ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Rafeek yace shikenan zanyi magana da Hamza saboda su san inda zasu farauceshi. Sameer yace wato a kullum ina k’ara godema Allah da yasa shiryata tazo mani tun ina da sauran kwana, hakika zalunci beyi ba, haka zalika aikata b’arna beda amfani, wallahi ayanxu ne nake jina cikekken mutum.
Rafeek yace sai ma kayi aure zaka k’arasa zama cikekken mutum. Dariya sukasa gaba d’aya. Sameer yace ai na kusa nayi auren nan, akwai Hindatu tana d’aya daga cikin matan da na b’atama rayuwa, sai dai ita ba ta hanyar da nakebi na bi da ita ba, anan bayan layin mu take, Iyayenta suna da rufin asiri haka yarinyar akwai natsuwa, tun farkon ganina da ita sai naji ta burgeni, hakan yasa na fara mata magana har muka fara gaisawa, a hankali sai ta fara sona, duk da bata fad’a mani ba amma na fahimci hakan, ni kuma kawai sha’awarta nakeyi, da haka na fara janta jikina, soyayyar da take mun yasa take bin umarni na, da haka har na samu na biya buk’ata ta da ita, tun daga lokacin na dena kulata, lokacin da Iyayenta suka gane abinda nayi mata tasha duka, inda Allah yaso bata d’auki ciki ba, mahaifinta yaso ya tada maganar sai mahaifiyarta tace ya rufa masu asiri yin hakan kamar tona masu asiri ne, dole haka ya hakura, tun Hindatu tana kirana bar na kulleta dole ta hakura dani, shiyasa a lokacin da nace zanbi wad’an da na b’atama rayuwa na basu hakuri naje har gidansu na bama Iyayenta hakuri itama na bata hakuri, cikin sa’a kuma ta yafe mani, tun daga lokacin kawai sai na fara tunaninta, daga baya na fara kiranta, maganar da nake maku yanzu haka soyayyarmu mukesha kuma za’ayi maganar bikin mu.
Tafi sukasa suna dariya. Rafeek yace gaskiya naji dad’in hakan, kuma nasan zaka kula da ita, dama kuma haka ake so, Allah ya baku zaman lafiya. Gaba d’aya suka amsa da amin.
Wayar Rafeek ce tayi k’ara, yana dubawa yaga Hamza ne, bayan sun gaisa ya fad’a masa mutuwar Yaran Lucky, Rafeek yace shikenan yanzu zan zo. Kashe wayar yayi ya fad’a masu abinda ya faru. Shiru sukayi suna jimamin abun.
Rafeek yace kada ku damu hakan bazai tab’a shedunmu ba, domin su kawai hanyar muce da zata sa mu gano inda Ogansu yake, kuma insha Allahu za’a kamashi. Suka ce Allah yasa.
**** ****
Wai Raheena me yake damunki ne kwana biyu bana ganin ki cikin walwala? Gyara zama tayi tana fad’in Momy haka kawai nakeji kamar bazan samu Ra’eez ba, ada nafi jin zan mallakesa, amma ayanzu zuciyata ta fara tsinkewa, kina gani yaushe rabon da yazo gidan nan, kowane irin aiki yakeyi tunda har muna gari d’aya ai ya kamata ko so d’aya ne ace yana zuwa wajena, idan bezo bama ai akwai waya, wallahi Momy jikina ya fara sanyi.
Hannu Momy tasa ta goge mata hawaye tana fad’in ki kwantar da hankalin ki, tunda har yace maki aiki yakeyi kiyi masa uzuri, kina ganin Alhaji ma yaushe rabon daya zauna muyi fira dashi, da alama wata shari’a zasuyi mai zafi, kinga duka shekaran jiya suka kammala shari’ar yaron gidan Alhaji M. Sanda, yanzu kuma gobe suna da wata shari’ar, shiyasa nima nayi ma Alhaji uzuri saboda nasan yanda aikinsu yake.
Murmushi Raheena tayi tana fad’in Momy kina ganin da sun kammala shari’ar nan zai dawo gare ni? Sosai kuwa, ai ina ganin suna gama wannan shari’ar za’asa maku rana, shima Alhaji lokacin hankalinsa ya kwanta kinga sai ashirya komai, wad’an nan kayan naki idan bakison su kawai zai siyar dasu.
Raheena tace a’a Momy abarsu tukunna. Momy tace shikenan tashi kije kici abinci.
**** ***
*Safiyar litinin a kotu.*
Ur’s.
Nabeelert Lady????[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣7️⃣
*High court Lagos*
Cikar kotu ya bama ma’aikatan wajen mamaki, yanda kasan za’ayi wata shari’ar da bata wuce kwana biyu da faruwa ba, wanda yazo da wuri shi ya samu waje.
Bayan da aka gama shiga Alkali ya shigo, bayan ya zauna kowa ya samu waje ya zauna. Kallon mutanan kotun yake yana so yaga kosu Alhaji Kamal sun zo, aikuwa caraf suka had’a ido, mamakin da yayi yau sun k’ara yawa, hakan yasa jikinsa yayi sanyi, gashi su Alhaji Marusa basu zo ba.
Magatakarda ne ya tashi domin karanto shari’ar da za’a gabatar…… *Kamar yanda aka karanta wannan shari’ar a wancan lokacin kafin a shigo da wadda ta gabaceta, hakan yasa aka d’age wannan shari’ar zuwa yau litinin. A yau litinin 18/12/2019 wannan kotu mai albarka zata saurari k’ararraki guda biyu, ta farko itace wadda zuri’ar Alhaji Sambo Jarmai suka shigar akan mutuwar d’ansu mai suna Naseer Sambo Jarmai, wanda aka tsinci gawarsa a shekaru goma sha biyu da suka wuce a ranar wata juma’a da misalin k’arfe 9:00 na dare a bayan gari, hakan yasa Iyayensa suka shigar da k’ara domin suna buk’atar kotu ta bi masu hakkinsu.*
*Shari’a ta biyu itace wadda Iyalan Malan Sani suka shigar, shari’ace tsohuwa wadda akayita a wannan kotun a shekarar 10/5/2008, inda aka yanke ma Malan Sani hukuncin d’aurin rai da rai a gidan yari, shari’a ce data shafi tsohon ma’aikacin Kwastam Alhaji Hamza Maiwada, wanda ake zargin Malan Sani da kasheshi da kuma yunkurin haikema matarsa a matsayinsa na direbansa, Iyalan Malan Sani sun sake dawo da wannan shari’ar baya saboda suna so asake shari’ar dan basu gamsu da hukuncin da kotu ta yanke a shekarun baya ba.*
Mik’ama Alkali takardun yayi kafin ya koma ya zauna. gaba d’aya kotun ta d’auki hayaniya dan basu san da wata shari’ar ba bayan ta Naseer. Alkali kuwa tamkar wanda aka sama shokin, gaba d’aya jikinsa rawa yakeyi yayin da zufa ta fara keto masa, duk yanda yaso ya daure sai da zufar ta sauko masa afuska tamkar wanda aka zuba ma ruwa, kyalle yasa ya goge fuskarshi kafin ya shanye ruwa kofi d’aya.
Bubbuga tebur Alkali yayi hakan yasa akayi shiru. Jarumtarsa ya tattaro kafin yace lauyen da zai gabatar da shari’a bismilla.
Tashi Ra’eez yayi yana gyara zaman farin glass d’insa, sosai yau yayi kyau sai kace zeyi gasar lauyoyi, gaba d’aya mutanan suka bishi da kallo yanda haibarsa ta fito.
Risnawa yayi yana fad’in ya mai shari’a kamar yanda muka fara karanto k’arar Naseer Sambo Jarmai a wancan satin yanzu ma zamu cigaba, duk da yanzu shari’ar ta zama biyu kuma duk nine zan gabatar dasu, amma ayanzu zamu fara gabatar data Naseer.
Kamar yanda na fad’a an samu gawar Naseer a bayan gari, kuma na gabatar ma kotu da bayanin mutuwarsa da ‘yan sanda suka rubuta, inda bincike ya nuna cewar ankashe Naseer ta hanyar shakeshi da akayi har ya mutu, kuma wannan kisa da akayi kisa ne da aka shiryashi domin a toshe wata kafa wacce ake zargin Naseer da kok’arin tona wani b’oyayyen sirri, hakan yasa aka kashe shi wajen b’oye wannan sirri.
A cikin sirrin da Naseer ya d’auka akwai wanda aka nuna anan ranar alhamis data wuce inda ya d’auki hoton Fawwaz alokacin da ya yanki Farouk da wuk’a, acikin abokan Fawwaz wani yaga lokacin da Naseer yake d’aukarsu, hakan yasa suka sanar da Mahaifin Fawwaz. Ina so kotu ta bani dama domin na kira Adnan d’aya daga manyana abokan Fawwaz domin yayi mana bayanin yanda komai ya faru…… Ajiyar zuciya mai k’arfi Alkali ya sauke kafin yace kotu ta baka dama.