AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????????????????????
???? AUREN WATA SHIDDA????
Story & written
By mmn
Fareesa
GODIYA… godiya ta tabbata ga ALLAH (S W T) tsira da amincin ALLAH su tabbata ga annabi (S A W) da ahlayensa d sahabbansa .
GARGADI…banyarda wani ko wata yajuyamun novel ta kowacce sigaba.in kunne yaji ,jiki ya tsira..
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
P1
Not edited
Kyawawan Yan mata ne guda3 ketafiya anutse.suna fira ko waccensu hannunta rik’e da tulu da alama d’ibar ruwa zasu..
Mitsss wadda ake Kira mero acikinsu taja tsaki “sakamakon hango dabar samarin karkarar tasu datayi”hade da cewa Ni wlh banison bi tanan haryar,sbd yarima HAMZA da abokansa kunsan ba mutumin kirkibane bbu abinda ya aje sai yima Yan mata da zawara FYAD’E Kuma mai gari yasani amma ya k’yalesa…yo har matan auren bebariba wlh cewar indo”yyinda RIYANATU dake gefe batace komaiba.”
K’arasowarsu gab dasu yarima HAMZA yasasu yin shiru hade da yin sauri Dan suwuce lfy”Dan beda mutunci.
Yarima kuwa Yana atsakkiyarsu Yana isa da gadarar shi. Wai shi Dan boko Kuma D’an me gari,sbd duk k’auyen acikin samari bbu Wanda yakaisa ilimin boko da wayewa dg shi sai GALI..tun dg nesa idonsa yasauka kan riyanatu dake tafiya cikin nutsuwa da sanyin hali hade da kamun Kai”
..bbu bata lokaci yasaka yaronsa guda yatsaidata..
Yan mata yarima HAMZA na mgn ! yafad’a yana nuna riyanatu dake tafiya bata ko kallesaba,yyinda su indo jikinsu ke kakkarwa sbd tsoro suna kallon riyanatu datak’i tsayaawa…yaron yyi saurin tare gabanta…wata doguwar tsuka taja hade da aikomasa da harara ta wuce abinta… kallon mamaki su indo suka bita dashi , yyinda yaron yanufi gun yarima HAMZA Dan sanar masa.
Tun kafin yyi mgn yarima yad'aga Masa hannu alamar beson ji sbd duk abinda riyanatu tayi akan idonsa..
Lumshe ido yyi Yana mugun mamakin wannan yarinyar Yar uban waye ce agarin nan be?" kamarshi yasa atsaida ita tak'i tsayawa sbd ita t isa...mittsss yaja tsaki hade da mik'ewa tsaye da nufin tafiya, yyinda yaransa suka tashi ,ya girgiza Masu kai . alamar beson abisa...salisu abokinsa dake gefe yace Kai gsky yarinyar can Yar renin wayoce wlh lallai mutumin batasanka bane shiyasa...wani munafikin murmushi yarima yyi hade da cewa hmmm yau kau zata sanni Dan wlh yau din nan sai na rabata da darajarta Dan agarin nan bbu macen data isa tamun haka ...bejira amsarsaba da sauran abokansa daketa mgn yabi bayansu riyanatu..
Bangarensu riyanatu kuwa suna barin Gurin su indo suka kama mata fad’a kan miyasa tayi hakan?”bacin tasan ko waye yarima da mugun halinsa Amma hartayi wannan abin.,,,,
Cikin dakiya tace be isa yamun abinda ALLAH bemunba bana tsoronsa ko kad’an Dan haka kubar maganar.
“Mairo tace inda zakiji riyanatu kije kibasa hakuri sbd gudun abinda zaije yafaru Dan ALLAH”
Murmushi riyanatu tayi mai sauti tace hmmm mairo kenan bbu inda zani balle har nabasa hakuri Dan banmasa laifi ba”indo tace Amma dakin sani baki k’i tsyawa…aitariga ta makara tunda har ta rigada tayi mun haka nikuawa ayau Zaki gane bakida wayo ko ke Yar uban waye agarin nan…cewar yarima a hassale cikin fushi”
Gaba d’aya suka juya banda riyanatu suna kallon sa…cikin bacin rai riyanatu tace dakata mlm kada kasake hadawa da iyayena ,ubanah na kabarinsa dan ha…..saukar Marin dataji yasakata yin shiru tana kallonsa” nunata yyi da yatsa hade da cewa lallai yarinya bakinki yajamiki ke har kin isa Ina mgn ki mayarmun to wlh yau saikinyi nadamar haihuwarki a k’auyen nan fuuuuu ya wuce abinsa… yyinda riyanatu dake rik’e da kunci tana kuka hawaye ya wanke mata fuska,nan su indo suka ba ta hkr hade da cewa data sani ta tsaya Allah yasa kada yyimata mugun Abu Dan sun tsorata da kalaminshi ,Amma ita bbu hakan atare da ita.
Byn sun gama d’ibar ruwan ko wacce ta wuce gidansu jiki asanyaye.
Riyanatu kuwa ko afuska bata nuna ma umma komaiba,Amma Abu daya yatsaya mata arai ,shine sai kinyi danasanin haihuwarki agarinan yau…,byn ta aje ruwan,” nan tashiga hidimar aza girkin dare Wanda da k’yar umman tahada kudin akasiyo abin bukata sudafa sbd basu dashi.
Sai gab da magrib ta ida tuwan ta gyara Gurin tayi alwarlal magrib ta nufi daki ta data Sallah”
Itama umma alwarlal ta Fara tana Duke taji anyi sallama”ta d’ago tana amsa fuska asake sbd ganin gali D’an aminiyarta ,saidai jikinta yyi sanyi ganin arikice yashigo gidan
Ko gaisawa basuyiba arude yace umma Ina riyanatu?”
“Da sauri tace lfy dai ki?”
Arikice yace bbu umma ,Dan ALLAH duk yadda zaayi cikin 2 kuyi guda ko kubar garin nan ko kada ku kwana agidan nan…
Cikin kosawa umma tace dan ALLAH kamun bayani mana! Sbd mezamubar gd?”
“Gali yace sbd yarima HAMZA nason yaketawa riyanatu haddin ta”
Inna lilahi wa Inna ilaihir Raju un” umma ta fad’a tana kuka,hade da cewa akan wane dalili,ko kuwa hakanan sbd zalinci anganta arainiya ko??”
Cikin tausayinsu gali yashiga sanar da ita komai kasan cewar agabansa yarima HAMZA yyi maganar,Amma be nuna yasan riyanatu ba kuma( Yana sonta be nuna mata)hakan yasa hankalinsa tashi sbd yasan yarima mugun busurune…
Sannan yyi ajiyar zuciya yace umma ga shawara ..adedenan riyanatu ta fito dg daki da alamar ta idar da sallar ta nufosu tana kuka..
Da sauri umma taceinajinka”
Yace muje gidanmu ku kwana scan kafin da asuba kubar garin sbd wlh kinsan zai iyayin komai akanku sbd ubansa bazaice Masa komaiba “
Umma da riyanatu na kuka suka kwashe kayan sawarsu agana,da abinda suke bukata suka saka a buhu ,Saida akashiga sallar isha’i sannan suka kwashe kayan su ,sukabar ledar k’asa d katifa suka rufe gida hade da nufar gidan Inna mariya mahaifiyar gali,yyinda uma gabanta ke faduwa svd batason wane gari zasu ?”kauye ko birni?”Dan xuwarta bunni guda alokacin yayarta nacan to yaxu Kuma batasan Ina yayarta takeba ta mutu ko tana raye..
Da wannan tunanin aran umma,suka iso gidan Inna mariya, yyinda riyanatu keta kuka da adduar ALLAH yakubutar da ita dg sharrin yarima.
Byn zuwansu gidan gali ya ma inna bayani ,salati tayi sbd ta tsorata. ta kalli umma tace ki kwantar da hankalinki bintu insha ALLAH zaku kub’uta sbd inaji ajiki na barinku garin nan alkhairi ne babba,Zan Kira wata zuwaira inada number ta agarin kaduna take can zakuje insha ALLAH zata baku masauki ta nuna muku gari Dan gaskiya nabaki goyan bayan kubar garin nan sbd martabar y’ar ki guda aduniya tak…
Ajiyar zuciya umma tayi tace to nagode sosai ALLAH yabiya.
Inna tace amin byn komai yalafa zan je nasanar da baffan riyanatu, sannan akwai kudi gurunku?”
Umma tace eh a”akwai dubu ukku”
Inna tace zanbaki dubu5 ,kukara sbd ai Sanaa Zaki samu acan harki maida riyanatu makaranta ko?”
Umma tace eh nagode mariya,Amma akwai busashena zasuyi kudi mai kauri kisiyarmun gali yakaimun kudin “inna tace to,yyinda riyanatu keta kallon su tana tunanin zasubar garinsu zuwa wani gari sbd wani banxa Allah yasa hakan shiyafi alkhairi…
Nan Inna ta sa gali ya Kira mata ita da wayarsa.
Bbu bata lokaci Inna ta amsa tayiwa zuwaira mai abinci bayanin zuwansu riyanatu d mahaifiyar ta , tace ALLAH yaka wosu lfy.
Nan Inna ta musu kwatance insun iso garin yadda zasu gane..
Shikuwa gali yaso yaja riyanatu yafad’a mata sirrin zuciyarsa kafin su tafi amma ganin su Inna sai yafasa.
Washe gari tunda asalati su umma sukayi ban kwana da mariya,gali yadaukar musu wasu dg cikin kayansu,yyi musu rakkiya sbd duk ana masallaci bbu Wanda yagansu ,dukda atsorace suke.
Be barsuba Saida suka yi tfiya mai nisa har suka iso titi suka hau acaba sannan yajuya yafafi cike d kewar su hade d tausayinsu..alokacin har gari yafara haske…
Bangaren yarima HAMZA kuwa da misalin karfe 2:00 am yanufi gidansu riyanatu da yaronsa da yasaka yabinciko Masa gdn su.
Suna zuwa….????????
Yawan comments yawan typing.
Share pls
BY MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
???? AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written
By mmn fareesa
Not edited
Dedicate to my lovely sister hauwau u lado????????