Labarai

Ban yi makaranta ba amma na kirkiri injin ban-ruwa mai amfani da hasken rana a Sokoto’

Ad

_____

Matashin mai suna Murtala Jaɓɓe Shuni ya Ƙirƙiro injin ban ruwan albasa mai amfani da hasken rana.

“Banyi karatun boko ba gaskiya amma dai-dai gwargwado duk abinda kakeso inai maka shi ko labarinsa ka bani,” Inji matashi Murtala

Ya hada injin da abubuwa kamar motor na fanka, bututun ruwa, danko, noti mai lamba goma da murafen kwalbar lemo.

Yace duka abubuwan da yayi amfani da su tsofaffi ne saboda bashi da hàlin sayan sababbi, Amma duk da haka zai kai shekara guda bai lalace ba.

Abinda ya ja hankalin sa ya ƙera wannan injin, shi ne ganin yadda ‘yan uwan sa suke wahala wurin tafiyar da harkokin su na noman albasa.

Ya Ƙirƙiri wannan injin ne don saukakawa mutane wurin tafiyar da harkokin su na noman albasa, yanzu da batir din babur ko mota sai mutum yayi ban ruwa a gonar sa.

“Alhamdulillah wadannan abubuwan sun kawo sauki a cikin rayuwar mu, ba mu gani ga ‘yan uwan mu, bamu gani ga abokan mu kuma ba ma ganin kyashin kai ka samu mu ba mu samu ba. Alhamdulillah muna samu har mu bawa wasu, da wannan sanaar na yi gida nake sutura har na ciyar da iyali na .” Cewar Murtala.

Daga Labarunhausa.com

 

 

Ad

 

 

 

               

Ad

_____

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button