ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Ummansa tace amin Nabeel, ya jikin Raheenar kuma? Kallonsu Abbah yayi yana fad’in wacece kuma Raheena? Duk’ar da kai Nabeel yayi yana murmushi.
Murmushi Abbah yayi yana fad’in to nagane, na samu surika kenan, amma a ina take haka? Sosa kai Nabeel yayi yana fad’in Abbah anan garin take, sai dai zuciyata tana cikin damuwa saboda nasan na d’auko abinda bazaku amince dashi ba, nima wallahi bansan yanda akayi zuciyata ta kamu da sonta ba, domin komai ya faru ne ayau, yanzu hakama daga wajen ta nake tana asibiti bata da lafiya.
Hannunsa Abbah ya kamo yana fad’in bana so kasa aranka ni zan iya tauye maka hakkin ka, fad’a mani wacece ita? Kallon Umma yayi yana fad’in ‘Yar gidan Alhaji Barau ce Alkali.
Ajiyar zuciya Umma ta sauke tayi shiru tana kallonsu. Shiru shima Abbah yayi har Nabeel ya fara tsorata da shirunsu, can Abbah ya saki murmushi yana fad’in Allah mai juya al’amura, nine nake tsoron ranar da zaka kawo mani surika arik’a goranta maka abinda Mahaifinka yayi, sai gashi Allah ya k’ulla alak’a tsakanin ka da wacce laifin Mahaifinta ya take na Mahaifin ka so dubu, matuk’ar ita yarinyar tana da hali mai kyau bazan hana ka aurenta ba, domin laifin wani baya shafar wani, Allah ya tabbatar da alkhairi.
Kallon Umma Nabeel yayi yana matse idanu. Hannu tasa ta ja kunnansa tana fad’in amsata kake jira? Kai ya d’aga yana kallonta. Murmushi tayi tace Allah yasa abokiyar rayuwarka kace.
Rungume Umma yayi yana fad’in amin Ummana, nagode sosai, yanzu na samu kwarin guiwar tunkararta da maganar dama amincewar ku nake jira sai dai kutayani da addu’a akwai soyayyar wani a zuciyarta, sanin bazata sameshi ba yasa tashiga cikin wannan halin.
Abbah yace *WAYE NE*? Nabeel yace Brr. Ra’eez ne. Jinjina kai Umma tayi tana fad’in itama ta d’ebo da zafi, koda yake kowama sai yanzu yasan d’an gidan marigayi ne, babu komai, matuk’ar kana sonta kaje ka gwada sa’ar ka. Abbah yace Allah ya baka sa’a. Yace amin.
*** ***
Kwance take ajikin Momy tana kuka, hakuri Momy take ta bata. Raheena tace Momy Dady ya cuceni, ba dan wannan abun daya aikata ba nasan dole na samu Ra’eez, amma kina gani sai dai na hakura dashi, gashima har yana da matar aure, shikenan nasan bazanyi aure ba har na mutu domin Dady ya goga mani bakin fenti.
Shafa kanta Momy tayi tana fad’in zakiyi aure Raheena, domin a yau da kika rasa Ra’eez Allah ya kawo maki wani, abinda nakeso da ke ki daure ki amshe shi, domin idan kika rasashi zaiyi wuya ki sake samun wani, domin shine yazo maki alokacin daya kamata kowa ya gujeki, dan haka ina mai baki shawara daki amshe shi, tunda kika suma yake tare da ke be jima da tafiya ba yace zai dawo, shima abokin Ra’eez ne, sunanshi Nabeel, d’an gidan tsohon shugaban makarantar kings college ne wanda aka yanke ma Mahaifinsa hukunci wan can satin shida Alhaji M. Sanda, yaron kirki ne ina maki sha’awarsa.
Shiru Raheena tayi ta d’ago kai tana kallon Momy, zatayi magana aka turo k’ofa. Nabeel ne dasu Ra’eez suka shigo bakinsu d’auke da sallama.
Saurin duk’ar da kai Raheena tayi dan yanzu kunyar Ra’eez takeji. Momy ce ta amsa masu tana masu sannu da zuwa. Zama sukayi suka gaisheta tare da tambayar mai jiki.
Momy tace gatanan taji sauki likita ma ya sallame mu dama zaman jiranku nakeyi tunda Nabeel yace mujirashi. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in K’anwata babu magana.
‘Boye fuskarta tayi tana murmushi. Jabeer yace ko saboda Nabeel ai sai a kallemu. Murmushi Nabeel yayi yana fad’in dan Allah kubarta ta huta. Tashi Ra’eez yayi yana fad’in anbarta mai Raheena, Momy kutashi mu wuce.
‘Dago kai Raheena tayi zata kalli Nabeel caraf suka had’a ido, da sauri ta kauda kai tana jin fad’uwar gaba. Haka suka tattara suka wuce gida.
Bayan sun ajesu Ra’eez ya fad’a masu nan da kwana biyu zasu koma Kano da zama. Momy tace muma ai bazamu zauna ba Kanon zamu koma gobe ma.
Ra’eez yace ashe muna kusa, to Allah ya taimaka, na manta Alhaji yace na fad’a maki ya datse igiyar auren ku. Tsaki Momy taja tana fad’in shi ya sani dai, nagode maku, kome kenan zamuyi waya.
Ra’eez yace shikenan. Sallama sukayi masu Nabeel yace nima ina nan. Jabeer yace dama kaji munce kaTaho? Ai gara ka zauna kuyi sallama.
Fita sujayi suna dariya. Suna shiga mota Jabeer yace wai da gaske garin nan zaku bari? Ra’eez yace wallahi kuwa. Jabeer yace aikuwa wallahi tare zamu tafi nima na rubuta takardar aje aiki na. Waro ido Ra’eez yayi yana fad’in yaushe? Jabeer yace tun lokacin da nasan zaka aje naka.
Ra’eez yace su Abbah bazasu barka ba ai. Jabeer yace tuni ma suka amince, da ace mace ce ni ai dole na rabu dasu saboda aure, dan haka sun amince zan koma Kano da zama kuma nima rin aikika zanyi.
Rungumeshi Ra’eez yayi hawayen farin ciki suna sakko masa, bayansa ya dafa yana fad’in nagode d’an uwana, hakika tarayyar mu daga Allah take, na dad’e cikin damuwar rabuwar mu, ashe zamu kasance tare, muje dole nayima su Abbah godiya.
Dariya Jabeer yasa yana fad’in sai dai zuwa anjima yanzu muje ka rakani na shigar da kaina wajen Husnah kaga muna komawa sai asha bikin mu tare. Dariya Ra’eez yasa yana fad’in yanzu kuwa.
*** ***
Kafin dare an gama kammala duk wasu labarai, tun daga gidan tv, gidan radio, yanar gizo, kai duk wata kafa ta yad’a labarai sai da aka yad’a maganar shari’ar su Alhaji Barau.
Ba iya Lagos ko Nijeriya ba, gaba d’aya duniya labarin wannan shari’a ya watsu, duk inda kasan akwai yanar gizo to dole su samu wanann labari.
Mutanan da suka kalli wannan shari’a basa kirguwa domin abune daya tab’a zuk’atan mutane, yayin da wasu suke Allah wadai da halin su Alhaji Barau.
Haka Rafeek sai da ya bada firar da suka tab’ayi da Kwamishna a gidan Tv aka kunna, wanda hakan ya jawo karin surutu awajen mutane, kowa yana fad’in ta bakinsa, yanda Kwamishna yake lailaya zance ta kamar mutumin kirki ashe azzalumi ne.
*** ***
Washe gari wajen k’arfe sha d’aya aka aiko kiran Alhaji Marusa. Koda yazo yayi mamakin wanda ya iske a wajen. Zama yayi jikinsa a sanyaye. Jin shiru anki magana yasa Alhaji Marusa yace Khalil!.
Idanuwa kawai Khalil ya tsura mashi ya kasa magana. Matsowa Alhaji Marusa yayi hawaye suna sauko masa, hannu ya kai zai kamo Khalil yayi saurin kwace hannun sa yana fad’in kada ka tab’ani. Alhaji Marusa yace kayi hakuri Khalil, nasan bani da bakin da zan maka magana amma inaso ka d’auka kaddarace ta sameni.
Tashi Khalil yayi yana fad’in babu wata K’addara Dady, kai ne ka zab’ama kan ka wannan rayuwar, ko haihuwar mu da kayi Allah ne yasa zamu fito duniya, kud’in ka sune Mahaifanmu domin sune suke kula damu ba kai ba, bakasan komai namu ba, baka san tarbiyar mu ba, kawai ka turamu cikin turawa dan kada muzauna akusa da kai mutakura maka, Alhamdulillahi ina k’ara godiya ga Allah daya shirya ni, haka ina bakin ciki da Yaya ya tsinci kasan a irin halin da kake ciki, dama kuma barewa bazatayi gudu d’anta yayi rarrafe ba, bansan abinda kayima Momy kenan ba sai jiya Yaya yake fad’a mani da mukayi waya bayan daya samu aron waya dan yaga abinda ya faru da kai.
Tunda aka kamashi so d’aya bakaje ba, shiyasa ya aiko ni na fad’a maka yana tayaka murnar zaman gidan yari, dalilin zuwana saboda ka fad’a mani inda Momy take naje na nemota domin bazan iya barinta ba, saboda itama bata barmu ba alokacin da baka kula damu.