AMANA TA CE Page 31 to 40

®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:49PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Kunnensa makale da dan kunne manne kana ganinsa kasan yana taba rayuwa yahadu ba laifi sai dai bai kama kafar Ammar ba don ammar na daban ne shi, kausar na hango ta nufi guy din nan tana fara’a tana isa kusa dashi dukayi shaking din hannu tace ur wlc bros fuskansa dau ke da murmushi yace tanks my lovely sis munay ce ta iso da mirmushinta amma sai wani kwar kwasa take kai ka dauka gun sau rayinta zata tana ziwa tace ur wlc tanks yace mata Kausar ta karbi yar jakar hannunsa kafin suka rankafa zuwa inda motarsu take suka nufo gida cike da murna.
Zee auta tun bayan fitarsu ta ci kuka har tagode ma Allah ita yanda rayuwa ke zuwa mata kenan tana fita a wannan zata shiga wancan amma zata daure ko kadan barata bari ammar ya sani ba don ta ga yana cikin kwanciyan hankali.
Matsawan ya sani dole ne subar gidan ko ya dau mata ki ni kuma bazan zamo silan rugujewan farin cikinsa ba tunda baya son ganina cikin damuwa hmmm a hankali na sau ke wani ajiyar zuciya tare da cewa ya Allah gani gareka ka fiddani a cikin wan nan hali,
Alhamdulilah ala kuli hallin.
Saukowa nayi daga kan gado na nufi dakin munay duk ta birkita kaya haka na tattara na shiha toilet shima duk ta bata sai da na gyara mata kafin na tafi na Aunty kausar na ita ma na gyara mata duk da yana gyare bayan na gama ne na fito na nufi cikin na debi abinci na ci na yi wanka na kwanta don banson in ketare dokar Munay banson abunda zaisa ta wula kanta ni bayan nayi wanka Al-qur’ani na dauka nasoma karatu
har zuciyata, tayi min sanyi nan na kwanta kan sallaya bacci ya dauke ni ban farka ba sai karfe 2:30pm wanka nayi ina son in fito falo ina tsoron karo da su manay ga warning din da tamin kar in sake inyi make up kuma kar na hadu da Yayan su Ahyan ko mai yasa oho ni ina ruwa na ma da shi gashi tasa nayi nisa da Ammar dina dole wanda kullum muna tare da shi ga kulawar da yake b an na musamman nan take naji wasu kwallan ta kaici yana zubo min na goge hawayena na jingina da gado na fara yan adu’ah dana saba ina mai adu’ah ma iyayena da sauran musulmai.
Sannu a hankali suke tafiya yana kallon yanayin garin kunnensa dauke da ear peace yana bin wakokin Arjuli siyn shararen mawakin da ke raira wakokin India Ahyan yana son wakan sa sosai don shi ya raira wakar Ashque ma, a haka har suka iso G R A, a hankali Kausar ke tukin har suka zo kofar gate din su horn tayi cikin nutsuwa kafin mai gadi ya bude musu kofar gate din taje tasamu parking tayi parking da murna ya fito yana kiran Mum yayi cikin gd hajiya mamu ta fito da murnanta ta tari danta nan ta kawo masa ruwa mai sanyi sai kaga bakin hajiya mamu har kuni danta namiji tilo ya dawo yau kam murna ba a magana sai da ya huta kafin suka nuna masa dining kausar da munay suna gefensa Mum dinsu da kanta tayi serving dina sosai ya ke cin abincin yana santi bayan ya gama ya nufi dakinsa ko ina a gyare sai kamshi ya keyi wanka ya shiga bayan ya fito ya yi sallah sannan ya sake fitowa falo hira suka dan taba kafin H Mamu tace yaje ya huta nan ya tafi dakinsa kausar itama dakinta ta nufa.
Rash Kardam
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Kausar tana shiga dakinta ta ganshi a gyare ko ina murmushi tayi Allah sarki baiwar Allah gsky auta tana da halin kwarai ko jikinta barin dubota yanzu haka halan ko abinci bata ciba dakin auta ta leka ta ganta jingine da gado ta lumshe idonta da alamar kamar bacci take amma ba baccin take ba fridge taje ta dauko mata kunun aya ta nufi kitchen ta dauko mata abinci da plate ta dawo dakin a hankali ta ke tada ta Zee ta bude idonta taga Kausar ce murmushi tayi tace Aunty Kausar kun dawo lfy ya hanya kausar tace wato ko ki fito ku gaisa da bros ko auta tace zanje in gaida shi
Kausar tace to tashi kici abinci na san yanzu haka ba abinda kika ci ba musu auta ta mike taci abinci sukayita hira harsai la’asar kausar ta nufi dakinta don ganatar da sallah la’asar auta ma sallah tayi bayan sun idar ne suka shiga kitchen sukayi abincin dare bayan sun fito ne auta ta koma daki don yanzu ta hana kanta zaman falo bata son hayaniya sam.
Ammar business ya zauna ga shago sai kara habaka yakeyi abun sai son barka burinshi kulum autarsa ya ganta cikin farin ciki san nan komai ya samu ita yake sayama wa haka account dinsa ma da sunanta ya bude duk kudin da ake basa nasa yana sawa a gun kamar kulum da ya saba zuwa sari kano yaje yayi sari nan ya ga wasu dogayen riguna masu kyau haka ya saya musu su uku Zee Auta maroon da ratsin golden colour na kausar baki na munay ash da ratsin baki sosai yayi sayya yana ta sauri ya dawo don ya gana da dan hajiya mamu wato Ahyan don shima ya nuna nasa farin cikin dawowarsa.
* * * * *
Kaduna kuwa haka rayuwan futha da sadiya ya kasance yanzu futha ta gama diploma har tasamu Admission a degree tana gamawa zata tafi school of law haka tacigaba da gu danar da yan bincikenta don ta dau ma kanta alkawari sai ta gano wanda ya kashe ma auta iyayenta.
Sadiya ma haka abun yake karatunta take cikin kwanciyan hankali amma sai dai kulum tunaninta autar ta awani haki take ga iyayenta ku su nuna damuwarsu a kan magana gashi dukiyar sai habaka take abinda ya daure mata kai yanda taga wasu mutane tu da alamar ko bacun ransu baba isiya da Abbanta basa son gani gashi kuma mai gadin gidansu Auta da sun dawo sun dinke da iyayenta kuma wani abun daure kai yanda pinky kewasa da naira ba mai kulata sai kara daure mata gindi akeyi in yau ka ganta awan nan motar gobe da wancan kawaye kuwa sai yayan manya take harka da su abun sai hmmm don yanzu ji take da kanta tana kallon Big Girl ce ita ga naira ga hutu.
Ammar ya dawo yayi murna da ganin Ahyan sosai ya kawo tsara ba masu auta da kausar san nan yanzu an yanke shawarar zai fara fita waje nan yayi murna da godia san nan ya ce ma auta ya kamata suje kauye su gaida su Inna larai da Malam don su musu karamci da bazasu taba mantawa ba, hajiya mamu ya samu ya mata bayani tayi murna san nan ta basu goma na arziki sukai musu nan kausar tace zata bisu tunda gobe zasu dawo munay sai wani yatsina take ita ala dole tana kyamar yan kauye,
Tunda Ahyan ya dawi ko da wasa basu taba haduwa da auta ba yau kwanansa 4 ya ba masu kausar hakuri akan kayansa ran Thursday sai iso sukace ba matsala,
Ammar wanka yayi sosai haka ma auta sunyi kyau kausar ta dau Camera don tana son zuwa kauye ran asabar da safe suka dauko hanyan suwa kauyensu Malam suna masu farin ciki.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:49PM, 9/20/2016] Rash Kardam: [10:47AM, 4/5/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Sai karfe 12:00 suka isa garin sun samu su inna cikin lfy bakaramin murna sukayi da ganinsu ba nan ina ta musu tuwon geronta mai kaushi miyar danyen kubiya ga man shanu sosai su kaci suna zuba santi baran Kausar ma tafi kowa santi don ta dade bata ci irin wan nan abicinba ga surki yaji suga sosai koni rash sai da na lashe baki don yawuna yana tsilo tsabar kamshi ya ishen.