ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Dariya Jabeer yasa ya tureshi. Wucewa Ra’eez yayi yana fad’in Yaya muje. K’arasowa sukayi Rafeek yace an gama Maths d’in ko? Kai Ra’eez ya d’aga yana fad’in sauran English. Dariya sukasa gaba d’aya. 

*** ***

Lokacin da aka shigar dasu Alhaji Barau wajen da sauran fursunonin suke bayan an basu kayan gidan yari sun saka gaba d’aya mutanan wajen sukayo kansu suka sasu tsakiya. 

Yanda kasan zasu rufesu da duka haka suka matse su kowa da abinda yake fad’i yayin da wasu suke masu dariya suna nuna su. Kunya da tsoro ne ya kamasu Alhaji Barau sai b’oye fuskarsu sukeyi. 

Wani daga cikin mutanan wanda da ka ganshi kaga rik’ekken marar ji, shine ya matso tsakiya yana fad’in ansutu jama’a. Kowa yayi shiru suna kallonshi. 

Takowa yayi kusa dasu Alhaji Barau yana tafa hannu, kallonsu yayi yana fad’in *da d’ina da gobe?*.. Mutane suka amsa gaba d’ayansu da *saurin zuwa.* Murmushi yayi yace *Alhaki?* suka amsa da *Kuikuiyo.*…. *Komin nisan jifa?*… *K’asa zata dawo*… *Idan zaka gina ramin mugunta*?… *Ginashi dai-dai tsawonka*… *NASHIGA BAN ‘DAUKA BA?*… *BATA FIDDA ‘BARAWO.*

Gaba d’ayansu suka d’auki ihu suna dariya. Hannu ya d’aga hakan yasa akayi shiru. Kallonsu yayi yana fad’in barkan ku da shigowa duniyar mu, gashi dai kun turo mu cikinta ashe dama zaku zo ku iske mu, dan haka ku sani kunzo wajen da za’a mulke ku, domin wannan gida Masarauta ta ce, Mazaje kuna ji? Gaba d’aya suka amsa da E muna ji. 

Kallonsu ya sakeyi yana fad’in yau dai Allah ya fidda Baba Sani daga gidan nan yayin da ya maido azzalumai a cikin gidan, saboda haka bana so kowa ya d’aga masu k’afa domin da yawa wannan tsohon macucin Alkalin shine ya kawo mu nan, sai wannan guntun Lauyan wato Barau shine yayi silar aka yanke mana hukunci, daga yau babu sani babu sabo tsakanin mu dasu, dole cikin kwana biyu su gane shayi ruwa ne, domin hukuncinsu horo ne mai tsanani. 

Dariya sukasa gaba d’aya yayin da suka sungumesu sama sukayi cikin gidan dasu sai ihu sukeyi. Masu gadi kuwa gefe suka koma suna shan dariya dan sun san basuda yanda zasuyi da su domin Allah ne ya kawo masu azzalumai har gida, hakan yasa kowa ya nufi wajen aikinsa. 

Fawwaz da yake gefe guda yana kallon abinda yake faruwa hawaye ne kawai suke zubo masa na takaici, tunda Amminsa tazo masa da labarin d’azu da safe yake cikin damuwa, da kunya ace shida mahaifinsa suna zaune waje guda, dole ma ya rik’a nisantarsa dan ba zai iya zama kusa dashi ba, gara kowa yayi hanyarsa danshi ayanzu ilimin addini yasa agaba domin nasihar Amminsa ta shigeshi. 

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaji an dafashi. Juyowa yayi sai yaga abokinsa ne wanda yake d’aukar karatu a wajensa. Zama yayi yana fad’in Fawwaz na fad’a maka sai kasa jarumta aranka idan ba haka ba ciwon zuciya zai iya kama ka, nasan da ciwo amma haka Allah ya k’addaro maka kayi hakuri kawai. Jinjina kai Fawwaz yayi yana fad’in nagode. 

**** ****

Zaune suke afalo bayan da Malan Sani yayi wanka dama yayo aski, kaya sababbi Alhaji Mansur ya bashi ya saka, sosai ya fito yayi kyau duk da alamun tsufa da wahala sun fito masa amma ya canza. 

Abdallah yana zaune saman cinyarsa sai shafa kanshi yake yana murmushi, abinci Mama ta zuba masu sai murmushi take kamar amarya. 

Gyaran murya Alhaji Mansur yayi yana fad’in muna k’ara mik’a godiya ga Allah daya nuna mana wannan rana, hakika Allah shine mai iko mai juya al’amura yanda yaso. 

Kallon Ra’eez yayi yana fad’in sannu da kok’ari Ra’eez, hakika kayi kok’ari kuma ka bada gudummuwa sosai, duk da ka fad’a mani duk ranar daka sauke wannan nauyi zaka aje aikin ka amma ban sani ba ko kana da sha’awar cigaba da aikin. 

Saurin girgiza kai Ra’eez yayi yana fad’in wallahi Abbah aikin shari’a ya fitar mun rai, nikam daga yau nagama tsayuwa domin na kare wani, dama saboda haka nayi karatun kuma Alhamdulillahi burina ya cika, takardar aje aikina tana nan na dad’e da rubuta ta kwanan wata kawai zan saka na basu abunsu, nifa na kosa mu bar garin nan ma. 

Dariya suka sa gaba d’aya. Ummu tace maganar ka gaskiya ce Ra’eez, koni bazan barka kacigaba da wannan aikin ba, haka kuma jina nake kamar ina zaune asaman k’aya domin garin nan ya fitar mun arai. 

Jinjina kai Abbah yayi yana fad’in tsarin mu yana kan hanya d’aya, dama na tambayeshi ne dan ban sani ba ko ya canza ra’ayi, amma tunda kana kan ra’ayin ka shikenan Allah ya albarkaci aikin da kayi, sai mu koma Kano a sama maka wani aikin, amma wane aiki kafi so? 

Murmushi Ra’eez yayi 

yana fad’in nafi son naganni ina koyawa a jami’a, domin buri na ne, shiyasa ma dana samu aikin nake son na k’aro karatu, dan arayuwata ina son aikin da yake da lokaci, wanda mutum zai iya tsara lokacinsa da kanshi, kuma kowa yasan koyarwa ce kad’ai take da wannan tsarin.

Kai Yaya makarantar ‘yan mata kuma zakayi aiki? Rumaisa ta fad’a kamar an tsikareta, hannu tasa ta rufe bakinta ganin a inda tayi maganar. Da sauri ta mik’e tayi waje hakan yasa suka kwashe da dariya. 

Umma tace kina da gaskiya ‘Diyata, nima na fara tayaki kishi haka kawai zaije cikin ‘yan mata yarik’a bud’e murya yana koya masu. Mama tace ai Yarona beda kalle-kalle kusha kurimin ku babu abinda zai faru. 

Dariya sukasa Ummu ta duk’ar da kai tana murmushi. Abbah yace tunda dai shine ra’ayinsa zan sama maka, kai ina tabbatar maka wannan shari’ar da kayi zata d’aukaka ka, duk inda ka nemi aiki a fad’in k’asar nan sai ka samu, dan haka mu fara shirin tafiya, Malan Sani gara mu tafi daga baya sai mu dawo asa duk gidajen kasuwa domin mun bar Lagos kenan sai dai muzo da yawo saboda mutanan arziki. 

Malan Sani yace duk yanda kace Alhaji haka za’ayi, domin banki kada na kwana alagos ba yau dan wallahi ta fitar mun arai. Abbah yace shikenan zuwa nan da kwana biyu sai mu tafi kafin nan an kammala komai. 

Madu ne ya kalli Malan Sani yana fad’in dan Allah Malan Sani ka yafe mani, har yanzu ina jin kunyar shedar dana bayar akan ka wancan lokacin. 

Murmushi Malan Sani yayi yana fad’in wai Madu bazaka dena wannan maganar ba, tun yaushe nace na yafe maka, ko nine fa amatsayin ka wallahi shedar da zan bayar kenan, dan haka komai yawuce. 

Abbah yace ai wannan maganar ma abar tada ta, wad’an da suka assasa fitinar ma suna can nasan mutanan gidan Yarin kad’ai sun ishesu, dan haka kowa yayi nagari kansa, ubangiji Allah ya k’ara tsare mana Imanin mu da zuk’atan mu. 

Sai magana ta gaba, muna komawa Kano zanyi bikin Yarana dan bazan jira komai ba, ko kuma hada Raheenar zaka had’a? Waro ido Ra’eez yayi yana kallon Abbah da yake kunshe dariya. 

Umma tace Allah ya kyauta wallahi Yarona bazai had’a zuri’a da wad’annan mutanan ba. Dariya sukasa Abbah yace dama tsokana ce, babu wata amarya agidan Ra’eez sai Rumaisa ta. Malan Sani yace ai duk yaranka ne duk yanda kayi yayi, Allah yasa alkhairi. Gaba d’aya suka amsa da amin. 

*** ***

Maganar ka gaskiya ce Nabeel, dama ka fad’a, zuwa kwana biyu za’a dena labarina, gashi kuma ya tabbata, sai fatan Allah ya yafe mani, dad’in da nakeji yanda Iyayen Farouk suka yafe mani. 

Nabeel yace ai Abbah dama na fad’a maka, duk abinda mutum ya aikata akwai wanda ya aikata abinda yafi nashi, Allah dai ya k’ara tsare mu baki d’aya. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button