An Yi Garkuwa Da Dan Uwan Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan
Maharan sun yi awon gaba da dan uwan tsohon shugaban kasar mai suna Jephthah Robert ne a gidansa da ke Yenagoa, hedikwatar jiharsa ta Bayelsa.
Har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton dai masu garkuwar ba su tuntubi iyalan Mista Jephthah Robert ba, wanda suka sace tun a ranar Litinin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da garkuwa da dan uwan na tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, amma ya ce rundunar na kokarin cafko bata-garin da suka sace shi.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da yadda aka yi garkuwa da dan uwan tsohon shugaban, amma Aminiya ta gano cewa a baya-bayan nan an samu karuwar matsalar garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a Jihar Bayelsa.
A ranar Litinin din da ta gabata masu garkuwa da mutane suka sako Kwamishinan Kasuwanci da Zuba Jari na jihar, Federal Otokito, bayan shafe kwana biyar a hannunsu.
Ana zargin gungun wasu masu haramtattun matatun mai a kauyensu ne suka yi garkuwa da shi saboda ya yi yunkurin dakatar da harkokinsu.
Daga Aminiya
[ad_2]