ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Zubewa k’asa yayi yana kuka ya riko hannunta yana fad’in kar kimun haka dan Allah, da wanne zanji, idan baki yafe mani ba zan shiga wani hali. Fizge hannunta tayi tana fad’in ina jiranka.
Kai ya jinjina yana fad’in bazan sake zaluntar ki ba, domin nasan yanzu banida amfani agareki, na datse igiyar auren mu, amma dan Allah… Wucewa tayi hakan yasa yayi shiru yana kuka.
Haka ‘yan sanda suka tasa su sukayi gaba, jiyowa Alhaji Barau yayi yana fad’in Ra’eez kace ma Momyn Raheena na yanke igiyar auren mu nasan bazata sake zuwa waje na ba, ka dubi girman Allah ga Raheena nan aduba mani lafiyarta.
Kauda kai Ra’eez yayi yana sakin tsaki. Rafeek yace muje muga halin da Raheena take ciki Ra’eez. Goge hawayen idonshi yayi yabi bayan su Rafeek da Sameer hada Husnah da suka shiga wajen su Jabeer.
Mama ce ta rik’e Ummu suka nufi mota saboda yanda jikinta yake rawa, haka Alhaji Mansur yayi sallama dasu Alhaji Kamal akan zaije gidanshi anjima, saboda yanzu zai kai su Ummu gida, tare da Malan Sani suka nufi motar.
Da sauri wasu ‘yan jarida suka sha gaban Malan Sani. ‘Daya daga cikinsu yace Malan Sani wane irin farin ciki kake ciki akan wannan ‘yanci daka samu yau?
Murmushi Malan Sani yayi yana fad’in yau kam bani da bakin magana sai hamdala awajen Allah, domin wannan nasara da muka samu Allah ne yasa muka sameta.
To me zakace akan wad’an nan azzalumai da suka jefaka cikin wanan tashin hankali? Babu abinda zance masu domin Allah ya fisu, kuma wannan zaman gidan Yari da nayi dama Allah ya rubutoshi acikin K’addarata, Alhamdulillahi nayi godiya ga Allah daya bani ikon cin wannan jarabawa, domin ba k’aramun alkhairi bane Allah ya jarabceka sannan ya baka ikon cin jarabawar, su kuma sai dai nace Allah shine zeyi maganin su.
Zasu sake tambayarsa Alhaji Mansur ya janyeshi yana fad’in sai mu kwana anan. Murmushi yayi ya shiga mota sukayi gida.
Sun dad’e suna zubama Raheena ruwa amma ko motsi batayi ba, cike da tashin Hankali Momy tasa kuka tana fad’in ku taimaka mani kada na rasata dan Allah, jikin Ra’eez ne yayi sanyi ganin halin da Raheena take ciki, da sauri Nabeel da Jabeer suka kai hannu domin d’aukarta, tuni Nabeel ya sureta suka nufo waje domin su kaita asibiti.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
5️⃣0⃣
*Last page*
Kusan mintuna ashirin suna tsaye babu labarin Raheena, Nabeel da Jabeer sun kasa zaune kowa ya tsaya bakin kofar d’akin kamar zai shiga. Ra’eez da yake gefe guda a zaune sai kallonsu yake, duk da shima yana cikin damuwar halin da take ciki amma k’asan ranshi dariyarsu yakeyi dan tuni ya gama harbo jirginsu.
Zama Rafeek yayi kusa dashi yana fad’in wad’an can Romeo’s d’in fa? Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in Yaya kaima ka ganosu kenan? Rafeek yace dama can ai Jabeer yana son Raheena, shi kuwa Nabeel shigar sauri Sonta yayi masa.
Ra’eez yace ga Husnah kuma a gefe. Murmushi Rafeek yayi yana fad’in abun ai yazo da sauki sai wani yayi hakuri.
Wai Husnah lafiyarki kuwa naga duk baki cikin natsuwarki. Ajiyar zuciya ta sauke tare da d’auke idonta daga kan Jabeer, kallon Sameer tayi tana fad’in Yaya. Sai kuma tayi shiru.
Murmushi yayi yace Jabeer ko? Hannu tasa ta rufe fuskarta. Girgiza kai yayi yana fad’in ai na fahimceki tun jiya, kada ki damu matuk’ar kina sonshi zanyima Ra’eez magana, ke kuma sai kiyi amfani da dabarun ku na mata ki janyoshi. Murmushi tayi tana fad’in nagode Yayana.
Fitowar likita yasa gaba d’aya sukayo kanshi. Ofis ya nufa hakan yasa suka bishi banda Nabeel da yayi saurin shiga wajen Raheena.
Ku kwantar da hankalin ku kawai tashiga cikin damuwa ne shiyasa tayi doguwar suma, amma yanzu komai yayi dai-dai munyi mata allurar bacci saboda zuciyarta ta samu natsuwa.
Ajiyar zuciya Momy ta sauke tana fad’in mungode likita, idan ta farka zata warke ko? Kai ya d’aga yana murmushi, kallon su yayi yana fad’in sai dai tana buk’atar arik’a kwantar mata da hankali idan ba haka ba zata iya had’uwa da hawan jini saboda akwai damuwa a zuciyarta.
Rafeek yace insha Allahu za’a kula likita, yanzu me ake da buk’ata? Takarda ya mik’a masa yana fad’in abiya wad’an nan kud’in zasu bada magungunanta. Amsa yayi suka fita suna masa godiya.
A gefenta suka iske Nabeel ya zuba mata ido, komawa da baya Jabeer yayi ganin abinda yake faruwa. Ra’eez yace Momy zamu wuce sai zuwa anjima idan ta farka zamu dawo kila ma asallameta zuwa anjima.
Momy tace nagode sosai Ra’eez Allah ya baku abinda kuke nema. Gaba d’aya suka amsa da amin. Rafeek yace Alhaji Nabeel muje ko. Kai ya sosa yana fad’in kuje Yaya anjima zan tafi. Murmushi sukayi Sameer yace ai gara ka tsaya kayi jinya. Sallama sukayi masu suka fita.
Suna fitowa suka iske Jabeer saman mota yana latsa waya. Ra’eez ne ya matsa yana fad’in Jabeer ya naga ka fito kuma? Jabeer yace jiran ku nake mu wuce. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in Jabeer kada ka kwari kan ka fa.
Kallonshi yayi yana fad’in wai Raheena kake nufi? Kai ya d’aga masa. Saukowa yayi yana fad’in fatana ta samu wanda zai kula da ita idan ta rasaka, kuma Alhamdulillahi ta samu, sai fatan ta amince dashi, kuma nayi murna daya kasance shine.
Hannunsa Ra’eez ya kamo yana fad’in kaine ka santa kuma kaine ya kamata ka kasance da ita, ina maka sha’awar samunta domin nasan wacece Raheena.
Murmushi Jabeer yayi yana fad’in wallahi ko son da nake mata zai iya cutar dani gara ya cutar dani da dai na aureta, bare kuma ni tausayinta yafi yawa a zuciyata, koda ina sonta to kad’an ne, kuma ni bazan iya aurenta ba.
Ra’eez yace dalili? Ajiyar zuciya ya sauke yana fad’in kaine dalilin, da ace wani ne daban da ban sani ba Raheena take ma irin wannan son to zan iya aurenta kuma na mantar da ita komai na koya mata sona, amma bazan iya aurenta ba bayan tana maka irin wannan son, har bada zuciyata bazata tab’a natsuwa ba, domin koda yaushe muna tare da kai, zaka zo gidana itama zata je gidanka, koda ta mance da kai zuciyata zata cigaba da raya mani tana sonka, kaga kuma shed’an beda gwani zai iya d’arsa wani abu a zuciyata shiyasa kaji nace maka bazan iya aurenta ba, ganin yanda Nabeel ya rikice daya ganta nasan cewar Allah ya kawo mata sauyi, dan haka ina so ka bar wannan maganar anan bana so Nabeel yaji kada wani abu ya tsarga zuciyarsa.
Rungumeshi Ra’eez yayi yana fad’in na fahimceka sosai abokina, kuma ko nine haka zanyi, idan ka amince dani zan iya baka mata? Saurin kallonshi Jabeer yayi. Jinjina masa kai Ra’eez yayi.
Murmushi Jabeer yayi yana fad’in na amince. Sakinsa Ra’eez yayi yasa hannu ya juya fuskarshi zuwa wajen dasu Sameer suke tsaye shida Rafeek, saitin da Husnah take ta zuba mashi ido ya aje fuskarshi.
Murmushi Jabeer ya saki har hak’oransa suka fito, shiru yayi suna kallon juna shida Husnah. Hannu Ra’eez yasa ya kamo hannun Jabeer yana fad’in na baka ita amatsayina na Yayanta.