ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Cikin kuka Alhaji Marusa yace kayi hakuri Khalil, nasan ban kyauta maku ba, kuma naji dad’i dana ganka cikin kamala, dama kuma Allah yana fitar da rayayye a jikin matacce, bakasan abinda Momynku tayi bane amma zan fad’a maka……
Hawayen bakin ciki ne suka zuboma Khalil daya gama jin abinda ya faru. Alhaji Marusa yace bayan tafiyarta da kwana biyu na samu labarin mutuwarta, ashe barin ta nan abinda saurayinta yayi mata ya jawo mata ciwon zuciya, ciwon kwana biyu zuciyarta ta kumbura ta mutu, kayi hakuri da ban fa….
Saurin tashi Khalil yayi yana fad’in ya isa, ba sai ka k’arasa ba, Allah yajik’anta, nima zan koma inda ka koya mani rayuwa, Alhamdulillahi na had’u da Ubangida nagari mai ilimin addini, duk da kasancewarsa farar fata amma musulmi ne, kuma ya samar mani shedar zama d’an k’asa, yanzu haka bikin mu za’ayi da d’iyarsa, dan haka daga yau ni ba d’an najeriya bane na manta da ita zan rik’e surukaina amatsayin iyayena.
Rikoshi Alhaji Marusa yayi yana fad’in na amince da haka, kuma naji dad’i, amma inaso kaje gidana cikin d’akina zakaga takardun kadarorina ka d’auka gadonka ne duk… Hannu ya d’aga masa yana fad’in kai da kotu ta bayar da dukiyar ka ina kake da wasu kud’i? Ko kana dasu wallahi bazan sake cin sisin ka ba domin dukansu haram ne, nizan wuce, ina rokon ka da ka yafe mani idan na maka badede ba.
Kuka Alhaji Marusa yasa yana kiran Khalil amma ko juyowa beyi ba. Zubewa yayi a wajen yana wani irin kuka. Masu gadi ne sukazo suka korashi ciki.
Haka ya koma wajen da suke fasa duwatsu, yana kuka yana cigaba da aiki, su Alhaji Barau ne suke bashi hakuri suma kukan suke, tausayin kansu ne ya kamasu, acikin kwana daya komai ya canza masu, lallai duniya abun tsoro ce.
*** ***
Duk wata dukiya ta masu laifi sai da jami’an tsaro suka had’a kanta, gidaje da sauran kadarori duk sun had’a takardunsu za’a sasu kasuwa dan sai an fitar da abinda kotu ta yanke idan anyi saura a basu kayansu.
Su Momy tuni suka kama hanyar Kano wanda Nabeel ne ya d’auki nauyin kaisu dan yakasa ya tsare dole sai da Raheena ta saurareshi, hakan yasa yace zai kaisu domin ya gano waje. Itama Raheena tana jinsa aranta dan tana kokarin cire Ra’eez dan tasan ta rasashi, gara ta amshi Nabeel koba komai yanzu ta fara sanin dad’in so saboda ta samu mai sonta ba wanda take so ba, domin za’a kirata aji lafiyarta, sab’anin da itace take kira.
Lokacin da shugaban kula da hakkin wad’an da kotu ta nema da a damk’ama tarar da ta yanke ya buk’aci ganin Malan Sani da Iyayen Naseer, bayan da yayi masu jawabi sai Malan Sani yace gaba d’aya abinda aka bashi a mik’asu gidan marayu dan bazai iya amfani da kayan haram ba, haka ma Baffa yace.
Wannan abu da sukayi bak’aramun burge mutane yayi ba, anan ya fito yasheda ma ‘yan jarida komai, su kuma suka shiga rattabawa a labaransu, hakan ya jawo masu d’aukaka da addu’oi a wajen mutane, domin ba kowa bane zai iya tsallake irin wannan dukiya ayanzu.
*** ***
Aje aikin Ra’eez da Jabeer ya tab’a zuk’atan manyansu da sauran mutane, domin sun san sunyi asarar hazikai, tun daga can sama aka aiko da sakon ban hakuri da neman alfarma akan Ra’eez ya koma bakin aikinsa amma yace ayi hak’uri ya gama aikin lauya, duk yanda Alhaji Kamal yaso amma hakan be samu ba dole sai dai sukayi hakuri.
‘Yan jarida kowa so yake yayi fira da Ra’eez amma yaki basu had’in kai, da sun tambayesa dalilin aje aikinsa amsar d’aya ce, dama cikar burinsa yake jira kuma ya cika shiyasa ya aje.
Tarin masoyan Ra’eez na garuruwa dama k’asashe basu fad’uwa domin har dena kunna data yayi saboda yawan sako.
*** ***
A ranar da zasu tafi kasancewar jirgin yamma zasubi hakan yasa Alhaji Mansur ya shirya masu taro a harabar gidansu Ra’eez, duk wasu abokan arziki sai da suka zo wannan taron domin su k’ara tayasu murna.
Iyayen Nabeel, Iyayen Sameer, Iyayen Rafeek, Iyayen Jabeer duk sunzo dan sunce zumunci yanzu aka fara.
Anci ansha kuma anyi raha, anan Alhaji Mansur ya tashi yana mik’a godiyarsa abisa goyon baya da kuma had’in kan da suka basu wajen ganin an kammala wannans shari’a, haka yayi ma Iyayen Jabeer godiya da suka amince mashi ya bisu, kuma yayi masu alk’awarin kula dashi kamar yanda zai kula da Ra’eez.
Anan ya kalli Iyayen Sameer yana fad’in ina nema ma ‘Dana Jabeer auren Husnah domin inaso da an koma a had’a bikinsu dana Ra’eez. Dariya akasa nan Dadyn Sameer yace ai duk ‘ya’yanka ne, dan haka na bama Jabeer Husnah.
Cusa fuska Husnah tayi cikin mayafinta tana sakin murmushi. Dadyn Sameer yace biki biyu zanyi, domin tare za’a had’a dana Sameer.
Abban Nabeel yace ashe kuwa za’ayi babban taro, domin shima Nabeel zan had’a nashi da Raheena, kunga kuwa ya kamata ace an tsaida bikin a waje d’aya.
Alhaji Kamal yace idan haka ne nine zan bada wannan shawarar, tunda mutanan Kano sunfi yawa kuma a cikin mu babu d’an asalin garin nan duk munfi kusa da can wajajen ina gani zamu maida bikin mu a kano, domin kuwa nasan zata d’auke mu.
Tafi akasa gaba d’aya kowa yana fad’in hakan yayi dai-dai. Baffa yace gaskiya naji dad’in wannan zumunci da yaran mu suka had’a, ubangiji Allah ya k’ara k’arfafashi har zuwa jikokin mu da masu zuwa bayansu.
Gaba d’aya aka amsa da amin. Alhaji Mansur yace insha Allahu zamu tsara yanda komai zai kasance, sai dai zamu aro al’ada, inaso bikin ya kasance tamkar na Yarbawa, ma’ana ayi komai arana d’aya atashi, a d’aura aure lokaci guda a wuce wajen cin abinci hada matan, ana gamawa amaren kusa akaisu gidajensu, na nesa kuma washe gari atafi dasu.
Dariya suka sa kowa yace wannan yayi ba sai an tsaya yin wani dogon biki wanda za’a fara tun daga laraba sai lahadi a gama. Bayan sun kammala suka kulle taron da addu’a.
Kowa wajen budurwarsa yawuce domin suyi fira. Jabeer da Husnah tamkar masoyan da suka dad’e, dan Husnah ta iya soyayya, tasan yanda zata sa namiji ya mace akanta ya kuma saba da ita cikin kankanin lokaci, abunka da sabon shiga tuni Jabeer ya zurma har yakusa fin Ra’eez kwarewa.
Kallon juna kawai suke fuskarsu d’auke da murmushi. Rumaisa ce ta fara d’auke idonta tana murmushi. Ra’eez yace komai yayi farko zaiyi k’arshe, kinga yanzu sai muje musha biki babu sauran damuwa ko tunanin shiga kotu. Dariya Rumaisa tasa tana fad’in ai wannan kotu taci mana lokaci.
Ra’eez yace shiyasa ai na zab’i wannan aikin domin nasamu damar kula dake, kinga kema sai kishiga makarantar ki anatse, ko har yanzu kina akan bakarki na bakison karatu? Murmushi tayi tana fad’in yanzu kam nake da sha’awar karatu koda bazanyi aiki ba, dan haka ashirye nake dana fara karatun aikin lafiya.
Tafi yayi mata yana fad’in haka nake son ji, ina matuk’ar son na ganki kina taimakon al’umma, duk da nasan zan baki kulawa amma inaso kema kiyi aiki domin kishiga cikin al’umma kirika sanin rayuwa, Allah ya baki sa’a kuma ya barmu tare. Kallonshi tayi tana fad’in Amin Annur.
***
Tsaye suke a tashar jirgin sama suna jiran akirasu, gaba d’ayansu fuskokinsu d’auke suke da farin ciki, acikin matafiyan hada Madu dan shima yace binsu zeyi, duk wanda yaga wannan zuri’a sai sun burgeshi saboda yanda fuskarsu take d’auke da annashuwa.