AMANA TA CE 1-END

AMANA TA CE Page 41 to 50

 Munay kuwa ganin kar dan uwanta ya mutu, yasa ta mike tana dingishi, ta nufi harabar gidan isa mai wanki ta ganin nan ta kwala masa kira, kazo ka taimaken, sanin halinta yasa ya biyo ta da sauki, sama suka haura nan tace ya kamata ahyan ahaka suka fito, mai gadi ke tambayan ta, maike faruwa? Wani mugun kalo tamasa wanda yasa dole yaja bakinsa yayi shiru, sabida sanin halinta, da gudu suka nufi T.H, suna zuwa emergency ta kaishi nan doctors sulayi caaa akansa basu dau lokaci ba suka gyara masa ciwon da yaji kuma ya farfado amma sun masa aluran bacci, sannan suka nufo munay suka fada mata san’nan ta tanadi kayan tea, don in ya farka ta fara bashi ruwa mai zafi ya sha, nan tayi godiya ta nufi hanyan gd.

Ammar ko ganin an wuce da auta ga kayan da ke cikinta duk ayage yake wani sas’san jikinta na aje, yasa ya nufi gd don ya dauko mata kayanta acanza mata, bai ce kala wa H Mamu ba don wani haushin su yakeji, fita yayi ya nufi gd a mota don yana hanzari baya son yin nisa da auta, gani yakeyi kamar za’a sake mata abunda aka mata, yana isa gd, dakita ya nufa ga mamakinsa bai ko ga su munay ba amma dake ba damuwar sa bane kuma baya son ganin su, nan ya dau mata fallen zani da karamar riga, sai hijab, yazo fita kafarsa ta gogu da takalmin auta nan yaji wani azaban zafi da sauri ya kali gun, sai alokacin yaga ciwon da yaji, bai tsaya takan ciwon ba yazo sauka daga stairs yaga munay tana tahowa sai dingishi takeyi, wani mugun kalo ya watsa mata, fuskansa sam ba ko annuri, kamar baitaba dariya ba, nan take wani tsoronsa ya dira mata azuciya.

    Luv u all my fanz

Rash Kardam

[7:57PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

 

                           

Wani mugun kalo yamata, yanzu tsoron ammar ta ke baran da ta tuna nashin da ya mata da sauri ta dawo da baya, ta sauko sai da ta bashi hanya ya fita, sannan ta haura ta debi duk abunda zata diba ta dau poss dinta dake tana da kudi aciki ta nufi asibiti, tana zuwa ta nimi gu ta zauna ta zuba tagumi tana kalonsa, tana fatan Allah yasa ya tashi.

Ammar ko yana fita ya nufi dakinsa ajiye ki din mota, don shikam yabar amfani da abun gidansu kuma yau zaisa afara nima musu gd, don tabbas shine silan ja ma auta wan’nan abun, in da bai yarda yazo gidan nan ba da ahyan bai mata haka ba, ko da ya fita abokinsa auwal ya kira yace masa gd yake so mai dan saukin kudi, amma ba wanda yake da mutane da yawa ba, auwal yace an gama zuwa gobe zakaji “feedback” nan sukayi sallama ya nufi asibiti, yana zuwa yasamu H mamu suna inda suke sun zuba tagumi, nan yaji tausayinta, gsky tayi masa karamci gashi tilon danta na miji ta wasa abunda bata tana zaton zatayi ba, bata so kanta ba ta bama dan ta laifinsa, gaskiya hajiya mamu tacika mutuniyar kirki uwa ta gari, wacce take son yayan wasu ta kuma kula dasu tsakaninta da Allah, Hajiya mamu Allah yasaja miki ya biyaki da rikon gsky da kika mana ameen, amma bazan iya cigaba da zama’a cikin gidan ki ba, don tunda yasoma kuskuranta, nan gaba zaiyi abunda yafi haka ni daman hankalina bai kwanta dashi ba, cikin zuciyarsa yake magana, sai da yaji H mamu tace ammar sannu da dawowa, firgigit ya dawo hayyacinsa, Murmushi ya kakalo wanda yafi kuka ciwo yayi, ammar duk yaba ma hajiya tausayi lokaci daya duk ya canza kamar bashi ba, kausar tamasa sannu, ya amsa ya tambayesu ya mai jiki sukace haryanzu dai ba lbr, kayan ya mika musu yace ya kamata su je gd su huta, h mamu tace ina ae ba inda zata zata kwana da auta, tace kausar taje gd, ido ta zaro don auta bata tsira itama tanaga intaje abunda zai mata kenan bare uwansu badaya bare uba, don da aure a tsakaninsu, ajiyar hrt tayi kafin tace mum kata kafarki, h mamu dake babbace ta gano kausar kuma sai taji badadi azuciyarta danta yau ake gudu,(umm tsakanin uwa da danta sai Allah duk da taga laifinsa amma sai da taji wani iri, yan’uwa ya kamata mu na tausaya wa iyaye mu kyautata musu, don sun sha wahala ba kadan ba akan mu ya Allah kaba mu ikon tausaya musu da jin kansu, kaman yanda suka mana muna kanana Ameen).

Su hajiya mamu da kausar suka kwana a dakin masu jinya, shiko zama yayi a kofar dakin akwai chair azaune ya kwana da safe bayan sunyi sallah yaje ya sayo musu abinci, suka karya sai ga Dr ta zo nan suka gaidata, suka tambayeta ya mai jikin tace musu da sauki nan ta wuce office dinta, wayarsa ce tayi kara yana daga wa yaga auwal da sauri ya dauka, bayan sun gaisa yace my man an samu gida ku biyu ne aciki amma yace min daki2 ne in kana da tym sai kazo muje a nan dutsin tanshi ne, yace ba matsala na gode sukayi sallama ya kashe wayarsa, sai kusan 10 ya bar asibiti direct gun auwal yaje, sun duba gd ba laifi yayi gashi daki dadai ne, ko wan’ne da bayi aciki san’nan akwai kofa a tsakiya, sai ta waje ma akwai kofa kamar na falo ta wajen gidan sai yar karamar gate dake gun, kuma gidan na da kyau sai na dayan yana tsam’manin ciki da falo ne da bayi, sai kitchen da wani karamin daki na saka kaya, dake bauchi muna da arahan haya kudin ba masu yawa bane, 60k ne kawai nan yaga arahansa don inda a kaduna ne abun sai a slow, nan yace zaibada kudin zuwa jimawa san’an yasa aka kira masa almajirai ya biyasu yasa su wanke masa dakin don yau zai kwaso musu kayansu ko gobe.

Yana fita bank yaje ya zaro kudi a account dinsa don duk wata hajiya mamu na sallamansa da 30k kudin da take basa gashi yau kusan shekaran su 2 da wani abu, a gidan kunga ya dan samu wani abu, duk abunda ya kamata ayi anyi, yaje gida dakin auta ya kwaso mata kayan ta dake sif dinta wanda yasan’nata ne, shima ya dibi nasa, ya ajiye, kasuwa ya shiga ya sayo musu katifa manya guda 2, yazo ya ajiye, ya gaji likis gashi yanzu magriba ta kusa duk da yana lekasu ya tambayi lfy auta, yanzun ma asibitin ya nufa.

Munay tana zaune ta zuba tagumi, ahyan yasoma bude idonsa, yana kalon dakin da kyau, sannu a hankali ya komai yasoma dawo masa, kara yasaki yana kiran no! no! no!, ( nikam nace to no! Din na me nene ko yaso sai ya gama biyan bukatar sa ne? oho, ko haushin da mum dinsa ta gansa ne? Oho zamuji koma miye nan gaba).

Taku a kulum mai kaunar ku

Rash Kardam

[7:57PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

 

                           

Ahyan bakaramin damuwa ya shigaba, yau yasan mum dinsa tayi fishi dashi bai kuma kyauta ba, dole yaje ya bata hakuri, da kyar ya iya shan tea ya sha magani ya koma ya huta.

 

         Yana isa asibiti ya gaida su H mamu, san’nan yanufi gun Dr yake tambayart cikin Zee tace d sauki, dakin ya dawo ya zauna a gefe, ya zuba ma auta ido ko kyaftawa baya yi,wayar H Mamu yayi ringin tana dagawa taga munay ce, da kamar bazata daga ba, amma sai ta dauka daga daya bangare akace, “hello mum ya kk? Mum duk abunda bros ya miki ya kamata kiyi hakuri ki tausaya masa, kizo ki ga jikinsa, a kan wan”nan yar da ba’a san asalinta ba, sai wai2 amma ki kyale dan ki wanda kikeso” wani tsawa ta daka mata nikaina sai dana tsorata, wato munay kema bayansa zakibi ko? Kuma kar in kuskura inji kin kara zaginta ni baruwana da shi, har sai ya gyara halinsa tukun mtss ta kashe, ammar har rashi saida yaji taisayinta don tacika uwa ta gari ba mai son kanta ba, sai yau yaji kara sonta a matsayin uwa, “Allah ya biyaki mum”, kausar ma jikinta duk yayi sanyi ammar yayi karfin hali yace mum kije ki dubasa da jiki, duk abunda zaiyi bazaki taba kankare alakar kuba, “hannuka baya ruba ka yanke ka yar” dan kine dan haka adu’ah shine mafita, taji dadi amma bata nuna ba sai kawar da kan ta tayi kamar bata jishiba.

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button