ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Dariya sukasa gaba d’ayansu. Jabeer yace Allah yaso Raheena da Momynta basa nan da Allah kad’ai yasan halin da zasu tsinci kansu. Murmushi Ra’eez yayi yana fad’in wallahi Jabeer kana son Raheena kawai dai kana b’oyewa ne saboda ni, kuma kasan dai ni ba aurenta zanyi ba.
Tsaki Jabeer yayi yana fad’in wai kai zuciyata kashiga da zaka rik’a fad’ar haka, nifa ba sonta nake ba kawai tausayinta nakeyi. Murmushi Rafeek yayi yana fad’in kai ma Ra’eez da sa ido kake, tun yaushe Jabeer yake fad’a maka ba sonta yake ba kawai tausayinta yakeyi abarshi ahaka.
Jinjina kai Ra’eez yayi yana dariya yace an barshi ahaka Yaya, Allah ya kawo masa mai sonshi. Tsaki Jabeer yayi yana fad’in d’ansa ido kawai.
Ra’eez zeyi magana wata matashiyar yarinya tayi masu sallama. Amsawa sukayi suna kallonta yayin da Jabeer ya juya baya yana waya. Gaishe su tayi tana fad’in dan Allah Yaya Sameer nake nema munyi waya yace yana kotu kuma nashigo wayarsa bata shiga.
Ra’eez yace wane Sameer fa? Tace Yayan Adnan wanda yazo bada sheda. Ra’eez yace oho, K’anwarsu ce ke? Kai ta d’aga tana murmushi. Ra’eez yace kuma bamu sanki ba ya sunan ki? *Husnah!* ta bashi amsa.
Ra’eez yace amma dai ba’a nan kike zaune ba ko? Murmushi tayi tace sati na d’aya dana dawo na kammala karatuna a A.b.u zariya. Ra’eez yace masha Allah, na tayaki murna, bara na kira maki shi yanzu na ganshi kila koya zagaya.
Kafin ya bar wajen saiga Sameer ya fito daga baya da alama band’aki yaje. Murmushi ya saki yana fad’in Husna ashe kin iso? Kai ta d’aga tana fad’in na kira ka bata shiga ba. Sameer yace kila network ne.
Juyowa Jabeer yayi yana maida wayar aljihu yace mu tafi idan ka gama surutun naka. Dariya Ra’eez yayi yana fad’in ai fa yau nashiga ukku, sai fushi kake kamar kaine Alhaji Barau.
Dariya sukasa gaba d’ayansu banda Husnah data shagala wajen kallon Jabeer????. Rafeek yace wallahi Jabeer sai kayi da gaske dan Ra’eez yaga wajen baccin ka.
Harara ya buga ma Ra’eez yana fad’in ka barni dashi Yaya nasan tsiyar da zan masa. Kamoshi Ra’eez yayi yana fad’in haba d’an uwana na kaina, yi hakuri muje, kasan akwai sauran abubuwa agaban mu.
Sameer yace bara na aje Husna gida zanzo. Rafeek yace shikenan nima ofis zan wuce dan dole ayau mu saki wannan labarin, gidan Tv ma nasan zasu haska dan nasan dole akwai wad’an da suka d’auka kasan mutane ba’a iya masu ko yaya ne sai an samu cikin ‘Yan jarida sun d’auka.
Sameer yace shikenan Husna muje. Jin shiru yasa suka juyo suna kallonta, ita ko hankalinta yana wajen Jabeer da yayi gaba zuwa wajen motarsu. Hannu Sameer yasa ya mintsinota da sauri ta juyo tana sosa kai.
Ra’eez yace K’anwarmu ki gaida gida ko. Murmushi tayi tana jinjina kai. Gaba Ra’eez yayi yana fad’in Yaya sai munyi waya. Murmushi Rafeek yayi yana fad’in tunda kana sauri kayi d’aukar magana ba.
Zama cikin motar yayi yana fad’in wai saurin me kake ko sallama dasu Husna bakayi ba bayan kuma kayi kasuwa. Harara ya wurga mashi yana fad’in wallahi Ra’eez kashiga hankalin ka dani, wacece kuma wata Husnah? Kafad’a Ra’eez ya d’age yana fad’in oho, lokacin da ka gama wayar wayace baka tsaida hankalin ka har ka ganta ba.
Murmushi Jabeer yayi yana girgiza kai yace naga alama yau ahaka zaka k’are wajen tsokana, ina su Ummu ko sun wuce? Ra’eez yace suna fitowa Abbah ya tafi dasu kasan kotun ta cika. Jabeer yace ina muka nufa? Ra’eez yace muyi gida dan nasan anjima Kawu Kamal zai nememu dan yace akwai zaman da zasuyi gara muje mu huta.
**** ****
Zaune suke a gidan Alhaji Marusa su ukku suna jiran tsammani, dan tunda sukasan an shiga kotu suka had’u a gidan Alhaji Marusa dan Alhaji M. Sanda ya fad’ama Alhaji Barau da zarar yaga za’a gabatar da shedar data tabbatar suna dasa hannu a kisan Naseer da Alhaji Maiwada yayi kokarin fitowa yazo su gudu tun kafin a kamasu. Sai dai basu san jiran gawar shanu suke ba.
Gyara zama Mr. Kallah yayi yana fad’in nifa hankalina ya kasa kwanciya, tun d’azu nake kiran Brr. Bajinta naji ko an gano wani abu amma wayarsa ma akashe take, da farko tana shiga be d’auka ba, nasan lokacin ko yana cikin kotun, amma yanzu a kashe ma take. (Abinda basu sani ba Brr. Bajinta ma yayi takanshi, dan tunda ya tabbatar da mugayen halinsu ya tsorata, danshi duk tarayyarsu dashi iyaka su sashi yayi shari’ar karya su biyashi amma betab’a sanin su d’in makisa bane, hakan yasa asiri yana tonuwa ya kashe wayarsa dan yace bazai fada masu ba kada su gudu, shiyasa ma ya sanar ma Hamza inda suke.)
Alhaji Marusa yace nima hankalina ya fara tashi, gashi na kira wayar Lucky itama akashe, da alama shima yayi takanshi, ina ganin fa lokaci yayi da kowa zai nemi hanyar tsira, kawai ku tashi mubar garin nan kafin komai ya kwab’e.
Mr. Kallah yace Alhaji Barau fa? Alhaji Marusa yace kai kasanshi, amma wallahi bazan sake mintuna goma awajen nan ba, idan kai zaka tsayashi to ni nayi nan.
Tashi Alhaj M. Sanda yayi yana fad’in jirani Alhaji Marusa. Dole Mr. Kallah ya mik’e jiki a sanyaye yabi bayansu. Suna fitowa suka iske ‘yan sanda suna jiransu, ai gaba d’aya sai hankalinsu ya tashi, nan fa suka fara kokarin tserewa, da sauri aka cafkesu akasa mota yayin da ‘Yan jaridan da Hamza ya taho dasu suke ta d’aukarsu.
Yayi haka ne domin a watsasu ayau saboda kowa yasan halin da ake ciki, haka suka tafi dasu sai zare ido suke a mota.
Ganin haka gaba d’aya ma’aikatan gidan Alhaji Marusa suka fito domin suyi takansu, sai dai kowa sai da ya kwashi rabonshi kafin yayi gaba.
Ur’s.
Nabeelert Lady????
[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣8️⃣
Gaba d’aya gari ya hargitse da labarin abinda ya faru, yayin da ‘yan jarida suke ta kok’arin had’a kan labarin da zasu gabatar.
Da misalin k’arfe hud’u su Alhaji Kamal suka shiga taron gaggawa. Manya sun fusata akan wannan abun kunyar da aka jawo ma kungiyar su, dan wannan abun ba k’aramun tab’a Kadar su zeyi ba domin sun san dole sai duniya taji wannan abu. Haka suka gama tattaunawa yayin da suka tsaida wanda zaiyi shari’ar a gobe.
Haka Alhaji Kamal ya sake kunna masu vedion kowa ya gani, tabbas sunji kunyar wannan abu, babu abinda yafi ciwo irin na Malan Sani, shekaru da yawa an kulleshi ba akan hakkinsa ba. Da haka taron ya tashi.
*** ****
Rafeek agaskiya yanzu kam naji dad’in wannan shari’ar daka tado, koba komai silar shari’ar Naseer ta jawo za’a tona asirin mutane da yawa, kamar yanda mutane suka aminta da wannan kotu suna fad’in irin adalcinta ashe dama a cikin duhu muke, Allah ya k’ara tona asirin munafukai.
Rafeek yace amin Baffa, ai yau jinake kamar nayi kuka saboda farin ciki, hakika Allah yana son bayinsa, kuma shi maji rokone, insha Allahu zuwa gobe kowa zaisan matsayinsa.
Ummansu tace nikam ko ba’ayi komai ba zuciyata ta wanke, koba komai duniya tasan waye ya kashe mani Naseer, kuma sun kunyata sai fatan Allah ya kara tona asirinsu. Rafeek yace amin Umma, bara na wuce dama ina wajen aiki naga kiran ku. Baffa yace Allah ya tsare ka. Yace amin.