ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Kuka kawai Ummu takeyi lokacin da ta gama sauraron labarin abinda ya faru, a hankali Ra’eez ya matso ya rungumeta shima yana kukan, gaba d’aya sai suka bama mutanan wajen tausayi sai mutuwar ta dawo masu farko. Da kyar Alhaji Mansur ya lallashe su kafin sukayi shiru. Ajiyar zuciya Ummu ta sauke tana fad’in Allah yajik’an ka Alhaji Allah ya kai haske kabarinka, hakika bazan tab’a yafema wad’an da suke dasa hannu a mutuwar ka ba, kuma insha Allahu sai sun wulak’anta. 

Alhaji Mansur yace kiyi hakuri komai yazo k’arshe, idan suna tunanin sun rufe sirrinsu Allah zai haskasu kowa ya gansu, ina so kisa jarumta aranki domin kije kiga yanda azzalumai zasuji kunya agaban idonki. 

Jinjina kai tayi tana goge ido tace dole nasa jarumta kam, kuma zanje har kotun domin na bada sheda akan zaluncin da akayima Malan Sani, domin duk abinda ya faru alokacin ban mance ba. 

Murmushi Ra’eez yayi ya rik’o hannunta yana fad’in Ummu ki kwantar da hankalin ki ina nan babu wanda zai sake saka ki zubar da kwalla, kuma zakiga yanda azzalumai zasu wulak’anta. Kanshi ta shafa tana fad’in Allah yasa Ra’eez. 

**** ***

Dan Allah ka cire damuwa aranka, bazan bari kayi zaman gidan yari ba koda ace bani da kud’in da zan biya tarar da aka saka maku wallahi zanje naci bashi, dan haka kadena damun kan ka. 

Ummah tace mu godema Allah da abun ya tsaya a haka, yau da ace kana dasa hannu a cikin kisan shikenan kaima rayuwar ka acan zata k’are, babu wanda besan k’addara ba, kuma zuciya bata da k’ashi dan haka kadena saka damuwa aranka kaga likita yace jinin ka ya hau. 

Ajiyar zuciya ya sauke yana fad’in dole na damu Nabeel, ka tunafa ko auren farko bakayi ba, kamar yanda wannan abun ya faru ina mai tabbatar maka daga lokacin da ka fara neman aure sai wannan abun ya shafi auren ka, wallahi nayi nadamar abinda na aikata domin nayi maku bakin fenti, taya zan iya fita na kalli mutane, nasan da zaran na fita za’a rik’a nuna ni. 

Nabeel yace ni dai bazan damu ba Abbah, damuwata d’aya idan ka kasance acikin damuwa, duk wanda zai nuna mu yaje yayi ta nunawa domin abun kunyar mu mai sauki ne, ina mai tabbatar maka daga nan zuwa litinin za’a mance da labarin ka, domin za’a tono abinda zai girgiza mutane, dan haka kacigaba da neman yafiya awajen Allah, kud’i kuma gobe zanje na kaisu. 

Murmushi Abbah yayi yana fad’in nagode Nabeel Allah yayi maka albarka kuma ya baka wad’an da zasuyi maka fiye da haka. Gaba d’aya suka amsa da amin. 

*** ***

Washe gari wajen k’arfe goma suka had’u a gidan Alhaji M. Sanda, zaune suke a lambu kowa tashin hankali kwance a fuskarshi. 

Mr. Kallah yace hakika muna cikin tashin hankali babba, dama irin wannan ranar nake tsoro, wallahi jiya banyi bacci ba bayan da naji wai an yanke maka hukuncin d’aurin wata ukku agidan yari, sannan Fawwaz d’aurin rai da rai, shiyasa nayi saurin kiran kowa nace mu had’u a nan dan muna da buk’atar tattaunawa kafin litinin saboda shari’ar da za’ayi ta shafemu duka. 

Alhaji Barau yace wallahi jiya kwana nayi ina gudawa, banyi baccin kirki ba saboda tashin hankalin da yake gaban mu, gani nake duk kunfini kwanciyar hankali domin nine wanda zan yanke hukunci da zaran an tabbatar da mai laifi. 

Alhaji Marusa yace wai an tabbatar da shedar ne? Alhaji Barau yace ai tunda har aka iya samun shedar kisan Fawwaz na tabbata akwai tamu aciki, domin idan baku manta ba alokacin da aka kawo wayar yaron a ciki mukaga duka d’aukar da yayi. 

Alhaji Marusa yace muna da sauran lokaci, nasan wannan shedar dole tana hannun Brr. Ra’eez, abinda nake gani mai zai hana mu aika Lucky ya sato mana ita ba shikenan ba. 

Mr. Kallah yace kana wasa da wannan lauyen, taya zai bar irin wannan shedar da ta riga ta fito a waje d’aya, kada kamanta yasan abinda yake ciki, idan ma an sace ta wajenshi ina da tabbacin ya tura a wani waje, kawai a samo wata hanyar. 

Alhaji Marusa yace bara na kira Lucky naji yanda za’ayi domin ina tsoron yaran can da aka kama idan sukaji duka zasu iya tona komai, kunga idan ma Ra’eez beda wata sheda akan mu sun samu a wajen su. 

Waya ya d’auko ya kira Lucky. Bayan sun gaisa yace wai Lucky kasan halin da ake ciki kuwa? Lucky yace na sani mana meye abun damuwa aciki dan kawai an kama Yarana, zuwa anjima zakuji labarin mutuwarsu dan yanzu haka sun kusa shek’awa, maganar shedar da akace an samu ta kisan Fawwaz kuma ina mai tabbatar maku ita kad’ai suka samu a flash d’in, idan kukayi duba da lokacin daya d’auki vedion zakuga be isa ace yaje ya tura a flash ba har ya nufi wajen shugaban kwastam, nafi tunanin tun bayan daya d’auki kisan Fawwaz ya adanashi a flash d’in kuma agidansu ya b’oyeshi, sauran na wayarshi kuma an k’onasu, dan haka kudena damun kanku idan ba haka ba zaku tona kan ku kuma wallahi ba ruwana dan zan iya barin garin gaba d’aya kuma babu wanda zai iya gano inda nake. 

Jinjina kai Alhaji Marusa yayi yana fad’in na fahimce ka, mungode sai munyi waya. Kashewa yayi ya kallesu yana fad’in kunji dai abinda yace, dan haka ku kwantar da hankalin ku yaran ma zai gama dasu, ai nasan Lucky beda wasa, kuma nima na aminta da bayaninsa. 

Gyara zama Alhaji M. Sanda yayi dan tun d’azu beyi magana ba, kallonsu yayi yana fad’in hankalina ba zai tab’a kwanciya ba matuk’ar ba gani nayi an gama da shari’ar litinin ba, wai meyasa ma acikin mu babu wanda yake hud’d’a da malan tsubbun nan.

Alhaji Barau yace haba dai ‘Yallab’ai kai da kan ka, ai wannan sai mutane marasa ilimin boko sune suke irin wannan harkar, dama can ban yarda da irin wannan abubuwan na Iyaye da Kakanni ba, nafi gane nasa majiya k’arfi suyi mani aiki, amma ka tsaya a wajen wani tsugunnan nan mutum kace shine zai maka aiki, idan Kura na maganin zawo tama kanta mana, kai tunda kake ka tab’a ganin Malamun tsubbu cikin kyakkyawan yanayi, shegu kullum suna zaune a bukka ko arami kamar mujiya, kawai ka barshi Lucky ma ya ishe mu da sauran basirar da muke da ita. 

Alhaji Marusa yace baka had’u da manya bane shiyasa, idan kana buk’atar aiki babu b’ata lokaci kaje wajen manyan arna a cikin tsaunuka anan sai abinda kaso. 

Mr. Kallah yace kudena wannan maganar ta wasu masu tsafi bamu da lokacin yin wannan, kamar yanda Alkali Barau yace aiki ne na marasa ilimin boko nima na goyi bayanshi, muyi amfani da ilimin mu da basirar mu kawai. 

Alhaji M. Sanda yace shikenan Allah ya kaimu litinin d’in muga da abinda zasuje, amma fa asanar dasu Adebayo domin suma acikin mu suke. Alhaji Barau yace wannan ba matsala bace duk za’a fad’a masu, kuma nasan ma dole suji hukuncin dana yanke a kotu tunda akwai sunan ka, abinda yafi kawai bakin mu ya zamo d’aya. Gaba d’aya suka ce badamuwa. 

Alhaji Marusa yace ni yanzu babban abinda yake damuna rashin kud’in da yake so ya sameni, domin jarina yayi k’asa sosai, a yanzu haka bani da jarin da zan iya shigo da kaya masu yawa dole sai dai na fara da kad’an-kad’an, gashi dama ni ba gwanin sayen kadara bane duka gidajena basu wuce ukku ba agarin nan, biyu haya ake aciki, gaskiya duk b’arayin da suka mani satar nan ban yafe masu ba wallahi kuma sai Allah ya saka mani. 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button