ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Kauda kai Alhaji Barau yayi yana murmushi a b’oye. Alhaji M. Sanda yace ka kwantar da hankalin ka a kammala wannan matsalar sai asan abunyi. Alhaji Marusa yace shikenan nagode maku. 

***** 

Bayan sun tafi Alhaji M. Sanda yashigo gida, zaune ya iske Ammi tayi tagumi tana tunani. Zama yayi yana fad’in wannan tunanin babu inda zai kai ki, idan zakije ganin Fawwaz kitashi muje. 

Ajiyar zuciya ta sauke tana fad’in yanzu Alhaji hankalin ka har akwance yake da zakace na bar tunani, gudan jinina fa aka yanke ma hukuncin kisa shine zakace na bar damuwa. 

Gyara zama yayi yana fad’in kinsan dai baki fini sonshi ba ko? To tunda kika ga na saka hakuri araina kema kisa, domin Fawwaz bazai tab’a wulak’anta ba, da ace yau ratayeshi za’ayi shine hankalina zai tashi, amma zan ganshi a duk lokacin da naso, kuma ni nasan yanda zanyi domin a sama masa kwanciyar hankali a gidan yari domin ina da mutane acan, kuma kinsan babu abinda kud’i basayi, dan haka kitashi muje idan zaki. 

**** ***

Ya isa haka Fawwaz kadena kuka babu abinda za’ayi maka, yanzu daga nan zanje naga shugaban gidan Yarin zamuyi magana dashi har wajen kwana dole asake maka, ina zaka iya kwanciya da manyan katti wad’an da suka gawurta awajen aikata laifuka, ko aiki ma bazan bari kayi ba, sannan abinci zansa arika baka wanda kake so kaji. 

Kai ya d’aga yana goge idonshi. Ammi tace Fawwaz ka godema Allah da yasa ba kisan lokaci guda za’ayi maka ba, yanzu lokacin da zaka koma ma Allah ne, kaga dai har abada bazaka fita anan ba sai dai a fitar da gawar ka, abinda nakeso da kai ka zama nagari, domin duk wanda yazo gidan yari zai had’u da wad’an da suka fishi komai arashin ji, haka kuma zai had’u da wad’an da yafi, dan haka ina so ka natsu ka koyi darasin rayuwa, kada kace zaka biyema wasu ka lalata rayuwar ka, duk inda aka tara jama’a akwai na banza dana kirki, abinda nakeso da kai kayi kokarin nemo na kirki kayi tarayya dasu, ni dai na yafe maka duk abinda kamun kuma zan cigaba da nema maka shiriya. 

Shiru tayi tana goge hawayen da suka zubo mata. Matsawa Fawwaz yayi ya rungumeta yana kuka, kasa daurewa Alhaji yayi shima ya juya yana goge kwalla, soyayya tasa ya jefa d’ansa cikin matsala. 

Wani daga cikin ma’aikatan yazo yana fad’in Alhaji lokaci yayi. Kallonshi Alhaji yayi sai yaga da alamu sabon d’auka ne dan duk ma’aikatan wajen girmamashi sukeyi. Kai ya jinjina yana fad’in naji, wucesu yayi yana fad’in kai ka taso kaje ku faskara wancan iccen. 

Kuka Fawwaz ya fashe dashi yana fad’in Dady kaji ko, dan Allah kayi wani abu wallahi bazan iya wahala ba, ni gara ma asake mani hukunci arataye ni zaifin mu sauki, kwana d’aya bakaji yanda nakeji ba. Saurin tashi Ammi tayi ta bar wajen tana kuka. 

Tashi Alhaji yayi yana fad’in kada ka damu zanyi magana yanzu. Kud’i yasa mashi aljihu yana bin kayan da suke jikinsa na gidan yari da kallo, wai yau ‘Dansa ne yake sanye a cikin kayan nan, shida yayi shekara da shekaru yana aiko mutane gidan nan, da masu laifi da marasa laifi yau gashi shima an kawo nashi. 

Juyawa yayi yana fad’in sai mun sake dawowa… Barka dai Alhaji Muhammad Sanda. Saurin jiyowa yayi yana kallon dattijon da yake tsaye kusa da Fawwaz. Ido ya tsura mashi sai dai ya kasa gane waye. 

Murmushi Malan Sani yayi yana fad’in dama ai bazaka sheda ni ba, domin ka yanke ma mutane da yawa hukunci zuwa gidan nan ba lallai bane ka iya gane kowa musamman wad’an da sukayi shekaru a gidan, sai dai su daka yanke ma hukuncin har abada bazasu tab’a mance fuskar ka ba. 

Murmushi Alhaji yayi yana fad’in bawan Allah duk wanda kagani agidan nan to abinda ya shuka ne yazo girba.

 Malan Sani yace sosai kuwa, tunda gashi ma har an fara kawo ‘Ya’yanku a gidan, da sannu sauran zasu biyo bayanshi, domin mutanan da sukayi suka agidan nan suna da yawa, lokaci kawai ake jira yayi domin akawo su su girbe shukar su, domin gidannan yana maraba da kowa, mai kud’i ko mulki ko sarauta babu wanda baya d’auka, kuma duk wanda yazo dole ya jeru da sauran mutane. 

Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke yana fad’in kaga Malan ni bansanka ba haka kawai kazo kana gasa mani magana, Fawwaz kaje ciki zanje wajen shugaban gidan nan. 

Juyawa Fawwaz yayi yana goge idonshi, har Alhaji ya juya Malan Sani yace idan baka sanni ba ai kasan Tsohon shugaban kwastma marigayi Alhaji Maiwada, idan har ka tunashi dole ka tuna da direbanshi da ka yanke ma hukunci zuwa gidan nan. 

Dammm!!! Gaban Alhaji ya fad’i, saurin jiyowa yayi yana kallon Malan Sani. Murmushi Malan Sani yayi yana fad’in da sannu zaku maye gurbina yayin da Allah zai d’aukeni naje nacigaba da rayuwa cikin Iyalina. Wucewa yayi yana murmushi. 

Jiki a sanyaye Alhaji yaja k’afarsa zuwa ofishin shugaban gidan Yari, har ya isa yana maimaita maganar Malan Sani. A bakin k’ofar ofishin ya tsaya suna gaisawa da masinjan, magana yayi masa akan yana son ganin shugaban wajen. 

Masinja yace ai baya gari Alhaji. Kallonshi yayi yana kallon motar mutumin, juyowa yayi yana fad’in amma ai ga motarsa can. Masinja yace ai yau yayi tafiyar bayan yazo nan ya ajeta suka tafi a motar abokinsa. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad’in shikenan bani lambarsa. 

Babu musu Masinja ya bashi, juyawa yayi ya tafi yana masa godiya. Tsaki Masinjan yayi yana fad’in munafukan Allah, a hankali asirin ku zai tonu, shekara nawa kana aiki baka tab’a zuwa gidan nan ba sai yau da aka kawo d’an ka, insha Allahu sai Allah ya toni asirin duk wasu masu zalunci, kun lalata Yara sai abinda sukaga dama sukeyi ba dole surik’a kisan kai ba.

Ciki ya shiga, yana shiga 

yace ‘Yallab’ai ya tafi. Tsaki ‘Yallab’an yayi yana fad’in ai tunda naji yanda shari’ar ta kasance nasan dole sai yazo shiyasa na shirya masa hakan, su sauran da ake kawowa suna rayuwa ba mutane bane, a yanda hukuncinsa yazo aikin wahala zeyi sosai, kaga hakan zai zama darasi akanshi, kuma wallahi zan jama sauran ma’aikatan kunne duk wanda ya amshi cin hanci akan wannan yaron zai iya rasa aikinsa, domin ni ba tsohon shugaba bane babu maganar cin hanci, duk wanda yazo gidan nan dole yayi aiki, wasu ma basu da alifi amma haka suke aiki, sai kuma ace za’a kare masu laifi, koya kirani ba zai samu ba ma. 

**** ****

Duk wani shirye-shiryen shiga kotu sun kammala shi, sosai Ummu ta sake a cikin su Mama da Umman Labiba, kuma jikinta yayi sauki sosai, sai damuwar rashin Abbu da take damunta. 

Zaune suke a falon gidan su Sameer sunzo duba Adnan, jingina yayi dan jikinsa da sauki sosai. Nabeel yace abokina kajiyo k’amshin lahira fa. Murmushi Adnan yayi yana fad’in ai azabar kishi bata da dad’i, wallahi mutanan nan basu da Imani, wai shikenan an sake su? Rafeek yace taya za’a sake su, ai tunda Alkali yace acigaba da rik’esu har sai an kawo kwakkwarar sheda akansu dole a rikesu, Hamza ma yace suna nan suna shirya yanda zasu kama Ogansu. 

Jabeer yace ai wannan Ogan nasu shine babban azzalumi, matuk’ar aka kamashi shikenan komai yazo k’arshe, dan yanda na fahimcesu bazasu tab’a tona asirin junan su ba. 

Ra’eez yace Adnan baka da wata hanyar da za’a iya kamashi? Adnan yace gaskiya gidanshi ba cikin gari yake ba, domin wani lokacin idan suna waya ina jin yana fad’a masu su sameshi bayan ruwa, ina kyautata zaton kamar yafi zama acan. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button