AMANA TA CE 1-END

AMANA TA CE Page 1 to 10

Ammar na ganin haka ya dauki Auta yasa gudu sai da yayi nisa ga ruwa ya soma tsagaitawa, ya samu wani rumfa ya ajiyeta ya huta, basu dade sosaiba ya auta sai hawaye:'(:'(take tayi ko da ya laluba kafarta yaji ta kubura suntum, taba kafar dayayi har sai da tayi ihu haka ya dauketa suka cigaba da tafiya.

Su gumus ansha wuya da kyar aka ciro shi don har yasoma shan ruwa, yana dawo wa hayyacinsa yake tambayar mugum ina suke yace sungudu, mtssss bahaka nasoba nan yace naga abunda ya faru kar ka sheke zuwa lahira da wuri shiyasa na cirokakai kajimin wayan nan sai kace mutuwar nima izini takeyi, mikewa sukayi gumus ya karbi wayar mugum don nasa ruwa ya bata, baba sani ya kira ya tambayesu suna ina yace yanzu zasu bar gidan Alhaji kenan sukace gasu zuwa.

 ko da suka isa nan suka samu baba isiya da sani sun daure sale mai gadi da musa, don daman sunyi akan zasu daure su sabida ace barayi ne suka zo, hakan sukayi, ko da su gumus suka iso nan sukaga abunda ke faruwa dariya sukayi sosai sukace Alhaji baku da dama, 

Baba sani yace ya ina fatan kun sheke su cikin sauri gumus yace ai har gawan ma sai da muka yardasu inda ba mai gani, nan kawu isiya yace aikin ku na kyau, gumus yayi murmushi yace oga sai kudin fa baba sani yace ina zuwa cikin gidan suka shiga dakin dad suka duba drawer nan suka ci karo da damin kudi sai dasukayi dariya sosai kafin suka diba nan suka fito falo, baba sani yazo cikin izgilaci yace su Al-hassan yau an sheka kiyama to ina naira kai dan taurin kai yau zamu facaka da dukiyar da kake ta kama dashi, yana zuwa kan hajiya sai da ya shureta da kafa, ke kuma yar iyeye yau munyi maganinki da yar da kuke so, harda dauko bare wanda bakusan daga ina yake ba ku fifita shi akan mu gashi yau duka bakwa nan mun kuma samu dukiyar cikin ruwan sanyi sai ya kece da dariya sosai, nan suka fita suka shiga mota suka tafi don suke su sallami su gumus.

           ®WHW®

  

Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

   

                  ®WWA®

                                

Ko da sukaje gidan kawu isiya wanda tutun nufawa, ba kowa aciki kuma ba nisa sosai da gidan Alhaji marigayi, nan suka shiga ko da suka zauna nan baba sani yace yau burin mu yacika na gama wa da Al-hasan da iyalansa, kamar yanda mukayi Alkawari zamu ba ku 400k kowa zai dau 200k kenan gumus ne yace oga mungo amma munaso aba mota koda kwaya daya ne ehhh musamu na yawo a gari, ko wani aiki kuke so zamu muku cikin sauki kawu isiya yace aaa bazai yuba abun yaso ya dawo musu rikici baba sani yace ba matsala za a duba in komai ya lafa abaku, nan ya ciro 300k ya basu yace kurike wan nan kafin komai in ya lafa zamu sallame ku, gaba daya nan sukayi sallama kowa ya kama gabansa.

 

Da safe yan unguwa suka fito don wasu sunji karar tsayuwardon haka suka yi cirko2 gashi jiya anyi ruwa sosa, mukwabcin dad wani mai suna Alhaji Abubakar yace yan uwa yau ban ga Al-hassan a masallaci ba kuma duk rintsi in ba jinya yayi tsanani yana zuwa sallah amma yau shiru, ko lfy wani mai suna Alhj kabir yace ni jiya fa kamar an shigo unguwan nan don duk da karan ruwan sama dake zuba naji ihu san nan naji harbin bindigasun dade suna jimami kafin wani acikinsu yace kamata yayi mu shiga gidan mugani, nan suka dun guma suka shiga tun a kofa sukaga masu gadi an daure su, da sauri suka isa wajansu, bakinsu an toshe da tsumma, kunce su sukayi nan Alhaji Abubakar ya fara tambayan lfy, sun wahala yasa ba wani amsa don dauri da aka musu mai kyau ne hakan shi ya gala baitar dasu, da sauri suka nufi cikin gidan bayan sunshiga a falo suka tarar da gawan Alhaji da hajiya nan suka soma jimami masu kuka suka fara, alhaji abubakar makocin dad policene nan take ya kira ja mi’an tsaro suka fara binjike nan sukaje dakin Auta inda suka ga yanda aka baza kaya da alamar kare kansu da sukayi da kuma fasa window da akayi gashi ba auta ko da suka zaga nan sukaga jini da kuma alaman harbin da akayi ta waje, Alhj Abubakar yace cikin daya biyu ko sun kashe Zainab ko sun dauketa ko da suka dawo gd sai alokacin ya tuna da ammar nan ya nufi dakin da ke tsammanin nasa ne sallaya tagani a shin fide da alamar anyi sallah akai ki da suka fito suka nufi kofar baya nan sukaga an tura kofar anshiga duk binciken da sukayi ba wani amsa nan suka kira Alhaji sani da baba isiya suka sai da musu, ko da suka iso gidan kuka sukeyi sosai kai ka rantse basu da hannu aciki har sani na ikirarin imyasan wanda yayi kisan nan sai ya dau fansa, kawu isiya kam ko mace iyakaci yanda yake kuka. haka police suka tafi da gawarwakin don kara bincike.

Ammar da auta kuwa tafiya yayi sosai, sun shigo cikin gari kuma dare yayi sosai don asuba ya kusa, nan yasamu inda ba ayi ruwaba ya kwantar da Auta ya yagi zanin dake daure a saman kayan baccinta ya kulle hannusa sai runtse ido yakeyi alamar zafi, ya daure hannuta ya dauketa suka cigaba da tafiya sunyi nisa sosai, sai ga wani mai mota yazo wucewa nan ya tsare shi sam yaki tsaya haka ya cigaba da tafiya sai ga wani da alamar wan nan irin yan taxi masu zuwa gari zuwa gari har yaki tsayawa komai ya tuna ya dawo daukarsu, nan Ammar nace ina zan kaiku Ammar yace ban sani ba mutumin yace to ni saminaka zanje yanzu, yace muje ka ajiye mu a hanya.Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

   

                  ®WWA®

                                

Motar suka shiga nan mutum min yace subada 1500 kudin mota sai a lokacin ya tuna basu da kokisi, innalinahi wa inna ilaihi raji’un abunda ya furta gashi sunyi nisa sosai, sun shiga jeji don sun bar cikin garin kaduna sosai, jiki ba kwari yace wa driver dan Allah ka tai make mu wlh fitowar gaggawa ne ya kama mu bakosisi ajikin mu, driver ya narko ashar yayi, aefa baka isaba zan dauko ku a bati ne ba ko sisi mai na tsada kuma niman kudi na fito, waya sani ko dan iska ne ma kai kasato musu yarinya inazaka da wannan yar gashi jikinta duk jini, kalala ta mata rayuwa, ko sayarta zakayi, nan take ran Ammar ya baci don tunda yake ba abundaya tsana kaman zargi ko kazafi, shi da ya tsani zina a rayuwansa mezaisa ya aikata cikin bacin rai yace kaii Malam ya isheka in har bazaka taimaka min ba karka min wan nan zaton, nan mutumin yace anyimaka kuma zata fita anan ba wlh sai kabani kudina, nan ran Ammar yakara baci wai shi dayake nima da guminsa ga kuma Zainab yar gata gabada baya wai yau sune a wulakance ga shi an kashe su Alhaji shikenan Zee sa ta dawo “MARAINIYA”nan take yaji hawaye:'(:'(:'( wasu na bin wasu, sai a lokacin ya kalli agogon hannusa mai kyau yace ma

driver bani da kudi amma ga agogona in zaka karba yafi karfin kudinka, driver yace nagani ko da ya karba yagani yasan zaiyi tsada dayawa nan yace to shikenan yanzu in kaiku saminaka ne ko zaku sauka anan tsabage bacin rai yace barin musauka anan, ya dauki Auta suka fita, gefen hanya ya kwantar da ita lokacin gari ya waye sosai, sai alokacin yaga kafarta ya kumbura sosai fa bakinta ma ya kumbura sosai, gashi yayi ja abunka da farar mace, gindin wata katuwar bishiya yaje ya shinfida fallen zani ya kwantar ta, ga yunwa yasoma damunsa ga hannusa yana masa zafi sosai, bayan ya kantarta, yasoma dube2 ko zaiga ruwa don yasha yakuma ji alwala.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button