ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Ra’eez… Ko zaka iya fad’ama kotu irin aiyukan da suka saka kayi masu.
Lucky… Gaskiya sun sani aiyuka da yawa, wasu zan iya tunawa wasu kuma bazan iya tunawa ba, dansu basa jin tsoron a kashe kowa matuk’ar zasu samu biyan buk’ata, hatta da junansu ma basu bari ba, domin ko kwanakin baya Alhaji Barau da Mr. Kallah sun sani nayi masu wani aiki akan Alhaji Marusa, duk da shi na sani amma silar kashe mun aboki da yayi yasa na amshi aikinsu.
Ba wani aiki bane sun sakani na kwace kayanshi da yayi odar su masu matuk’ar tsada, sannan na kashe matuk’an motar, ni kuma aikin da nayi mashi na cinna ma babban ma’ajiyarsa wuta kuma duk sun san da haka, wanda silar haka har ya kamu da ciwo.
Dalilin da yasa na fara baka wannan labarin saboda kasan cewar suma zaluntar junansu sukeyi, sai kuma kashe yarana da aka kama wancan satin da nayi a ofishin ‘yan sanda kuma na fad’a masu duk sun san da haka.
Wani irin kallon Mamaki Alhaji Marusa yake bin Alhaji Barau da Mr. Kallah dashi, gaba d’aya takaicinsu ya rufeshi, jiyayi beda sauran wata dabara garama ya amsa laifinsa kowa ya rasa.
Ra’eez… To Lucky kotu tana sauraron ka.
Lucky… Acikin aikin da suka saka ni wanda bazan manta ba shine kashe tsohon shugaban Kwastam, sai kuma Naseer wanda ake magana amma shi ba nine na kashe shi ba abokina Peter ne ya kashe shi domin aranar aiki biyu mukayi, mune mukaje har gidan Alhaji Maiwada muka bugi matarsa yayin da muka shak’ama direbansa abun kauda hankali sannan muka saka hannun Matar Alhaji ta yakushi wuyanshi, bayan daya koma gidansa nine na kaima Inspector Bello wato Kwamishnan ‘yansan na yanzu jakar da aka samu a gidan Malan Sani had’e da allurar da mukayi ma Alhaji, shine ya sakata a d’akin Malan Sani, sannan Dr. Aliyu shine aka had’a baki dashi wajen tabbatar da Malan Sani akan zargin da ake masa.
Ra’eez… Hannu yasa a aljihu ya ciro kyalle ya goge kwallar data zubo masa, gyara glass d’inshi yayi yana fad’in bayan wannan sai wane aiki kayi masu?
Lucky…. Labarin yanda suka saka kayan Alhaji Marusa a gidan Alhaji Maiwada ya basu wanda akayi shari’a har kotu tasa ya biya Alhaji Marusa makudan kud’i wanda silar haka ya siyar da gidanshi, duk abubuwan dasu Alhaji Marusa suka k’ulla sai da Lucky ya fad’a.
Gaba d’aya kotun tayi shiru ana sauraronshi har ya kammala bada labarin.
Jinjina kai Ra’eez yayi yana fad’in zaka iya tafiya. Inaso kotu ta bani dama domin nayima Kwamishna da Dr. Aliyu tambaya… Kotu ta baka dama.
Dr. Aliyu kaji bayanin da Lucky yayi, shin ko kana da ja akan abinda ya fad’a? Duk’ar da kai Dr yayi dan beda ta cewa, a hankali ya d’ago kai yana fad’in wallahi tsautsayi ne yasa na amshi tayinsu ba halina bane.
Kallon Kwamishna Ra’eez yayi yana fad’in ‘Yallab’ai akwai abinda Lucky ya fad’a wanda ba haka yake ba? Sunkuyar da kai yayi yana goge zufar data zubo masa.
Hannu Ra’eez ya tafa yana fad’in ya mai shari’a inaso kotu ta bani dama domin na gabatar da wasu shedu… Kotu ta baka dama.
Flash d’in da suka samu a d’akin Abbu yasa Jabeer ya kunna…. Anan kowa yaga yanda su Alhaji Marusa suka shirya duk wani tuggu akan Alhaji Maiwada, da yanda ake shigo da haramtattun kaya da yanda su Adebayo da Umar suke kulla nasu sharrin har zuwa lokacin da aka cire abinda Malan Hassan yasa a gidan Alhaji Marusa.
Kashewa yayi yana fad’in inaso abani dama domin nayima d’aya daga cikin mutanan da sukayi wannan aikin…. Kotu ta baka dama.
Cike da mamaki suke kallon Abubukar wanda ya zama babban mutum, haka ya tako har gaban kotu.
Ra’eez… Kotu zataso taji sunanka da kuma alak’ar ka da shugaban Kwastam.
Sunana Abubakar Sani, kuma ina d’aya daga cikin ma’aikatan da sukayi aiki tare da Marigayi Alhaji Maiwada, hakika shi mutum ne mai son rike gaskiya da amana, be yarda da cin hanci ko zalunci ba, zuwansa garin nan mun samu cigaba, sai dai wannan gaskiyar tashi itace ta jawo ajalinsa, domin duk abinda aka gani ayanzu haka yake, wasuma ba’a d’aukesu ba, amma tabbas Alhaji Marusa shine yasa aka kashe Malan Hassan tsohon maigadinsa kuma yasa aka rufeshi ba tare da iyalinsa sun sani ba, haka yasa aka wahalar damu nida abokin aikina shima ya mutu Moses saboda muna bayan gaskiya, sannan Mr. Kallah yayi mana canjin wajen aiki kuma suka tsorata mu da kada mu sake dawowa garin nan.
Tunda na bar garin nan ban sake dawowa ba, sai dai mutuwar Malan Hassan ta tsaya mani arai, domin mune silar jefashi cikin halin daya shiga, hakan yasa na kasa daurewa domin anbar Iyalinsa cikin tashin hankali saboda basu san halin da yake ciki ba, haka na dawo garin nan na fad’a masu abinda ya faru.
Sanin bazasu iya komai ba yasa suka sai da d’an gidan da suke ciki suka tattara suka koma garinsu. Tun daga lokacin bansake zuwa garin nan ba, bayan wani lokaci naji aikin kwastam ya faitar mun shine na ajeshi.
Ra’eez… Jinjina kai yayi yana fad’in mungode Alhaji zaka iya tafiya. Inaso kotu ta bani dama domin na gabatar da Matar Alhaji Maiwada… Kotu ta baka dama.
Fitowa Ummu tayi tana share hawayen da suke fuskarta, tabbas yau mutuwar Abbu ta dawo mata sabuwa. Da kallo su Alhaji Barau suka bita kowa jikinsa yana k’ara sanyi.
Ra’eez… Kotu zata so taji sunanki da kuma abinda kika sani akan sharrin da akayima Malan Sani.
Sunana Bilkisu kuma nice matar Alhaji Maiwada, tabbas abinda akace Malan Sani ya aikata k’arya ne, domin aranar yashigo yana kuka, bayan na tambayesa abinda ya faru shine kafin ya fad’a mutanan suka shigo, nice nayi yunkurin bugama wani flask sai shi kuma ya kwad’a mani sanda anan na zube, amma tabbas Malan Sani be aikata abinda aka fad’a ba.
Girgiza kai Ra’eez yayi, duk yanda yaso b’oye hawayenshi sai da suka zubo, gogewa yayi yana fad’in zaki iya tafiya.
Cikin d’aga murya Alhaji Marusa yace ya mai shari’a duk abinda aka gabatar agaban kotu gaskiya ne, gaba d’ayan mu muna dasa hannu a duka laifukan. Shiru yayi yana harararsu Alhaji Barau, dan gara ya fad’i gaskiya kowama akamashi.
Ra’eez kuwa shiru yayi har sai da zuciyarsa tayi dai-dai kafin ya kalli Alkali yana fad’in ya mai shari’a anan na kawo k’arshen duk wata sheda da zata tabbatar da wad’an da suke da hannu akan mutuwar Naseer da Alhaji Maiwada, ina rokon wannan kotu data hukunta masu laifi sannan ta bima Malan Sani hakkinsa na d’aureshi da akayi shekara da shekaru bisa zalunci wanda Alhaji Muhammad Sanda tsohon Alkalin kotun nan ne ya yanke wannan hukunci kuma akan sani ya yanke domin dashi ne aka aiwatar da komai, sannan ta hukunta Kwamishna domin ya bada gudummuwa wajen jama Malan Sani sharri akan saka masa jaka a d’akinsa da yayi, haka zalika ta hukunta Dr. Aliyu domin ya bada sakamakon k’arya wanda biyanshi akayi domin yayi hakan, sai Shugaban Kwastam na yanzu Adebayo da mataimakinsa, suma suna cikin wannan b’arna da akayi. Ina fata wannan kotu mai albarka zata bima Mahaifina hakkinsa bisa kisan zaluncin da akayi masa, kuma… Kasa k’arasawa yayi saboda kukan da yaci k’arfinsa.
Tashi Jabeer yayi ya kamoshi suka zauna dan shima hawaye yakeyi. Gaba d’aya kotun tayi shiru mutane da yawa sai da suka zubarma da Ra’eez hawaye saboda tausayi.