ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Ra’eez kuwa mutane sai zuwa suke suna gaisawa wasu kuma suna d’aukar hoto. Kiran sunaye da aka fara yasa mutane suka barshi.
Murmushi Jabeer yayi yana fad’in kaga angon Rumaisa. Ra’eez yace ga kuma angon Husnah ba, wai ya akayima bata zo rakiya ba? Jabeer yace nine na hanata dan bana so ta sani kuka.
Dariya sukasa gaba d’aya hada su Rafeek, Sameer, Adnan da Nabeel. Rafeek yace ai dama fa ance farin shiga sunfi saurin iya abu, yanzu ko kunyar Yayunta bakaji kake fad’in haka.
Rufe fuska Jabeer yayi yabar wajen yana fad’in na d’auka bakowa ai. Dariya sukasa Adnan yace gara ka fad’a sai dai kuma baka canka dai-dai ba ka ganta can a baya dan kuka tasa mana sai ta biyo mu hakan yasa Yaya yace ta taho.
Jabeer yace Yaya Sameer kai da kan ka? Gira Sameer ya d’aga yana fad’in bana son k’anwata tayi kuka shiyasa na taho da ita, kaje ku k’ara sallama kafin azo kan ka. Ra’eez yace ba sai yaje ba kamar naji an kira sunanshi fa.
Da gudu Jabeer yayi wajenta yana fad’in d’an bakin ciki saboda kasan da Rumaisa za’a tafi ai dole ka fad’i haka, to sai naje. Dariya suka sa. ajiyar zuciya Rafeek ya sauke yana fad’in gaskiya zamuyi kewa, amma bakomai ai Kano da Lagos babu nisa musamman da sauki yazo yanzu, insha Allahu zumuncin mu bazai lalace ba zai d’ore a haka.
Sameer yace Allah yasa. Haka sukayi ta fira har aka kirasu. Sallama sukayi cike da kewa dan Ra’eez sarkin kuka sai da yayishi, suma duk jikinsu yayi sanyi haka suka rabu cike da kewar juna.
Sai da kowa ya gama shiga jirgin kafin jirgi ya d’aga. Hannun Jabeer Ra’eez ya rik’e yana fad’in aiki ya kammala gashi yayi riba tunda ya sama mani babban aboki kuma d’an uwa. Jabeer yace sosai kuwa domin gashi na samu K’ani daga sama.
Harara Ra’eez ya watsa mashi yana fad’in kamanta, ai kasan dai na girmeka. Juyawa Jabeer yayi yana fad’in dan Allah Ummu nida Ra’eez waye babba? Murmushi Ummu tayi tana kok’arin maida kwallar idonta ta kewar mijinta kafin tace kaine babba.
Dariya sukasa hada mutanan da suke kusa dasu. Gwalo Jabeer yayi ma Ra’eez. Murmushi Ra’eez yayi ya rik’e hannun Jabeer, runtse ido yayi yana fad’in daga k’arshe Allah ya bani Yaya nima. Hawaye ne suka sauko masa. Hannu Jabeer yasa ya jawo kanshi ya kwantar a kafad’arsa yana shafa bayansa.
Murmushin farin ciki Alhaji Mansur yayi yana fad’in Allah ya k’ara had’a kanku baki d’aya. Malan Sani da yake gefe yace amin.
*ALHAMDULILLAH*
Nima anan jirgina ya d’aga zuwa Zango daga Lagos????. Ina mik’a godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafi nawa mai suna *ALKALI NE,* ina rokon Allah ya yafe mani kuskuren da yake ciki, ya kuma bada ikon d’aukar darasin da yake ciki.
Share this
[ad_2]