AMANA TA CE 1-END

AMANA TA CE Page 41 to 50

 Zee ce ta fara motsi kada2 sai tasaki wani kara take sukayi kanta dukansu, ihu take tana kiran sunan Allah, sai kuma ta soma cewa Ammar…. ammar….. Ammar kazo ka kwace ni zai kashe wayyo Allah na, wayyo mum kun tafi kun barni, ammar da sauri ya je ya kira Mrs Abdul da sauri sukazo allura ta mata take bacci ya sake daukarta, Mrs Abdul tace karku damu zata farka cikin hankalinta, ajiyar hrt ammar yayi godia ma Allah dr tafita ta basu gu.

        Sai can dare ta farka, taga mum nan ta soma tuna mai ya faru kuka tayi sosai, mum na lalashinta, tea ta hada mata tasha ta kai mata ruwan wanka tayi taji dadin jikinta kafin tayi sallah.

        Ahyan kuwa an sallamesa cike da tsoro da zullumi ya shiga gd, da farko kam yaki shiga sai da munay tashiga ta duba masa ko mum na’nan, taga batanan tukun ya shiga gidan.

         Kausar jin munay na gd yasa tadawo kuma hauwa mai aiki ta dawo yau, tukun ta koma gd, ya rage h mamu ke ajikinta, gsky ta gwada musu kulawa.

Sai can yamma ammar yazo yana gun cuku-cuku neman shagon da zai dan sari kaya yazuba aciki, ya fara business da yan kudin da ya tara na albashin da yake samu.

Sai da ya gaida h mamu tukun ya yima auta ya jiki? ta amsa da sauki, sun dan taba hira kafin yace ma mum yana so zai roki gafaranta don ya mata laifi sai da ya bata hakuri kafin yasanar mata da hukunci da ya yanke, da farki taso taki akan sai dai ahyan ya bargidan, ammar ya nuna mata ilan hakan san’nan ta amince, sun na cikin hira Mrs Abdul tazo ta basu sallama, kaya suka tattara san’nan ya tsara musu napep suka je gudan sai da h mamu ta gyara ma auta daki duk da a gyare yake kafin ta musu salama akan gobe zata dawo.

         Ko da ta koma gd tasamu ahyan ko kalon inda yake batayi ba, da gudu yazo ya rike kafarta yana bata hakuri tureshi tayi ta wuce idonta cike da kwalla, “a zuciyarta tausaya masa amma sai ta gwada masa kurensa”.

Washe gari sukaje da kausar suka duba auta tare da kayayaki bayan sun dade suka musu sallama suka dawo, washe gari ammar ya tattara yan kudin h mamu da ya sani da wasu ta kardunta ya kaimata yabata hakuri sam bata so ya bar yi mata business ba don yaron yana da “AMANA” amma ba yanda ta iya haka ta hakura nan ta dibi kudi mai yawa tabasa yayi godiya ya fito kenan suka tsaya da mai gadi sunyi hira sosai sai kusan 9:00 ya nufo gida ya sai musu nama da yan kayan motsabaki abakin titi mai mashin ya ajiye shi yazo shiga lugun gd da suka koma wasu yan’isa suka tsaresa harda wukakensu suka nuna kudi suke nema baiyi musu ba ya basu kudin da aka bashi, har sunce ya tafi dayan yace kai tsaya ban…..

Taku mai kaunar ku a kulum

Rash Kardam

[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

 

                           

Wani daga cikinsu ya ce tsaya, baiyi musu ba ya tsaya, daya daga cikinsu yace haka zamu kyaleshi baiji a jikinsa ba,ammar adu’ah ya ke tayi na neman tsari, gani basa kusa da shi kuma yana yin kwana zai shiga gidan da suka kama, fakar idonsu yayi yasa gudu don ya sadakar ko ya tsira ko su mishi illa, iya karfinsa yake gudu yazo dai2 shiga gidan kafin ya bude kofar gdn, wani daga cikin yan saran ya kai masa sara cikin ikon Allah bai same sa sosai ba, ya shiga gidan sakata. 

Auta jin haya niya ta fito ita da matar gd sun tsaya cirko2, nan matan gd take bata lbr yan sara garin nan take auta ido ya ciko da kwala, yayanta ta tuna ko a wani hali yake oho nan ta fara masa adu’a kariya daga uban giji, suna tsaye agun sukaji an rufo kofa matar rayi daki da gudu sabida tsoro, auta kam ko motsi kasawa tayi da sauri tayi zaure tsaban dakiyar zuciya tana haska wa taga ammar da sauri tazo ta rike hannusa tana hawaye shiko ido ya runtse sabida safin ciwo sai mai da numfashi yake yi kama hannunsa da auta tayi yasa ya bude idonsa, han’nu da ba ciwo yasa yana goge mata hawaye suka nufi daki, dan kwalinta ta yanka biyu ta daure masa han’nu tana masa san’nu ya amsa.

 3yrs leter

Garin kaduna wata kyakyawan yarinya na hango cikin farin ciki ta nufi gidan inspector Abubakar ko dana kare mata kalo naga futha ce ta kara girma sosai tadawo cikakiyar mace abun sai mai karatu ya ganta, cikin murna iyayenta suka tareta bayan yar kwarya-kwaryan malimar da aka shirya mata, sadiya ma ta hallara inda yanzu tagama karatunta ta dawo cikakiyar yar’jarida walima ya gudana cikin kayatarwa.

     Baku tambayeni ya labarin pinky yar’rawan kai, hmm ku biyo ni kuji.duniya ta juya don yanzu pinky ko yar motar da take ja babu don yanzu dukiyar baba isiya ta kare ba abunda ya rage masa yanzu sai diabetes da tasa sa agaba har an yanke kafa daya gasa rai kwa-kwai mutuwa kwa-kwai, don shi tun daga duniya yafa ganin nasa saka makon bai ko ina ba matansa sun gujesa don tanzu ba abun duniya.

       Baba sani kuwa ba laifi komai yana tafiya yanda ya kamata don har ya manta da wasu yan’uwansa da kuma yar’auta rayuwansa ya ke ci son ransa.

       Garin bauchi kuwa ammar da auta ci gaba ya samu cikin she kara biyu Allah ya buda wa ammar ya albarkaci dukiyarsa da ya nema da guminsa yanzu shaguna 2 garesa na atamfa da shadda less masu kyau sai na takalma da jakukuna, wani abun dadi sunan auta yasake mayarwa, haka rayuwansu ya kasance cikin jin dadi da farinciki, watara na ammar suna zaune da auta take cemai tana son suje kaduna ko da ba dade wa zasuyi ba, ina son inga futha da sadiya don nasan bayan tafiyata suna cikin damuwa ina son inga wasu yan’uwa, ammar yace ina sane da haka don ba yanzu nake son zuwa ba akwai lokaci in muna raye don na dau wa kaina alkawarin matsawan ina raye sai na dau fansa masu Dad da mum kuma sai an yanke masu baba sani hukunci dai2 da laifinsu, auta har cikin zuciyarta taji dadi ta kuma kara masa fatan na sara.

        5 weeks leter

Ammar ne a shago yana ta fama da jama’a cikinsa ya fara murda masa tun na daurewa abun har yasoma da munsa kafin kace me ammar ya fadi akasa cikin firgici yaron shaginsa ya dauwaya yana son ya kira auwal abokinsa ya kira auta cikin rudewa yake mata bayani akan zasu kaishi asibiti, sai da tayi magana ya ga ba auwal ya kira ba, da sauri ya kira na auwal akwai yace gani a kofar Central market din yanzu zan shigo da gudu yazo suka daukesa sai “NI’IMA CLINIC” auta cikin rudewa ta kira wayansa nan auwal ya daga tana kuka tace kuna wani asibiti ne yace suna ni’ima tace to gata zuwa, duk da bawani yawo take a gari ba mai napep tatsara ya kaita tana zuwa ta samu auwal sai safa da marwa yake a kofar emergency, nan yasoma lallabinta don kuka take sosai, ana cikin haka nurses tafito ta ba ma auwal ta kardan magani yace bari yaje ya sayo.

Dr tace tafito auta na ganinta ta nufeta tana hawaye Dr ya jikinsa, ta ce da sauki, ke ce matarsa, auta kamar ta ce aa ta dauka ba wani abu bane kawai sai tace eh nice ok!! Ki biyo ni office to tace Dr tayi gaba tana binta a baya sai da sukaje wani office ta nuna mata kujera ta zauna, sai da Dr ta cire glass din idonta, tace ya sunan ki madam tace Zainab, Dr tace zainab daga ganin ki kamar wayyayiya amma kina abu kamar baki san komai ba, ae yanzu kai ya waye, duk auta na cikin duhu sai da Dr tace mai yasa baki ba wa mijinki hakkinsa kinsan laifin ki kuwa Allah na fushi dake haka mala’iku suna tsine miki, ga shi kinsa mijinki cikin wani hali yanzu in ya fara bin matan banza fa hakki na kanki, don a yanzu haka sperm ya masa yawa don in bai samu ya biya bukatarsa ba zai iya shiga ko wani irin hali, auta sai da taji gananta ya fadi, dake Dr macece nasiha ta mata sosai, tukun tace ta je ta duba mijinta, sai a lokacin suka ga sun dade sosai kusan 1hrs tana mata nasiha kwatance dakin da aka kaisa tamata, auta jiki ba kwari ta fito ta nufi dakin.

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button