AMANA TA CE 1-END

AMANA TA CE Page 1 to 10

Acikin garin kaduna kuma Alhaji Abubakar ko ince Inspector Abukar shiyatsa akan gawan su dad har akayi zana idarsu aka kaisu makwancinsu na gsky, kafin kace me lbr ya baza gari, yan uwan dad sun taru a gidan ko da Sadiya yar Baba sani taji lbr ba karamin girgita yayi ba baran da taji ance ba a ga Zee ba tashiga tashin hankali don suna shishiri sosai,

Inspector Abubakar daya koma gd ya tausaya ma yarsa bulkisu don kawar Autace sosai tayi kuka kuma nan ta dauki aniyar saita dau fansa akan duk wanda ya aikata abun, bayan kwana uku da rasuwan su Dad yan uwansa sukace su duk wanda yayi abun nam sun barshi da Allah, sirutu kala2 su ka rinkayi har saida Inspector Abubakar yaso ya ganesu, bilkisu kuwa ranan kwana na uku, tasami Abbanta akan ita ta canza ra’ayi daga kan Science courses, yanzu Law zata karanta don tazama barrister don ta nimo ma Kawarta Ameeniyar ta, hakkunta da cutar da ita da akayi, kuma tace Abba ni ajikina inajin Zee bata mutu ba ko ga yanayin statement din da aka samu kuma kaga ba aga Ammar ba nisan yana tare da ita kuma bazai cutarta ba da yardan Allah don yana da hali mai kyau, Inspector Abubakar yaji dadin maganar yarsa Bilisu wanda ake kita da futuhatul-khai, yamata Adu’an Alkairi da fatan nasara.

Su baba sani nan suka fara kiciniyan raba dukiyar dad har yaso su samu sabani da baba isiya akan wanda zai zauna a gidan dad da kyar Baba isiya ya hakura akan shi za a bashi motar dad babban ya rike.

Rayuwa kenan wai naka najikinka shiyake son ganin bayanka basa tunanin suma zasu mutu ba tsoron Allah wan nan wani irin zamani ne burin wasu mutanen su ci “Amana” yan uwa muji tsoron Allah musani Amana tana gefen siradi da Zumunci duk wanda ya karya daya aciki to yasan makomarsa, don ranan kiyama akwai wasu kugiyoyi a kasan gadan siradi duk wanda yaci amana ko ya bata zumunci ko da ya kusa karshen haye gadanne haka kugiyar zata finciko shi wasu kafin su isa duk sun yaga naman jikinsu, ‘Yasalam’ yan uwa muji tsoron Allah mu gyara rayuwar mu musan man zumunci da Amana mu kiyayesu, ya Allah kasa mudace da karshe mai kyau Ya Allah ka daura mu akan hanya madaidaiciya Ameen.

 Ammar sai da yayi tafiya mai nisa kafin ya ga wani rafi nan ya rasa ya zaiyi ya debi ruwa ya kaima Auta tasha ko zata ji dama2 ga tausayinta shikam kasa sha ma yayi in har Auta bata sha ba ba zai iya sha ba, ya sanya hannumsa biyu ya debi ruruwan yanufi gunta tun kan ya isa ruwan ya zube nan yaji wasu hawaye:'(:'( sun zomasa. Yana zuwa kusa da ita ya ga sai wani irin nishin azaba takeyi kamar wai shirin mutuwa Ammar baisan lolacin da yasaki kuka kamar karamin yaro yana cewa Zainab dan Allah kar ki tafi ki barni ke kadai kika ragemin bani da uwa ba uba, gashi sun kashe mana Dad da Hajiya in kintafi ina zansa kaina kuka yakeyi sosai da sosai.

Nima Rash bansan lokacin da nasaki kukan tausayi ba. Allah sarki rayuwa juyi2 Allah ka kawo masu Auta da Amar mafita Ameen.

                  ®WHW®

    

Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

   

                  ®WWA®

                             

Nan yasaki kukamai ban tausayi, jijigata ringayi sai yaga tasaki ba ko alamar motsi atare da ita, da sauri ya dauketa yayi gun rafin da ita yana isowa yaga wani dan tsoho yazo diban ruwa a gora, tsohon nan, ganin halin da Ammar ke ciki yasa yace subhanallah bawan Allah mai yasa meta Ammar kasa magana yayi sai hawaye:'(:'(wani na bin wani, tsohon na ganin halin da Ammar ke ciki ya dibi ruwan goransa tare da bisimillah ya watsamata sau 2 nan take ta saki ajiyar zuciyamai karfi, muryan ta ya dishe, ga jikint ba kwari duk ya mutu, ahankali take magana sai da Ammar ya sunkuyo dai2 bakinta kafin yaji mai takecewa wayyo kafarta, ammar da sauri ya riki kafar sai a lokacin tsohon ya lura da kafan yace yasalam mugani ya rike kafar wan nan ae cizo kunamane ya daneta, yace yanzu ku biyo ni in taimaka mata, ammar ya dauketa suka bi tsohon.

A cikin garin kaduna kuwa, su baba sani sun shiga sabon rayuwa mai dadi da dukiyar da suka dade suna mafarkin samunsa, Sadiya sam nataji dadin yanda Abbanta ke zakewa akan dukiyar dan uwansa ba, tunda ba a ga Autaba kuma hakan bai tabbatar da cewa ta mutuba, abin duniya duk ya isheta, haka rayuwa ta kasance musu cikin nishadi har sun manta da wasu wai su Al-hassan da fatima da wata diyarsu Zainab bare Ammar dan kallo. 

Ammar ko haka yabi tsoho nan sunyi tafiya mai nisa sosao kafin suka shigo wani karamin kauye wanda gidajen ciki baifi a kirga ba, in kazo gida daya sai kayi tafiya mai nisa kafin ka iske diga daya, ko da suka isa kofar wani diga an masa rufi da da ciyawa sai katangan kara aka dan zagaya gidan naki biyu ne a gidan sai dakunan kaji da baru yan kanana da agwagi, suna sallama wata yar tsohuwa ta fito daga dakin danake zaton nan ne gurin kwanan su, tace lale maraba baki mukayi, ganin Ammar rike da joda ga jini ajinsu duka yasa tace lfy kuwa, suwaye wayan nan, tsohon nan yace bakine da sauri ta dauko taburman sakar kaba ta shinfuda musu, ammar ya kwantar da Auta tsoho nan daki ya shiga ya dauko wani yar jakar fata, ya dauko magani da nan ya kama kafar ya matse gun cizon saiga karin ya fito nan ya sake matsewa har sai da Auta tayi kara ta kan kame Ammar sai zufa tayi, saida yacire yashafa mata magani, san nan yasa inna laure ta dafa

Musu ruwan zafi ta kawo masa kadan a kofi ya saka magani yabama Auta da kyar ta iya shan maganin tana runtse ido.

               ®WWA®

 

  

Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

   

                ®WWA®

                             

Bayan Auta tasha maganin, sai aka dawo kan Ammar nan shima ya kunce daurin da yayi ma ciwonsa, tsohon nan da naji inna laure nakira da malam, ya dauko wasu magun guna, ya wanke masa ciwon da wani farin ruwa, nan ya haungo karamin glass ya shiga hannun, sai da ya dauko aska ya ciro glass din, duk da Ammar na miji ne sai da na ga indonsa yayi jajazur da alamar yana jin zafi sosai, baran ciwon ya kwana shiyasa, Auta kam kasa jure gani tayi sai kifa kanta tayi tana kuka maras sauti…,

wai yau itace a kungurmin kauyen da ko wuta babu bare ruwan fanfo, kafin asauko gun kwanciya mai kyau, nan take kalaman Dad dinta ya fado mata, inda yake mata nasihan sa na karshe akan ta yi hakuri a duk inda tasamu kanta, sabida yanayin rayuwa.

Allah sarki duniya kenan wai ace su baba sani su zasu kashe iyayenta akan dukiya da son duniya, mai suka maida zumunci ne ga cin “Amana” wan nan wani irin rayuwa ne sam tausayi ya kaurace a idon jama’a basa tunawa zasu mutu su koma ga Allah, in har kayi mai kyau zaka taras, kwanciyan kabari ma akabar mutum dashi babban aiki ne bare ace ka aikata mumunan abu har akaika wutar yasalam!!… Innalilahi wa inna ilaihi raji’un duniya tazo karshe wayan nan abun duk alamun karshen duniya ne Allah ya kyauta yasa mudace da karshe mai kyau ameen.

Hawaye ke gan garimata daga idonta, tayi nisa cikin tunani, sai ji tayi ana share mata hawaye, tana daga ido taga Ammar ne, shima hawayen yakeyi sai alokacin tasamu tasaki kuka mai ban tausayi, shima kukan yasaki, an rasa mai rarrashin wani.

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button