ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Cak suka tsaya ganin ‘yan sanda a gabansu. Tsoro ne ya kamasu gaba d’aya, babu b’ata lokaci suka kamasu suka tafi, motarsu ma sai wasu ‘yan sandan ne suka tukasu. 

*** ***

Kafin gari ya waye sai da su Hamza suka had’a kan duk wasu masu laifi, sai dai kowa da wajenshi babu wanda yasan an kamo wani sai wad’an da aka nuna a tv, hatta dasu Kwamishna da Dr Aliyu Sani duk an kamasu, sai dai shi kwamishna basu kawoshi ofishinsu ba wani waje suka ajeshi saboda girmamawa. 

**** ****

*Tuesday 19/12/2019*

*High court Lagos*

Fad’in cikar da kotun tayi ba abu bane me yuwuwa, domin duk wanda yasan labarin wannan shari’a yasan dole tayi mutane, ko yawan masu d’aukar rahoto ya isa ya cika rabin kotun. 

Gaba d’aya ma’aikatan kotun k’arfe bakwai suka halarci kotu saboda dole akwai tsare-tsare, manyan jami’an tsaro ne a harabar kotun su duka suna d’auke da manyan makamai, duk wanda zai shiga kotun dole sai an bincikeshi da abun duba mutane, hanyar maza daban ta mata da ban, sosai abun ya k’ayatar domin sun shirya ma shari’ar saboda sun san ana iya samun wani tashin hankali musamman da shari’ar ta kasance ta manyan mutane. 

Lokacin da kotun ta cika dole sai hakuri sauran mutanan sukayi domin jami’an tsaro sun tare hanyar shiga sai dai masu son jin kwakwaf suka tsaya a harabar kotun. 

Masu laifi dama da wuri aka kawosu kotun kowa da inda aka ajeshi, kana shiga cikin kotun zaka iske Alkalai ukku zaune asama sai b’angare guda na manyan mutane, yayin da d’ayan b’angaren lauyoyi suke zaune, sai wajen da su Magatakarda suke a zaune, daga wajen zaman mutane kuma duk akwai jami’ai ko wace hanya suna tsaro. 

Tsit kake jin kotun dan kowa yasan yau babu wasa, iya mutanan da suke zaune agaba kad’ai ya isa yasa mutum ya natsu, ga kuma jami’ai suna zagaye da bindigu. 

Bayan da kowa ya natsu aka umarci da ashigo dasu Alhaji Barau. Idanuwa kawai mutane suka zuba dan gangar jikinsu ta kasa motsi bare ta jawo hayaniya gudun kada suma suyi laifi. 

Gaba d’ayansu kawunansu a k’asa suka shigo kotun, Alhaji Barau da aka kamashi yana sanye da kayan aiki zuwa yanzu babu su ajikinshi dan an bashi wata jallabiya yasaka. Haka suka jeru a gefe suna sunnar da kai. 

Tashi Magatakarda yayi domin ya karanto shari’ar…. 

*A yau talata 19/12/2019 wannan kotu mai albarka zata cigaba da sauraron shari’ar da aka fara jiya litinin 18/12/2019, an tsaya a inda Brr. Ra’eez ya gabatar da shedar data tabbatar da wad’an da suka had’a baki wajen kashe Naseer Sambo Jarmai.*

*Sai shari’a ta biyu itace ta Iyalan Malan Sani, inda suke rokon wannan kotu data sake shari’ar da aka gabatar shekaru sha biyu da suka wuce akan mutuwar tsohon shugaban kwastam Alhaji Hamza Maiwada a wannan kotun domin an samu wasu manyan shedu da zasu tabbatar ma kotu ba Malan Sani bane ya aikata laifin da aka yanke masa hukunci akai.*

Risnawa yayi ya mik’ama d’aya daga cikin Alkalan da suke zaune. Bayan da ya gama dubawa ya mik’ama sauran. Na tsakiyar daya kasance shugaba shine ya bama Ra’eez izinin ya cigaba da gabatar da shari’a a inda ya tsaya jiya. 

Tashi Ra’eez yayi yana risnawa, ganin bakin fuska yasa ya fara da gabatar da kanshi. Gyara riga yayi yana fad’in ya Mai shari’a ni sunana *BARRISTER RA’EEZ HAMZA MAIWADA, ‘DAH GA MARIGAYI SHUGABAN KWASTAM NA LAGOS WATO ALHAJI HAMZA MAIWADA.* 

Nine wanda yake kare wad’an da suke k’arar shari’a ta farko data biyu. 

Gaba d’ayansu suka d’ago cikin firgici suna kallon Ra’eez, Alhaji Barau yafi kowa girgiza da abinda kunnuwanshi sukaji, tabbas sai yanzu ya gama gano dawa Ra’eez yake kama. Runtse ido yayi yana jin wani irin tashin hankali. 

Mutane kuwa duk yanda suka natsu jin abinda Ra’eez ya fad’a dole tasa aka fara kus-kus, domin abun ya basu mamaki. 

Raheena da Momy kuwa suman zaune sukayi. Runtse ido Raheena tayi hawaye suna zubo mata, ayanzu kam tasan Ra’eez ya girmema tunanin ta, dama fansa yazo d’auka kenan. Saman cinyar Momy ta kwanta tana kuka. Bubbuga teburin da akayi ne yasa kowa ya shiga hankalinsa. 

Gyara tsayuwa Ra’eez yayi yana fad’in, kamar yanda aka gabatar da shedar vedion da aka shirya yanda za’a kashe Naseer a jiya nasan wannan shedar ta tabbatar da wad’an da suka shirya kashe Naseer domin fuskokinsu sun fito yayin da akaji muryoyinsu suna ambatar sunan juna. 

Ina so kotu ta bani dama domin na yima mutanan da suke gabanta tambayoyi…. Kotu ta baka dama. 

Matsowa yayi kusa da masu laifin yana sakin murmushi. 

Alhaji M. Sanda zan fara ta kan ka, duk da fuskar ka bata bayyana a cikin vedion ba amma muryarka ta sheda kai ne, sannan mutane biyu sun tabbatar da cewar kai ne ka bada umarnin aka kashe Naseer, domin duk sauran goya maka baya kawai sukayi, kotu zataso taji daga bakin ka yanda komai ya kasance. 

Alhaji M. Sanda… Kanshi a k’asa yace maganar gaskiya duk abinda akaji a ciki haka yake, sai dai kuma mun fad’a ne kawai amma ba mune muka aikata ba, domin mun aje akan zamusa ayi sai kuma aka samu wani ya rigamu aikatawa, dan haka ni bansa a kashe kowa ba. 

Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in Alhaji Barau me zaka iya cewa agame da wannan vedion? 

Alhaji Barau… Haka maganar take, kamar yanda Alhaji M. Sanda ya fad’a tabbas mun shirya yanda za’a kashe Naseer saboda a b’oye abinda Fawwaz ya aikata sai kuma wani ya riga mu. 

Murmushi Ra’eez yayi kafin ya matsa gaba ya tambayi Alhaji Marusa da Mr. Kallah, sai dai duk amsar d’ayace. Murmushi yayi dama yasan za’ayi haka shi kuma yafiso su k’aryata kafin ya tabbatar masu. 

Juyowa yayi yana fad’in ya mai shari’a inaso kotu ta bani dama domin na kira mutumin da akayi hayarshi ya gabatar da wannan kisa…. Kotu ta baka dama. 

Kallon k’ofa kawai suke yayin da zufa ta fara keto masu, ji suke kamar su nutse, duk da basu san wanda zai shigo ba amma sun tsorata da murmushin kan fuskar Ra’eez. 

Ur’s. 

Nabeelert Lady????

[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud’i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k’asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub’e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*

4⃣9⃣

Hannu Mr. Kallah ya d’ora akai ganin anshigo da Lucky, bayansa kuma Dr. Aliyu Sani ne sai Kwamishna Bello kabir wanda duk kunya ta hanashi kallon kowa. Mamaki ne ya cika mutane ganin Kwamishnan ‘yan sanda a jerin masu laifi, sai wad’an da suka san Dr. Aliyu suma sunyi mamakin ganinshi. 

Lucky ne ya fara fitowa zuwa wajen da ake tsayawa. Matsowa Ra’eez yayi yana fad’in kotu zata so taji sunanka da kuma san’ar ka. 

Sunana Adekulle Isnewa, amma anfi kirana da Lucky, sana’ata itace sata sai kuma ana d’aukata nayi aiki a biyani. 

Ra’eez… Kamar wane irin aiki kenan? 

Lucky… Kamar idan wani yana son ajama wani kunne ko kuma a shekeshi to ina irin wannan aikin a biya ni. 

Ra’eez… Shin Lucky ko kasan wad’an nan mutanan? 

Lucky… Kallonsu yayi yana sakin murmushi, juyowa yayi yana fad’in sosai kuwa, domin tunda nake harka da mutane ban tab’a harkar da nake jin dad’inta ba kamar harka dasu, zan iya cewa sune Ubayen gidana domin mun dad’e atare musamman Alhaji Marusa dan shine ya nuna masu ni. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button