ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

**** ****

Ya Allah wannan wace irin bak’ar rana ce haka, yanzu Alhaji ne ‘yan sanda suka kama har wajen aikinsa saboda tozarci, ina zansa kaina yau, da wane ido zan kalli K’awayena da sauran mutane? Zubewa Raheena tayi jikinta tana kuka. 

Dafata Momy tayi tana fad’in wallahi dole kiyi kuka Raheena, mu kam Alhaji ya gama cutar mu, taya zamu iya rayuwa cikin wannan tashin hankalin, ashe dama halin da yake aikatawa kenan ab’oye bamu sani ba? Duk tarin dukiyar nan daya tara mana ta hanyar haram ya tara ta? Kalli wannan uban gida da muke ciki, haba ashe shiyasa Alhaji Marusa ya sayar masa da gidan ashe duk jirgi d’aya ne ya d’ebosu, yanzu gashinan sun kaishi sun baro, meyafi wannan kunya ace kana zaune saman kujera kana shirin yankema wani hukunci sai kuma a nunoka kana cikin masu laifin. 

Tashi Raheena tayi tana fad’in wallahi Momy nayi dana sanin shiga yanar gizo ayau, domin ina hawa nayi bakin gani, a group d’in da nake kawai naga an turo hoton Dady a kotu hada vedion shi lokacin daya sulale a kotun, dan bala’i hatta da shedar da aka kunna akotu wallahi an samu wad’an da suka d’auketa, ina hawa face book ma abinda nagani kenan, duk wata kafa ta yanar gizo idan kika shiga maganar su Dady akeyi. 

Goge ido Momy tayi tana fad’in bamu da bakin magana kam, abinda nakeso da ke kawai ki kashe wayarki, idan da hali ma kawai ki kulle account d’inki sannan ki karya layin ki hakan zai fi maki kwanciyar hankali, idan yaso lambobin da kike so ki barsu akan wayar dan nima haka zanyi wallahi Raheena bazan iya wannan abun kunyar ba, dole mubar garin nan, gara na koma asalina dama nayi gini na a kano ina shirin zuba ‘yan haya wallahi na fasa garin zamu bari. 

Raheena tace ya zamuyi da wannan gidan kuma? Waro ido Momy tayi tana fad’in ke yanzu har maganar wata kadara ta Alhaji kikeyi, to ina tabbatar maki sai kotu ta kwace komai nashi dan sai ya biya diyar mutanan da ya kashe, kayan d’akin ki ma zansa azo goben nan a tafi dasu kano, kije ki fara had’a kaya ki da duk wasu abubuwa masu muhimmanci dan wallahi idan masu bincike sukazo bazasu bari mu d’auki komai ba. 

Kuka Raheena tasa tana fad’in shikenan yanzu kam nasan Ra’eez yafi k’arfina, dan ko rana aka samana sai ya fasa dan yanzu Dady yayi mana bakin fenti. Momy tace ki kwantar da hankalin ki sai kiga kuma yaji tausayinki tunda yasan ba laifinki bane, dole muje kotu domin ayi komai agaban mu, tashi ki kunna mana Tv nasan yanzu zasu nuna komai. 

Aikuwa Raheena tana kunnawa sai ga masu labarin k’arfe takwas na dare. Kowace tasha ka kunna ko gidan radio duk maganar d’aya ce, nuno su Alhaji Marusa ne ya k’ara d’aga masu hankali, shikenan yanzu an had’a kan masu laifi dole a yanke hukunci. 

Daga k’arshen labaran aka tabbatar da gobe talata k’arfe goma na safe za’a zartar da hukunci a babbar kotu. Kashewa Momy tayi tana sakin kuka. Masu aikin gidan ne suka shigo jiki asanyaye suna masu jaje. 

Tashi Momy tayi tana fad’in bazan bari a cuce ku ba, domin nasan gidan nan ya kusa haramta agaremu, dan haka zan sallame ku zuwa gobe kowa ya tafi ina rokon ku daku yafe mana, bara naje d’akin Alhaji dole nayi maku sallama mai tsoka. 

Farin ciki suka kamayi jin abinda Momy tace. Fitowa tayi da wata k’atuwar jaka wadda kud’i ne kawai aciki, haka tasa suka d’auko bakar leda ta bama kowa kud’i masu yawa, kayan Alhaji ta d’auko duk ta raba ma mazan masu aikin, sannan ta d’ebo wasu daga cikin nata dana Raheena ta bama matan, haka sukayi ta godiya kowa ya nufi wajen kwanansa kafin gobe.

 Ciki suka shiga suka fara had’a kaya yayin da tayima wani d’an uwanta waya da yake Lagos akan ya taho da motar d’aukar kaya tunda asubar fari zai kai mata kano kafin a kammala shari’ar sai su tafi. 

**** ***

Hawaye ne kawai yake zubo ma Ammi bayan data gama kallon labarai, mai aikinta da take gefenta sai hakuri take bata. Ammi tace dole nayi kuka Inno, Alhaji ya gama zalunta ta, ya b’ata mani tarbiyar yarona, ya lalata mani mahaifa, gashi daga k’arshe ya sani jin kunyar duniya, na farko an yanke ma Fawwaz hukuncin kisa, na biyu an kama Alhaji shima nasan hukuncin kisa ne domin rayuka ya kashe, shikenan na tashi a babu, wannan gidan dole na barshi koda bazai shiga cikin diyar da zai biya ba wallahi bazan zauna aciki ba domin komai na ciki haram ne, sisinsa bazan d’auka ba, haka zan tafi garin mu gara idan naje Iyayena su siya mani sutura da kud’insu amma babu abinda zan iya cigaba da amfani dashi domin duk haramun ne. 

Inno tace kiyi hakuri Hajiya ai bakisan haramun bane sai yanzu kinga duk abinda kike dashi ya halatta agareki sai idan ya sake baki wani abun ne. 

Murmushin takaici Ammi tayi tana fad’in Inno bakinsa girman haram ba, matuk’ar ka kasance kana cin haram kuma kasan haram ne wallahi Allah bazai barka ba agobe kiyama, tabbas ada bansan bakin halin Alhaji ba, nasan dai ma’aikaci ne kuma albashinsa muke ci, amma zuwa yanzu na fahimci ya cakud’a kud’insa da haram domin harkar shigo da haramtattun kaya sukeyi, ban tab’a sanin haka ba sai jiya da nayi bincike a d’akinsa naga wasu takardu, kinga kuwa idan har nacigaba da amfani da kayanshi nima nashiga layin halaka, dan haka ki barni, idan kina son kayana gasu can kije ki had’a dan sallamarki zanyi, sauran kud’ina na banki ma asusun marayu zan kaisu, idan baki son kayan zan mik’asu gidan marayu sadaka. 

Inno tace tunda sadaka kika bani ai ba haram bane zan d’ebi wasu sai akai sauran gidan marayu bazan had’e duka ba, gaskiya wannan abu beyi dad’i ba, amma ai zakije kotun gobe ko? Ammi tace badan inaso na mik’a mukullin gidan nan a gareshi ba kuma ya furta mani saki da babu abinda zai sa rana ta fito ta sameni a Lagos, amma dole naje nayi sallama da Fawwaz kuma na amshi sakina.

 Inno tace gaskiya zanji babu dad’i, amma Allah yasa haka yafi alkhairi, yama sunan garin ku? Ammi tace Sokoto. Inno tace ikon Allah ashe fa kin tab’a fad’amin wallahi na manta, ai gaskiya garin ku akwai nisa, amma idan da rai wata rana zaki ganni. Ammi tace Allah yasa, kira mani masu gadi su duka. 

*** ****

Umar yanzu ya zamuyi, ni wallahi na manta da wannan maganar, tunda na haye saman kujerar Oga shikenan na manta dashi da abubuwan da mukayi, sai cikin satin nan Alhaji Barau yake fad’a mani an fara bincike akan shari’ar da akayi shekarun baya. 

Miyau Umar ya had’iye yana fad’in Adebayo wannan shi ake kira ga k’oshi ga kwanan yunwa, muna farin ciki shekaru sun ja an manta da komai ashe abu be wuce ba, kana kallon dai yanda aka kama Alkali a kotu, su Alhaji kuwa har gida aka bisu, taya kake tunanin abun bazai zo kan mu ba, koda ba’a kamma mu yanzu ba idan akaje shari’a gobe dole bincike yazo kan mu. 

Adebayo yace wallahi tsoro nakeji, da nasan da wannan abun bazan zo aiki yau ba, gashi aiki ya rik’emu mun kai har dare kada mu fita akama mu, da ace ina da mai a motata daga nan hanyar garin mu zan nemo gara na kwana a ahanya tunda ATM d’ina yana mota bani da matsala, to yanzu idan na tafi an kulle gidan Mai sai na masu jarka kuma ina tsoron na siya da yawa ya bani matsala. 

Umar yace kasan abinda za’ayi? Tunda sai gobe k’arfe goma za’a shiga kotu kuma sai an fara shari’a sannan bincike yazo kanmu kawai yau mu kwana cikin shiri, gobe tunda asuba kowa ya kama gabanshi, lokacin da za’a neme mu nasan munyi nisa, dan haka kawai mu tafi. Adebayo yace haka za’ayi Umar kulle ofis d’in mu tafi. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button