuwar Fawwaz ce, kuma duk wanda ya ganta zai tabbatar cewar bata k’arya bace.
Ajiyar zuciya ya sauke, shikenan babu sauran wata hanya domin duk wasu shedu sun tabbata dole ayanke ma Fawwaz hukunci. Kallon gefen dasu Alhaji Kamal suke zaune yayi, ganin shi kad’ai suke kallo dole tasa yayi gyaran murya yana fad’in kotu ta gamsu da wannan shedar, dan haka zata yanke hukunci.
Abisa hujjojin da aka gabatar ma kotu kwarara, wanda suka tabbatar da Fawwaz shine wanda ya kashe Farouk, abisa kundin tsarin mulki na k’asa, sashen kisa, amfani da makami ko wani abu, wannan kotu mai albarka ta yanke ma Fawwaz M. Sanda hukuncin d’aurin rai da rai agidan yari, sannan Iyayen shi zasu biya diyyar Farouk ga mahaifansa idan sun buk’aci hakan.
Sannan kotu ta yanke ma Alhaji Sulaiman da Alhaji M. Sanda hukuncin d’aurin wata ukku a gidan yari ko kuma tarar naira dubu d’ari biyu saboda an kamasu da laifin taimakawa wajen b’oye gaskiya.
Mutanan da aka gabatar ma kotu cewar sun kama su Alhaji Sulaiman kotu bata gamsu da hujjar da aka gabatar mata akansu ba, dan haka take umartar da a koma a sake bincikensu a tabbatar da hujja kafin a sake kawo su.
Annan kotu ta kawo k’arshen wannan hukunci, zaku iya d’aukaka k’ara nan da wata ukku idan kuna buk’atar hakan.
Ihu Fawwaz yasa yana kuka yana kiran Dady, saurin rik’eshi akayi aka fita dashi. Tashi Ra’eez yayi yana fad’in ya mai shari’a sai shari’a ta gaba akan Naseer Sambo Jarmai.
Runtse ido Alkali yayi ya bud’e yana fad’in kotu ta d’age sauraron wannan shari’ar zuwa ranar litinin idan Allah ya kaimu. Kottt!!!
Gaba d’aya mutane suka tashi kowa yana fad’in shari’a tayi, haka kowa ya jinjina ma Ra’eez, sannan sun k’ara jinjina adalci irin na Alkali.
Alhaji Barau kuwa ta kofar kotun yayi saurin ficewa dan yasan ‘yan jarida zasu iya rutsashi.
Suna fita Nabeel yaja Abbansa zuwa mota dan yasan ‘yan jarida suna iya rufeshi da tambaya, ayanda yaga jikinsa yayi sanyi yasan dole yana buk’atar hutu, hakan yasa yasashi mota suka bar kotun, ko su Ra’eez sai dai yayi masu waya.
Brr. Ra’eez wane irin farin ciki kake ciki da Allah ya baka sa’a kayi nasara a wannan shari’ar? Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in ina mai cike da farin ciki domin yau Allah yasa Iyayen Farouk sunga yanda aka yankema wanda yayi silar mutuwar d’ansu hukunci, duk da shari’a ce tsohuwa amma yau Allah yasa an kammala ta, har Allah yasa a cikinta an samo wata hanya da zata kaimu ga samo gaskiyar wata shari’ar.