AMANA TA CE 1-END

AMANA TA CE Page 41 to 50

         Ammar ko bayan da aka masa allura ciwon cikin bai dade ba ya lafa, auwal a gefensa kusan 40 minutes yayi ya farka dake jinisa da karfi ko alluran bacci aka masa bai cika dadewa ba, nan auwal ya fara masa nasiha akan tunda auta yakeso ya fito ya fada mata ko yanimi wata ya aura, sai da yagama maganarsa kafin ammar ya fara magana da ni bana son takura ma zainab don banga alamar tana sona ba, abunda ya hanani sanar mata kenan kawai shakuwar da mukayi ne, ni kuma banjin zan zauna da wata mace kamar bazan iya mata adalci ba, zuciyata zainab take so, sai hawaye ya fara zuba masa amma zan bama zuciyata hakuri matsawan zainab taki amincewa na auri wata ko don gudun fadawa halaka.

Auta da ta dade da isowa tana shirin shiga taji anakiran sunanta, nan taji duk abunda suke fada kuka takeyi tana fadi bazan iya ba Ammar .

  

Hmmm karkuso ku gani alokaci idi na zaro don tsananin mamakin auta duk halaci da ammar ya miki cab… Ko dai mai take nufi zamuji nan gaba.

Taku a kulum mai kaunar ku.

Rash Kardam

[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

 

                       

             Ammar abu duniya ya ishe sa, zaune yak’e a shago, ya zabga tagumi, wayar sa ce tayi kara ya duba yaga Auwal ne, ya dauka da sallama sa, daga ban garen Auwal yace” kana jina Ammar ta fiya ce ta kamani ta gaggawa zan fita zuwa waje,” kana leka min gun business dina komai ake ciki kana sanar da ni.

Ammar ya ce “ba matsala Allah ya k’are,” sai ka jini.

    Hajiya Mamu ce zaune tak’e na zarin hukunci da yakamata ta yanke ma Ahyan, ta dad’e ta na tunani, kafin naga ta saki wani lallausan murmushi, wanda hakan yak’e tabbatar min da ta samu amsa ta.

 Munay ce ta shigo gdn, H Mamu ta mata kalon tsaf tana na zarinta, sunan ta kira Munay zo nan, tazo ta zauna, a nats’e ta ke kalonta, Munay ina kike yawan zuwa kw’ana b’iyu?, ba kya yawan zaman gida, fada min?, “cikin zafin rai tayi maganar.”

           Munay duk ta tsorata da yanayin Mum dinsu, kame-kame ta far’a yi, tsawa ta sake daka mat’a, Mum da… Ma..umm..um.. Wani mari ta sakar mat’a, kin bar fit’a. “sam ni ban yarda da tarbiya kawarki sholly ba.

Fada ta mata sosai, ta tashi ta bar Munay a gun.

       

           Ahayn karatun sa yak’e ba wasa, duk randa zasuyi waya da “Munay sai ya mata nasiha sosai mai shiga jiki. Don shi yanzu ya fita harkan yan’matan b’ariki, ya kima ga Allah.

          Auta z’aune tana nazarin abunda take ma Ammar sam wani sa’in bata ky’autawa amma ta rasa mai yasa zuciyarta ke sata hakan, abun na da munta, ga wasu muna’nan makarkan da rakeyi, wani sa’in ma ko ta f’arka, bakinta kasa furta addu’a ya keyi.

Haka rayuwan su ya kasance, ba d’adi, don yanzu “Ammar ya bar shiga harkanta,” tun daya gane bata son ganin sa bare farin cikinsa.

Sam ba zai iya mata wulakanci ba in ya tuna “Dad da Mun da AMANATA da suka bashi, sai yaji ba zai iya wulakanta ta ba.

     Munay ke shirin ta na zuwa gun “Malam don yau’ne zai gama mat’a hadin mafani ta,da in ta tun kari “Ammar bazai iya mata musu ba.

 Da kyar ta samu ta fito a gida ba tare da Mum ta ganta ba, ta dau hanyan Firo nane garin da bokan yake. Tayi tafiya mai nisa har ta kusa g’arin, tun daga nesa ta hango wasu mutane sun taru amma basa da yawa, basu fi su b’iyar zuwa shida ba, sai da ta iso kusa ne taga wata motar da tana yawan zuwa gidan Malam, kamar zata wuce ganin hatsari ne yasa ta d’awo da baya ta tsaya. Matar da tak’e zuwa a motar ne ta yi hatsari, ga wasu muna’nan magan-ganun da tak’e fada, ba dad’i ji. ” ni Jimma’i na kashe Farida, ni nayi asiri ma Sadiq ya bata, ni na haukata zainabu” da sau’ransu, abun ba dad’i ji.

 “Munay jikinta yayi sanyi, tasoma nadamar a’bunda tak’e aikata wa. Kafin su bar guri “Matar nan ta cika tana ihu tana birgima a cikin dati.( Mata muji tsoron Allah kar ku d’auki zuwa gun boka a’ bu ne mai kyau, tun daga ranar da zaki sa ka f’arki sallah bazata karbu ba, ga azaban lahira ga haduwa da karshe maras ky’au, muji tsoron Allah mu gy’ara).

Munay ta shiga motarta, ta dawo gida cik’e da nadama, kuma yau zata fasa kwalban da “Malam yace asirin ciki kwalban, zai raba Ammar da Auta. Kuma zan nimi gafaran su, kar nima nayi irin wan’nan mutuwar.

            Garin kaduna kuwa yau sun tashi da jimami don yau sunyi rashin “Baba Isiya, Allah ya karbi abunsa.( tabbas duniya ba gurin zama ban’e, ko kai ko ka so sai ka bart’a. Yan’uwa mubi duniya, a san’nu in ka d’auka da zafi, zaka ga da z’afi, rayuwa bata da guarantee).

Su “Pinky an shiga damuwa,” yanzu sai Mum dinta k’adai ta rage mata. “Ya Allah ka jarrabe mu, jarabawar da zamu iya Ameen”.

        Auta ce zaune tana sauraron wa’zin Malam ja’afar Mahamud Adam, sosai wa’azin ke shigarta, gashi yana baya ni game da yawan Addu’a da amfanin zama da al’awala, duk sai taji kamar ta ita yakeyi, tunani ta far’a ” Yaushe rabon da na zauna da al’awa?, Yau she rabon da na yawaita yim azkhar?. Tabbas ko tantama b’abu shiyasa nak’e yawan ma farkai. 

“Yaro ne yayi sallama, ana kiran Zainab a waje,” wai tazo yana jiranta. Wani gaushi ne ya tur’nuketa, mts tayi tsuka.

Taku a kulum mai kaunarku

 

Happy birthday to you Maman Abideen, i wish you long life n prosperity.

Rash Kardam

[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

 

                           

          Auta ta d’ade a bakin k’ofar “Room”, duk “maganar da su k’ayi taji”.

Kuka ta k’eyi sosai tana fadin no!! B’azan iya ba, Ammar.

         Ta d’ade a gun tana k’uka, sai da taji ‘Auwal na shirin fit’owa’, kafin ta share hawayen ta, nufi d’akin.

San’nu tayi ma Auwal, ta b’aye shi, ya’ya mai jikin? “Da s’auki’ ya bata amsa, a takaice”, jikin ta ba kw’ari, ta isa gun g’adon, idon sa a lumshe”tamkar mai bacci” kan “white chair” da ke gefen g’ado ta z’auna, sai da aka kira sallah la’sar kafin ya m’ike ta basa “pure water”, yayi al’wala.

 Dake ” jikin sa da s’auki, “Alhamdulilah”, b’ayan ya d’awo daga sallah, ta basa abinci da aka k’awo musu yaci.

“Kw’anan uku, aka sallame su, duk w’ani hidima, “Auwal shi ya yi musu, har aka sallame su”.*****Kw’ana ki sun tafi, “Ammar ya daina gani fuska a gun Auta” ta d’aina shiga har kansa, duk ” Ammar ya fita a hayyacin sa, ya rame ga damuwa ta masa y’awa,” Auta ko bata ma san yana yi ba”.

       Yau take “friday” ta fito gidan” Aunty Mamu ta kai musu ziyara” tun tana napep ta lura da “wani mai jar m’ota, yana binsu a b’aya, har suka iso k’ofar gidan su, tana sallaman mai napep, zata shiga g’ida, sallama ya mata”Assalamu’alaikum c’ikin murya mai d’adi” k’amar ana busa sarewa ya mata sallama”, Auta kamar zata shiga g’ida amma s’anin muhimanci “sallama” yasa ta amsa ba t’are da ta juya ba, cikin salo da hikima, ya ke mata magana, wanda sai dayasa ta juyo, hira ya soma yi m’ata, tana yar dariya, sun d’ade agun sosai, sai da yama sallama zai tafi tana juyowa, “Ammar ta g’ani ido sa c’ike da kw’alla ” abun gw’ani tausayi,” Auta ko kalo sa bata yi ba, tabi g’efen sa ta wuce, hmmm nikam n’ace “Auta kar ki mana haka”.

          Soyayya ce mai k’arfi ta kulu tsakani Auta da Adam’s abun ba’a cewa k’omai, “Ammar ko ya d’awo “so silent” komai ya cakude masa, ga son Auta da ke barazana ga rayuwan sa”, abun sai Addu’a.

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button