AMANA TA CE 1-END

AMANA TA CE Page 1 to 10

Malam da inna laure sun zuba musu ido sai kallonsu sukeyi, tabbas ko basu fada musuba suna cikin tsananin tashin hankali, nan take ina kaure ta fara hawayen tausayi, malam idonsa yayi ja sosai, malam kenan akwai tausayi ga taimako.

malam yace bawan Allah kai na mijine ka kasance mai juriya a kowani hali duk da bansan mai yasame ku ba aman da alama kuna cikin tashin hankali, kuyi hakuri, kusani duk tsanani yana tare da sauki, kuyi hakuri ku bar ma Allah komai, zai yi muku saukin Al’amarin, haka rayuwa take kowa da irin jaraban da ubangiji ke masa kuyi fatan Allah ya baku ikon ci, Ammar ya amsa da ameen.

Inna ta mike ta debu ruwan wanka a yar bahonta da tsage aka nane shi ta surka kafin ta kaima auta bayi, sai da ta taimaka mata kafin ta kaita bayi tafito ta barta nan ta dauraye jikinta, don ruwan da dumi sosai ya gasa mata jiki kuma ta samu dan karfi, bayan ya fito inna tasake sama Ammar ruwan ta kaimishi shima wankan yayi, bayan yafitoa wanka suka shafa mai dake lokacin da mina ne, a kwai dan sanyi kadan.

Malam ne ya hau kekensa yaje can kauyen da gabansu anan ake samu shago, yasayo musu suga, yadawo inna laure ta musu surki mai dumi sosai, don ya ware musu hanji, abinci ta dauko musu dambu tayi daman, kuma ta danyi da yawa, san nan Malam ya karamusu da nashi, aiko sunci danbun sosai don yunwa sukeji, sai da suka gama cin abincin, san nan sukayi godiya ga Allah da ya kubutar dasu, san nan Ammar ya juyo ya gode ma Malam, cikin kulawa malam yace karkada mu ni domin Allah na muku, ita rayuwa bakan wa zai tai make ka nan gaba, kuma dukiya da dan mitum, da dabba ba a musu keta, ku kara gode ma Allah ammar sai da yaji kwalla, asai ana samun irin wayan nan mutane a zamanin yanzu, Hamdalah yasakeyi ga Allah da ya ciyar dasu.

Inna laure ta gyara daya dakin nan dama da kyausa, in sunyi baki anan suke kwana, ta kwantar da yar katifar bonun da ke dakun tayi shinfidi akan gado, inna laure kenan duk da acikin kauye suke tsohuwar akwai tsabta, komai nata tsab2 gwanin burgewa, ga kamala da kyautawa.

Malam yace ga daki an gyara zamu kwana da kai inna laure kuma sai su kwana da kan warka, kafin in Allah ya kaimu waye wan gari, sai kubamu tarihin ku da abunda ya baroku da gida, Ammar yace to, Malam ya kara cewa meye suanan ka..? Amar ya nisa yace sunana Ammar ita kuma kanwata Zainab, Malam yace aaa babban suna gareta, sunan Mahaifiya ta gareta, Allah sarki Uwata zan kiraki da shi, har cikin ran Auta taji sunan da irin kauna da suka gwada musu, haka ta shiga dakin inna laure ta kwanta don huce gajiya.

               ®WHW®

  

Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

   

               ®WWA®

                            

Bacci tayi sosai akan yar katifan inna, sai magriba ta farka tayi sallah, bayan ta idar inna ta kawo musu tuwon dawa mai laushi miyar danyan kubiya yaji man shanu, sai kamshi takeyi,nan suka ci suka koshi, sai da sukayi isha’i kafin Auta ta dingisa kafarta tashiga daki ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa, Ammar ma dakin suka shiga shida malam suka kwana, 

Auta bata farka ba dai asuba da inna ta daga ta tayi sallah bayan sunyi sallah,

ta gaida inna ta din gisa zuwa dakinsu malam ta gaidasu ta dawo ta zauna, don ba halin taya inna girki,… Bata da lfy,

 inna ta musu dumame da kunun tsamiya, nan sukaci duk da damuwan da suke sai da sukayi santi don inna gwanar iya girki ce,…

sai bayan da suka karya kafin malam ya umurci Ammar da ya basu tarihinsa dana Auta, ammar ya gyara zama nan take idonsa ya kawo hawaye, da bai zubo ba ya fara dacewa,

Sunana Ammar Saad Saraki, ni haifafen dan maiduguri ne iyayena yan mai duguri ne, kenan su Barebari ne gaba da baya, baba na ya kasance dan gidan sarkin Gwaza ne, su biyar mahaifinsu ya haife su, Uku mata biyu masa matan akwai Ya fanna, da da hajja gana da Yakura, sai wan babana sunasa hashim sai babana mai suna Sa’ad, mahaifina ya taso cikin kulawa da kaunar mahaifinsa kasan cewar yana da nutsuwa sabani yaya shi da suke uba daya wato hashim, 

hakan yasa suka tsani baba na da mahaifiyarsa don shikadai ta haifa sauran hudun duk yayan kishiyarta ce Hajiya faima,…

duk tsanar da suka masa bai damesa ba ya nimi ilimin boko da na addini bayan ya kammala karatun degree dinsa ya dawo gd,

sai mahaifin sa ya masa Auren gata da mahaifiya ta, Hakimin liman kara, hajja faty mahaifiya kenan ta kasance mace ce mai kamala da kyautatawa ga hakuri da juriya ga sanin darajan dan adam, lokacin auren kudin da sarki Abdallah Saraki ya kashe ba karamin tada hankalin hajiya fatima yayi ba, nan tace ita mai yasa baza ayi auren danta ba, sarki yace a yanda bai nitsu ba shine shaye2 yar wa za a hada shi da ita, 

tun daga wan nan lokacin suka dau tsan gwama suka daura ma kakata da da mahaifiya ta, duk da hakan bai damesu ba, 

kwanaki sun ja yau wata 5 da auren mahaifina da umma na nan ta fara laulayin ciki, gashi yazo mata da laulayi, bata son shan ruwan fanfo sai na rija tunda suka lura da hakan, sukayi makircinsu aka bata ruwan gdn gaba daya don karta samu na sha, haka kullum sai anje nimota ta a gari don in bata sha ba tashin hankali ne, haka rayuwa tayita tafiya.

Sarki Abdallah Saraki, ya yanke shawaran sauka a mulki sai daura dana Sa’ad Saraki akan mulkin gwaza, tun daga randa sarki ya yanke hukunci, hankali hajiya fatima ya tashi, nan suka soma shiga bokaye, sai da suka san makircin da sukayi mahaifina ya dau mahaifiya suka bar garin bashi tun daga lokacin ba asan inda mahaifina yake ba, bayan tafiyan mahaifina bakin cikin yasa yagamu da ciwon hawan jini, harya makance da ganan kuma Allah ya karbi abunsa,……

Mahaifina na barin gari bai zarce ko ina ba sai kanon dabo tunbin giwa ko da mai kazo anfika,….lol…. Amma basufi yan Bauchi ba fa,

nan ya samu wani mutumin kirki ya rikesa a unguwar Dakata, haka yayi ta rayuwansa da umma na harta cikinta ya kai na haihuwa, nan laraba ta tashi da matsanacin ciwon mara nan sukayi asibiti, ana kaita ta haifi danta, tubarkala ko kalon dan batayi ba Allah ya karbi abunsa, asai masalan da aka samu lokacin tana mai duguri, maganin da aka a rijiya ta sha don karta haihu dake Allah yayi zanzo duniya sai da ta haifen lokacin ya mata illa sosai, shine sanadin mutuwarta.

          ®WHW®

  

Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

   

               ®WWA®

                          

Bayan anyi zana idarta matan da babana ke gidan ta karbe ni haka ta raineni har na girma na kai 15 yrs lokacin ina secondary school, haka zamu fita aiki mudan samo abunda zamuci sam baba na yaki aure, ana cikin haka malam suka shirya komawa garinsu, don suma mazuwa ne, yan jalingo ne, tunda suka shirya tafiya, mahaifi na yace na shirya muje muga yan uwansa, 

tunda ga ranan ya nimi kudin motan tafiya muka shirya ranan asabar 12 /3/ 2012 muka tafi mai duguri tun a hanya mahaifina ya ke cemin gabansa na faduwa, ko da muka isa mai duguri, muka shiga motar gwaza, muna isa yaga masarauta ya canza nan ya samu lbr rasuwan iyayensa, mahaifiyar sa ma bata dade da rasuwa ba, gidansu ya watse nan mukayi kuka tare, daga nan yace mu wuce cikin mai duguri, washegari muna zuwa, cikin garin mun sauka a tasha, kenan nace ma baba na ina jin fitsari, nan yace inje bayan gidan tashar na tafi kenan, 

Previous page 1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button