ALKALI NE Page 81 to 90 (The End)

Bayan mintuna Alkalai suka gama duba shedun da aka gabatar, babban cikinsu ne yayi gyaran murya yana fad’in abisa manyan shedun da aka gabatar ma wannan kotu, kotu tayi dogon nazari wanda ta tabbatar da ingancin wad’an nan shedu, dan haka kotu zata yanke hukunci.
Da farko ina mai bakin cikin faruwar wannan al’amari, domin an samu manyan mutane wad’an da mutane suka yarda dasu, suka basu amana da hannu dumumu wajen aikata miyagun laifuka. *Tsohon shugaban Kwastam na k’asa, tsohon Alkalin babbar kotu ta lagos, Alkalin babbar kotu na yanzu, Kwamishnan ‘yan sanda na Lagos, babban likita, shugaban Kwastam na yansu alagos da mataimakinsa.*
Wad’an nan mutane dana lissafo gaba d’ayansu manyan mutane ne wad’an da suke kula da dubban mutane a k’asan su, sai dai sunci amanar k’asa, sunci amanar aikinsu, sun had’a kai wajen dakusar da gaskiya, da kunya ace mutumin da yake kwatoma wasu hakkinsu yau shine aka kama da wad’an nan miyagun aiyukan, shigo da miyagun kaya, kisan kai, gaskiya ina mai tsananin jin kunyar wannan al’amari daya faru a k’asata, amma shari’a bazata barsu ba, domin duk matsayin ka bakafi k’arfin hukunci ba, dan haka kotu zata fara zartar da hukunci daga k’asa.
*Adekulle Lucky*… Bisa shedun da suka tabbatar cewar shine yake wannan kisa, da kuma amincewarsa akan laifukansa, bisa kundin tsarin mulki na k’asa k’ark’ashin Penal code shashin kisa, wannan kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai ya mutu.
*Dr. Aliyu Sani*… Abisa hujjar da kotu ta samu da kuma amincewarsa bisa laifin bada shedar k’arya, wannan kotu ta soke lasisin aikinsa, sannan ta yanke masa hukuncin d’aurin wata biyar agidan yari tare da tarar naira million d’aya ga Malan Sani.
*Kwamishna Bello Kabir,* bisa kamashi da hannu dumudumu wajen taimakawa masu laifi, da kuma aikata laifi wajen sakama Malan Sani jaka a gidanshi, wannan kotu ta soke lasisin aikinsa, sannan ta yanke masa hukuncin d’aurin shekara biyu a gidan yari, sannan zai biya Malan Sani tarar naira million d’aya da rabi.
*Shugaban Kwastam Adebayo da Mataimakinsa Umar,* bisa kamasu da akayi wajen k’arba’r cin hanci, taimakama masu aikata laifi, da zaluncin da sukayi ma Alhaji Maiwada wannan kotu ta kwace lasisin aikinsu, sannan ta yanke masu hukuncin d’aurin shekara asirin agidan yari, sannan zasu bada tarar naira million ukku ga iyalan Alhaji Maiwada.
Sai hukunci na k’arshe akan mutuwar Naseer Sambo Jarmai da Alhaji Hamza Maiwada.
Mutane hud’u ne suka had’u wajen bada gudummuwa akan wannan kisa, dan haka kotu zata yanke masu hukunci.
*Alhaji Barau, Alhaji Muhammad Sanda, Alhaji Marusa da Mr. Kallah,* bisa kwararan shedu da aka gabatar ma wannan kotu, da kuma amincewar masu laifi akan laifinsu, kotu ta tabbatar da laifinsu, hakika sunci amanar aikin su, dan haka kotu ta yanke masu hukuncin d’aurin rai da rai agidan yari tare da horo mai tsanani, Alhaji Marusa zai biya diyar kashe Malan Hassan da yayi ga Iyalansa, sannan su duka zasu biya diyar Naseer da Alhaji Maiwada tare da tara mai yawa ga Malan Sani, domin sun zalunceshi.
Da wannan ne kotu ta kawo k’arshen wannan shari’a, kuma ta wanke Malan Sani daga zargin da ake masa, haka kuma tana buk’atar masu kula da hakkin d’an Adam da su tsaya wajen tabbatar da biyan duk wata tara da aka d’ora akan masu laifi, had’e da sauran jami’an tsaro, sannan za’a sake d’ora sabon Alkali zuwa wani lokaci. Kottt!!!.
Hayaniya ce ta kaure a kotun. ‘Yan sanda ne sukayi kok’arin fitar dasu Alhaji Barau dan mutane sai jawosu sukeyi, da kyar aka fitar dasu. Malan Sani kuwa zubewa k’asa yayi yana sujada hawaye suna bin kuncinsa.
Alhaji Mansur ne yaje ya kamoshi, rungumeshi yayi yana kuka. Ra’eez ma sai da yayi sujadar godiya ga Allah, kuka kawai yakeyi domin yau itace ranar farin ciki agareshi domin ya cika burinsa. Rungumeshi Jabeer yayi suna murna, haka suka fito waje.
Suna fita suka tsaya suna kallon fad’a atsakanin su Alhaji Barau. Alhaji Marusa ne ya cakumo wuyan Alhaji Barau yana fad’in tsakani na daku Allah ya isa, shegu ashe dama kune kuka jefani cikin tashin hankali, duk amanar dana baku sai da kuka cuce ni.
Dokeshi Alhaji Barau yayi yana fad’in dalla can azzalumi kawai, waye ya cuce mu idan ba kai ba, mu dukan mu nan kaine silar shigarmu wannan halin ba dan kai ba babu abinda zaisa na aikata wannan abun kunyar, waye ya koya mana kisa.
Haka sukayi ta mayar da kalamai yayin da suka fara fad’a suna tona asirin juna, ‘Yan sjarida kuwa sai d’aukarsu sukeyi. Da kyar ‘yan sanda suka rabasu.
Takowa Ra’eez yayi har gaban Alhaji Barau yana murmushi. Ido kawai Alhaji barau ya tsura mashi yana sauke numfashi. Raheena da Momy suna gefe sai kuka sukeyi.
Kallonshi Ra’eez yayi yana fad’in ina taya ka murnar samun sabon waje na rayuwa, ina fatan yanzu ka gane komai akaina? Murmushi yayi yana fad’in yau kam zanyi bacci mai dad’i domin karatun da nayi yau ya k’are domin ya biya buk’ata, dama nayi shine saboda ku, tunda naga k’arshen azzalumai Alhamdulillah, Allah shine abun godiya.
Takawa yayi har gaban Raheena, ido kawai ya tsura mata yana kallon yanda take kuka ajikin Momy. Kauda kai yayi dan tausayinta ne ya kamashi. Matsowa su Jabeer dasu Nabeel sukayi wajen.
Momy ce cikin muryar kuka tace Ra’eez bani da bakin magana, ayanzu kam mun fahimci komai, sai dai laifin wani baya shafar wani, ina rokon ka da girman Allah ka yafe mana domin bamu da sa hannu a cikin mutuwar Mahaifinka.
Ra’eez yace bakuyi mani komai ba, dama kuma ban tab’a furta kalmar so ga Raheena ba, hannu yasa ya jawo Rumaisa yana fad’in wannan itace matar da zan aura d’iya ga Malan Sani wanda Mahaifin Raheena yayi sanadiyar zamanshi agidan Yari shekara goma sha biyu, ina fatan bazaku kullace ni ba.
Momy ta kalli Alhaji Barau cikin kuka take fad’in ka gani ko, tun kafin aje ko ina abinda bakin halin ka ya jawo mana, shikenan kaji dad’i zaka tafi ka barmu cikin tsangwama da tsana, domin babu wanda zaiso had’a zuri’a damu, ka cucemu, dan haka garin zamu bari ka bani takardar sakina domin kai yanzu gawa ne.
Hawayen bakin ciki ne suka zubo ma Alhaji Barau, sunkuyar da kai yayi yana jin tsananin nadama atare dashi, zeyi magana sukaga Nabeel yayi gefen su Momy da gudu, yana zuwa Raheena ta fad’a jikinsa a sume, dan tun zuwanshi wajen ya sauke ido akanta ya kasa d’aukewa, duk bidirin da akeyi besani ba dan hankalinsa yana kanta, hakan yasa da yaga alamun zata fad’i yayi wajenta.
Kanta sukayi gaba d’aya, cak Nabeel ya d’auketa Jabeer na gaba sukayi hanyar ofis d’insu da ita.
Ammi ce tasha gaban Alhaji M. Sanda idanuwanta jawur alamun taci kuka, hannu ta mik’a masa tana bashi mukullin gidanshi had’e da biro da takarda.
Kuka yasa yana girgiza mata kai. Daurewa tayi tana fad’in wallahi bazan tab’a yafe maka ba, ka rubuta mani saki na a hanya nake, Fawwaz kuwa ba laifinsa bane, naje wajensa tunda safe kuma naji dad’in yanda na ganshi, domin alamu sun nuna yayi watsi da shawararka, kai da kake kok’arin sama masa gata kaima zakaje ka iskeshi acan, kuma har na mutu zan cigaba dayi masa addu’a, dan haka ina jiran ka.