ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Adnan ne ya fito yana takawa da kyar dan har yanzu jikinsa beyi kwari ba. 

Ra’eez… Kotu zata so taji sunan ka da kuma alak’ar ka da Fawwaz. 

Sunana Adnan kuma Fawwaz abokina ne, domin alokacin da mukayi secondary kowa yasan abotar mu saboda mu ukku ne muke tare, duk inda kaga Fawwaz to dole kagan mu nida marigayi Sufwan, abotar mu ta kai har Iyayen mu sun san mu atare. 

Ra’eez… Kotu tana buk’atar kayi mata cikekken bayani akan abinda ka sani na kisan Farouk da kuma abinda ya shigo da Naseer cikin maganar. 

Adnan…. E to, kamar yanda kowa ya gani a vedion da aka nuna Fawwaz ya kashe Farouk wanda ba kowa bane ya d’auki wannan vedio sai Naseer, kuma Naseer d’an ajin mu ne muna gaisawa dashi, alokacin da Fawwaz ya kashe Farouk bayan munzo muka iske ta’asar da yayi sai hankalin mu ya tashi, kasancewar mu abokai yasa mukayi kokarin rufama Fawwaz asiri, nine na d’auki wauk’ar na jefata a wani rami da ake tara bola, bayan da muka juyo zamu tafi sai na hangi Naseer yana d’aukar mu, sai dai muna jiyowa shi kuma ya bar wajen da gudu. 

Bayan da mukaje muka sanar ma Dadyn Fawwaz sai yace kada mu damu, abinda yake so shine kada mu fad’ama kowa yasan yanda zaiji da komai. 

Washe gari dana tambayi Fawwaz ya naji ance a bayan gari aka samu gawar Farouk, shine yake fad’a mani Mahaifinsa ya had’a baki da shugaban makarantar aka fitar da ita. 

A ranar da za’a kashe Naseer munzo gidan su Fawwaz sai muka iske Dadynsa da bak’i a waje, bayan mun gaisa sai ya bukaci da mu fad’a masu kwatancen gidansu Naseer kuma mu tura masu hotonshi, haka muka bashi muka tura masu hotonshi. 

Washe gari sai mutuwar Naseer naji, tabbas na girgiza da mutuwarshi, kuma har gobe ina ganin laifina, domin nine na fad’a cewar ya d’auki vedio, da ban fad’a ba babu yanda za’ayi asan shine, tun daga lokacin na fara janye masu Fawwaz har Allah yasa muka gama kowa ya kama gabansa, ina mai bama Iyayen Naseer hakuri abisa sakarcin da nayi. 

Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in mungode Adnan zaka iya tafiya. Ya mai shari’a wannan shine Adnan abokin Fawwaz, kuma kowa yaji wanda yasa aka kashe Naseer saboda kawai a b’oye gaskiya ina…. 

Saurin tashi Brr. Bajinta yayi yana fad’in ya mai shari’a ai wannan shedar baki ce kawai Adnan ya bayar, kuma shi kad’ai ne ya bada sheda wanda kowa yasan cewar mutum d’aya baya sheda, domin za’a iya biyanshi yazo ya b’ata Alhaji M. Sanda. 

Miyau Alkali ya had’iye dan ya riga daya sadakas, yasan Brr. Bajinta yana kokarin kare Alhaji M. Sanda ne kawai saboda ba komai ya sani ba. Ruwa yasha kafin yace Brr. Ra’eez kotu tana buk’atar cikakkar sheda domin bazata amshi wannan hujjar da aka bayar ba. 

Risnawa Ra’eez yayi yana fad’in ya mai shari’a zan so kotu ta bani dama domin na nuna mata hujjata ta k’arshe wadda zata tabbatar da abinda Adnan ya fad’a gaskiya ne… Kotu ta baka dama. 

Tashi Jabeer yayi ya had’a kayan da za’a kunna. Tunda Jabeer ya tashi Alkali yaji cikinsa ya kad’a, zufa kawai take keto masa ta ko ina, gaba d’aya kyallen dayake goge zufar ya jike. Mutane kuwa mamakin yanda hankalin Alkali ya tashi suke dan zuwa yanzu ya kasa b’oye tashin hankalinsa, zaman kanshi a d’osane yake. 

Shiru kotun tayi yayin da fuskokin Alhaji Marusa dana Mr. Kallah suka bayyana, sai gefen fuskar Alhaji Barau saboda shi a gefe yake hakan yasa ba’a d’aukoshi duka ba, idan ba wanda yasanshi ba bazai iya shedashi ba, sai kuma bayan Alhaji M. Sanda danshi ya bama mai d’aukar baya. 

Muryoyinsu ne suka fara cika kotun, muryar Alhaji Barau itace ta tonashi, domin yana magana wasu suka fahimci shine, sai kuma lokacin da aka fara ambatar sunanshi, haka suka cigaba da sauraron shirin da suke akan kashe Alhaji Maiwada da kuma yanda zasu sa akashe Naseer. 

Babban abinda ya k’ara tabbatar da Alhaji Barau ne awajen alokacin da Alhaji M. Sanda yake fad’in *Brr. Barau idan har kayi mani wannan taimakon ina mai tabbatar maka kaine Alkalin gobe*. Zuwa lokacin mutanan kotun kasa jurewa sukayi dole wajen ya d’auki hayaniya, dama kuma d’aukar tazo k’arshe. Hannu Jabeer yasa ya kashe. 

Jiyowar da Ra’eez zeyi sai dai yaga wayam a kujerar Alkali domin ya sulale ta kofar da take kusa dashi????. Ra’eez besan lokacin da dariya ta kwace masa ba, hannu yasa ya toshe bakinsa yana girgiza kai, ai da mutane suka fahimci abinda yake faruwa sai kotu ta hargitse da dariya tare da surutu. 

Duk yanda aka so mutane suyi shiru abun ya faskara, dole sai Magatakarda ne ya hau sama ya buga tebur hakan yasa kowa yayi shiru ya juyo sun d’auka Alkali ne ya dawo. ‘Daya daga cikin manyan ma’aikatan kotun ne ya mike yana fad’in an d’age wannan shari’a zuwa lokacin da za’a sanar. 

Haka kowa ya fito daga kotun yana fad’ar yanda akayi, ‘Yan jarida kuwa sun cika wajen kowa yana son yaji yanda za’ayi, kamar ance su kalli gefe sai ganin ‘Yan sanda sukayi sun saka Alhaji Barau a tsakiya suna shirin barin kotun dashi, ai da gudu ‘Yan Jarida sukayi wajen, sai dai kafin su kai sai kurar motar suka iske. 

Abinda ya faru shine, tun alokacin da hankulan mutane suka raja’a wajen kallon abinda aka kunna hankalin Alkali ya tashi musamman da yaga an hasko hotonsu, tabbas ya tuna da wannan vedion, domin irinshi ne suka kalla a wayar Naseer kuma anan suka konata, ganin beda wata mafita gashi su Mr. Kallah basa wajen hakan yasa ya fakaici idanuwan mutane ya sulale. 

Sai dai yana fita su Inspector Hamza suka tareshi, domin sun shiryama hakan, gaba d’aya jikinsa ya d’auki rawa a lokacin da suka kamashi, rokonsu ya farayi akan su barshi ya tafi baya son yaji wannan kunyar, har zasu wuce dashi Hamza yace su jira mutane su fito dan yafison kowa yasan an kamashi. Hakan yasa suka tsaya har sai da aka fara fitowa sannan suka taho dashi. 

Tsaye su Alhaji Kamal suke tare da sauran mutanan da yazo dasu. ‘Daya daga cikinsu yace lallai Alhaji Kamal maganar ka gaskiya ce shiyasa kace muzo, wallahi na d’auka ba wata babbar shari’a bace, amma meyasa baka fad’a mana komai ba kafin muzo dan nasan kasan da wannan vedion? 

Murmushi Alhaji Kamal yayi yana fad’in nafiso ku gani da idon ku. Mutumin yace fad’i gaskiya dai Babban Alkali, kawai kace kasan halin zuciya, kada ka nuna mana asamu wani ya sanar dasu Alhaji Barau kafin muzo. 

Alhaji Kamal yace kunga laifi na? Gaba d’aya sukace a’a, ai ana son sirri, kuma hakan da kayi yayi dai-dai, dan haka sai asanar da manyan mu saboda wannan babban abu ne dole sai anyi zama. 

Alhaji Kamal yace tun kafin muzo na sanar da Chief Judge, duk da bansanar dashi komai ba amma na fad’a masa ana zargin babban Alkalin kotun nan tare da wasu manya da aikata babban laifi, kuma na sanar dashi za’a gabatar da shari’ar a yau wanda acikinta ne za’a gano komai, kunsa dai mutum baya yanke ma kanshi hukunci, hakan yasa shima Alkalin ya gudu tun kafin a sauke shi, dan haka nasan zuwa yanzu sun kusa isowa dole muyi zama zuwa anjima dan bana so shari’ar nan ta wuce gobe. 

***

Wallahi Ra’eez kai mugune, ashe dama ka iya dariyar mugunta, yanzu agaban mutane kasa dariya sai ka tona kan ka. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in ayanzu bana tsoron kowa yasan waye ni, domin komai yazo k’arshe, kuma tsakani da Allah bazan iya rike dariyata ba alokacin shiyasa nayi abuna domin Alhaji Barau yayi abun kunya Alkali da guduwa. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button