AMANA TA CE Page 31 to 40

Sai da suka huta bayan sunyi sallah asazahar tukun ammar ya basu tsarabansu nan sukayita murna kafin suka fara hiran yaushe gamo nan ammar ke bama su inna lbr bayan barin su garin sun tausaya musu sosai sai yamma sukayi wanka suka fita zaga gari dandali suka nufa tun daga nesa suka hango yam matan garin sunyi wanka masu sayar da abinci na sayarwa abun dai sai kun gani.
Najaat ce da tawagar kawayenta tunda ga nesa ta hango ammar da su auta zunguro ummen da zulai kaii kalli wancan kamar wanda suka taba zuwa maciya da malam la shine dan birni kai kali wancan auta ta nuna sina kama da wan nan yar India mai gashinan ga kawarta ma kamar yar india nan suka saki baki sai kallinsu suleyi haka su auta da kausar da ammar sukayita hotuna sai magriba sukamar dandali suka dawo gd bayan sunyi sallah ne suna zaune suna hira sukaji surutun mutane da yawa kuma mata sai azo a dan lekasu a koma
can dai abun yayi yawa sai malam ya mike ya a hankali ya fake aiko lokacun su najaat suka leko karaf malam ya rike ta waye nan tafara inda2 daman tazo gaida ina ne sai taga yan birni malam da ya gane waye sai ya kyaleta yace su bar labe ba kyau nan suka shiga cike da murna suka gaida su inna sai satan kallon ammar sai da suka dade sosai kafin suka musu sallama suka nufi gd su malam ma sukayi sallama wa su auta suka shiga dayan dakin inna da kausar da Zee suka kwana daki daya da safe inna ta soya musu kosai da yar tsame ta musu kunun tsamiya haka suka karya cikin farin ciki daga nan suka fara shirin dawuwa bauchi,
Su inna sun cika mu da tsaraban kauye su daddawa ne wake gyada kuka harda zuma,
Wanka sukayi sannan ammar ya ciri 10k ya bama malam inna ko 5k godia sukayi sosai kafin suka rakosu gun motarsu suka dau hanyan bauchi.
Tun bayan da su kausar suka tafi kauye da yamma ahyan tazo cin abinci ya ga ga abinci har abinci a ido yana sawa a baki yaji ba test karshe haka ya hakura tea ya hada ya sha mum ma da tana sawa a baki ta ajiye gashi hauwa bata nan ta shiga cikin gari yau munay ce tayi abinci sai da ta sha tea kafin ta kira munay tayi mata fada akan ta dage ta koyi girki din girki shine mace kiga kausar da Zee mana yanzu ina ne zasuje baza suyi abinci wa mitum yaci har yana santi Munay sai zun bura baki takeyi ita a dole an mata fada ta tashi ta nufi daki sai kunkuni takeyi haka dai a daddafe suka kai washe gari Mum ke musu abunci ahyan ma ya masu kausar ta dawo don yafi gane cin abincinta sai ko in mum ce ta musu yana ci sosai.
Ba mu iso cikin gari ba sai kusan 1:40 dake ba mu fito da wuri ba ko da muka dawo wanka mukayi muka ci abinci kafin mukasa aka shigo da tsaraba muka nuna wa mum yau hauwa’u mai girki ta dawo dan haka daki na nufa na fara baccin gajiya.
Yau kwanan mu 3 da dawuwa daga kauye kulum gidan mu cike yake da wakar india daga gani nansan yayan su kausar ke sawa kuma shima da alama masoyin wakokin india ne kulum in ina daki yasa wataran nayi rawa wataran in zauna ina bin wakar baran wakikin Arjuly Siyn ina son wakarsa yau tun da safe munay tazo ta min warning in gyara mata daki san nan in kade mata cikin Waldrop dinta zata fita sai yamma zata dawo tun da ta fita nasa ka wando wizy da yar rigata mai dan tsayi ya kama jikina nan nashiga na gyara ma munay daki na fito zan sauka kasa dauko dauko fresh milk insha don nayi aiki sosai ina fitowa naji daga wani dakin da ke kusa da down stairs naji ansaka wakar Vear wai take Surili akhiyon wale, daman mayar wakan ce ko ada nan na fara tika rawa irin na wakar don mutum2 ake wakar amma ni daya nakeyi sai nan take na tsinci kaina cikin ni shadi ina bin wakar ina rausayawa.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
A hankali ya ke saukowa sanye da 3quater da yar riga mai gajeren hannu, ya jimma a tsaye yana kallonta wannan wacece da bai taba ganinta ba ko ita ce Zee din da mum ke fada gsky yarinyan ta hadu ba laifi wani juyinda tayi a rawan sai da yasa Ahyan hadiye yawu don wannan tana daya daga cikin irun matan da ya ke so ta hada koma2 gyara tsayuwa yayi yana kallinta don baison ta bar rawan,
Sam ita bata san da mutum ba tsakaninta da Allah take tika rawa,
Dai2 nan Ammar ya shiga kallon ta yakeyi cike da so da kauna dake yasan ita mayyar wakokin india ne ganin auta cikin farin ciki yasa shima ya tsinci kansa cikin farin ciki sai a lokacin ya lura da ahyan da yayi tsaye yana kallonta nan take ransa ya baci kishin sa ya motsa bai san lokacin da yaje ya mata wata damka ba kee baki da han kaline bakisan akwai wanda bai kamata su kalleki haka ba tsaya wa nayi ina masa kallon tuhuma sai a lokacin naga ahyan ya karasa saukowa sai min wani kalo yake wanda ni kaina sai da na tsargu,
Munay ce ta shigo ko sallama babu ganin irin hallin da muke ciki yasa ta nufo ni da sauri kee baki da han kali ne zaki fito cikin irin wan nan shigan duk ta rude kai ka rantse a kwai mijinta a ciki na fito da wan nan shigan nan take jikina ya hau rawa da gudu na haura sama ammar kam dakinsa ya koma ransa duk a jagule ahyan kuma bayana yabi da kallo yaga duk yanda illahirin jikina yake motsawa tabbas dole yasan abinyi akan wan nan yarinyan.
Wacece Hajiya Mamu?,..
Asalin sunanta Maryam Alkali haifafiyar garin katsina ce aure ne ya kawota bauchi,
Hajiya mamu ta taso cikin kulawa da tattalin iyayenta Alhaji Alkali mutum ne mai karamci da sanin ya kamata yana da mata daya mai sunan Xahra mace ne mai mutumci da kamala shekaransu 2 da aure basu sami haihuwa ba sai da suka shiga shekara na 3 Allah ya basu haihuwar diyarsu ta farko maryam inda suke kiranta da Mamu sai bayanda suka sanu shekara 4 Allah ya sake basu haihuwar fatima haka suka taso cikin kulawa da kaunar juna inda mamu tayi aure ta auri wani shararen dan kasuwa bayan tayi aure da wata 3 Allah ya bata cikin ahyan haka sukayita tattalin cikin har tazo ta haifeshi yaci sunan Ahyan ma’ana Gift of Allah
Bayan shekara 2 akayi bikin fatima itama bayan aurenta da sheka 4 ne ta haifi Kausar kenan kausar yar kanwan hajiya mamu ne tunda fatima ta haifi kausar ta kamu da lalurin rashin lfy bata dade tana jinya ba Allah ya karbi abunsa nan H Mamu ta karbi kausar ta dawi hannunta sai da kausar ta kusa 4 years hajiya mamu ta haifi munay haka taci gaba da kula da yaranta tana basu tarbiya mai kyau mijinta yana kasuwancinsa ka Allah ya sanya musu Albarka dukiya sai haba ka yakeyi kwanaki sunja lokaci ya tafi har ahyan yagama secondary nan Abbansa ya fara shirye2 na fitansa karatu waje yayi hatsari ya rasu tabbas sunji mutuwar nan ba kadan ba bayan yanyi arba in ne hajiya mamu tayi ciki ciku yatafi karatu kasar waje nan ita kuma tani mi aiki tana zuwa sam taki aure don tana kula da yaranta Kausar dake tana kama da mamarta in ka ganta baakace ba hajiya mamu bane ta haifeta ba don suna kama munay da dad dinsu tayi kama sam ita halinta ya fita daban bata son kowa a kusa da ita ga jinkai ga nuna isa kamar yar President.. Lol…
Yawancin kawayenta yaran manya ne bata harka da yaran masu kananan karfi acewarta za a raina ta don kalin kanta take kamar yar gidan dan gwate ….lol…