AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru Abdallah yyi yanajin dogon sharhin mom harta Kai aya azancenta”

Tamkar zai fashe sbd bacin rai ,sbd ganin Wai kamarshi zaa tsorata wata can akan tace tana sonsa Wai ta auresa ,Kuma Wai duk arasama wadda zaa ce a aura Masa sai wannan vileger girl d’in k’aramar yarinya mittsss yaja tsaki afili….

Azabure mom tace nikakewa tsaki abdallah?”

Da sauri yace ah ah mom tunanin zuci nake kiyi hkri pls”

Shiru tayi tana mamakin halinsa, sannan ta ce yanxun kaje gun abbanka ka gaidashi sannan ka koma part naka ka turomun wannan yarinyar….

To”yafad’a atakaice, sannan ya fice dg parlourn.

Koda ya shige part d’in abban,samunsa yyi zai fito ya shirya da alama fita zaiyi,fadawa jikinsa yyi tamkar yaro yasaki kuka.,,,

Da sauri Abba yace yah Salam”

My son gayamun damuwarka kaji ?”

Ahankali yace gsky Abba Ni banson auren nan Dan ALLAH ku barni… ajiyar zuciya Abba yyi hade da cewa to shikenan tunda kafison in kunyata agaban babban mutum irin yallabai yadauki mahaifinka mak’aryaci Abdallah na fasa yimaka auren…bazanso sakaka adamuwaba” saidai matsalar mominka da k’yar zata….Abba na amince kayi hakuri Dan ALLAH insha ALLAH zankasance mai biyayya agareku.

Murmushi Abba yyi yace yauwa yaron Abba ko kaifa ,ka daure sbd nasan Kai jarimine insha ALLAH inaji ajikina akwai wani babban al’a mari mai kyau ko akasin haka da zai faru nan gaba , sannan wannan auren na sirrine bazayi shagaliba sbd gudun kada agane sai yanzun zakayi aure nafison aganka d matar ranar bikin bud’e campanin insha ALLAH sbd baniso mai girma president yaji lbarin bikin ,inhar sun amince iyayanta zasu baka ita,to da’a d’aura aure washe gari ta tare bbu wata bidia ko al’ada daza ayi.

Sannan apart naka dake gdn nan zaku zauna,ka fahimta?”

ak’agare Abdallah yace eh sbd yadda yakejin zafin maganar auren…. sannan yajanye jikinsa dg na Abba had’e da cewa to Abba sai kadawo, yafad’a had’e da saurin varin Gurin…

Azuciye ya isa part nasa,yasami riyanatu zaune kan carpet tana kallon indiyan firm a receiver”ke kije inji mom…..batamasan ya shigowa b.

Atsawace yace keee eeee!wawiyar inace?” anamiki mgn, atsorace ta juyo sukayi 4 eyes wata uwar harara ya aiko mata da ita had’e da Jan doguwar tsuka,yace kije momna kiranki , sannan kada ki koma yimun kallo a parlou”kinji ko bakijiba?” Yafad’a atsawace….

Jiki na kirma tace naji, had’e da saurin fita t nufi part d’in mom…

Zaune tasami mom itada aminiyar hjy ikilima wato mahaifiyar zeenat, sallama riyanatu tayi gabanta na mugun faduwa sbd tana mugun jin tsoron mom had’e da shakkarta.

Sama d qasa suka kalleta hjy ikilima ta tabe baki .sannan mom taja tsaki hade da hararan riyanatu dake gaidasu tace ki rik’e gaisuwarki.

Tuni mom ta Fara mgn kamar haka ,dalilin kiranki shine inason saki wani aiki mai hadari saidai zanmki GARGADI 2 na farko kiyi shiru kada ki fadawa kowa na biyu dole ki amince ko kuwa duniyar ta gagareki Zama….zaro ido riyanatu tayi cikinta yyi k’ara k’uuuuuuuuuuu tuni xufa tafara keto Mata…. murmushn samun nassara mom tayi sannan ta zayyane wa riyanatu k’udirinta akan son ta auri Abdallah Kuma AUREN WATA SHIDDA….

Cikin tsoro riyanatu tace Dan ALLAH hjy kirufamun asiri wlh tsoronsa nake ……rufemin baki ai na Masa mgn bbu abinda zai Miki sbd shi mgn Bata sha Masa kaiba saiki kiyaye kada kimasa kuskure akwai dalili shiyasa Zaki auresa inba hakaba ai ke ko darajar matar direbansa Baki kaiba.

daga k’arshe gobe zaa je gdnku gun ummanki neman aurenki inta amince ta fad’a musu suje gun iyayanki maza abasu aurenki.

Sannan inaso ki nunama ummnki kinason Abdallah Kuma soyayya kuke dashi….

Cikin tsoro riyanatu tace Amma Dan ALLAH kada kimun komai sannan da way shidda yyi zai sakeni?”

Harararta mom tayi tace eh bbu ragi bbu k’ari ,saiki tafi ko!kin wani kama kallonku d k’wala kwalan idanunki….

Jiki asanyaye Riyanatu ta fice ta na mamakin meke Shirin faruwa d rayuwarsu itada ummanta be?”

Tasan in bata amsaba to komai mom zata iya yimata sbd tunda taji maganarsu rannan ta yarda hjy batada Imani.

Da haka ta koma part d’in Abdallah,tasamu bayan nan,haka ta zauna tana tunani har 12 tayi,saiga wani yyi knock ta bud’e nan yasanar da ita shine zai rik’a koya Mata turanci .
Babu musu ta bisa alambun gdn yafara koyar da ita.
Cikin ikon ALLAH kafin su tashi riyanatu ta iya wasu abubuwa,shi kansa malamin yyi mamakin k’wak’walwarta….

Byn sun tashi dg islamiya ta koma gd ,duk jikinta asanyaye Fatima na lura da ita,harta tambayeta Amma sai tace bbu koma.


Washe gari Gurin karfe 2:30pm su umma na zaune atsakar gd suna fira yyinda mutane na zuwa siyan abinci…wani yaro yashigo yace Wai ance ana son mgn da umman riyanatu inji wani mutum….

Da mamaki zuwaira tace to kace tana zuwa.

Byn fitar yaron ,umma tacewa mama zuwaira tayi hkri ita bazata b sbd batasan kowa agarinba.

Murmushi zuwaira tayi sannan ta saaka hijab ta fice waje…..tafi minti12 sannan ta dawo tana murmushi ta kalli umma tace kisaka hijab naki muje soro bara na shimfad’a ta barma bak’i mukayi sunxo mgn da kene akan dansu nason riyanatu….

Umma tace….

Share pls

BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????

???? AUREN WATA SHIDDA????

????????????????????????????????????????

Story & written by
mmn fareesa

Wannan shafin nakune
Queen
Fatimatou
Mmn Bilkisu
Sury baby
Bilkisu Auwal
Zee hamis wada
Queen mimi
Inajindadin comments naku sosai love u wujiga wujiga????????????????

p11

Umma tace anya kuwa da gaskene?”
Murmushi zuwaira tayi tace muje Dan ALLAH!ta fad’a had’e da daukar tabarma ta nufi soro….
Umma ma tasaka hijab tabi bayanta ranta fal da tunani”
sallama tayi had’e da Zama kusada zuwaira” byn gama gaisawa,alh bukar yyi gyaran murya had’e da cewa to nasandai zakuyi mamakin ganina a wannan lokaci,suna Alh Abubakar da’aki sani da alh buka .nasan kunsan ALH KABIR GIRMA ko?”suka d’aga Kai” sannan yacigaba da cewa ni amininsane yaturoni akan neman iziniku akan zaya turo a nema ma D’ansa auren y’ar ku,wato RIYANATU dake ma D’ansa aiki,wato ABDALLAH dg nan suka Fara soyayya d juna ….
Cikin mamaki umma tace oh D’an yau kenan dama ba aiki takemasa ba soyayya suke?”
Murmushi alh bukar yyi hade da cewa kunsan halin Yara insunason Abu to shine ai Abdallah ya matsa ayimusu aure saita cigaba da karatunta acan insha ALLAH,amma yanxun miye amsar ku?” Umma tayi ajiyar zuciya had’e da cewa da farko dai sai naji ta bakinta intana sonsa sannan muyi binkice akansa d iyayensa tukum saina turaku gun dangin mahaifinta dake k’auyen…

 Tashi alh bukar yyi hade da yimusu godiya sannan ya ajiye musu rafa guda ta 1K ya fice Yana cewa ah ah su karb'a sbd jin umma na cewa yabar kud'insa...

byn fitar sa,su umma suka shiga cikin gd”mama zuwaira nata murmushi tace oh ikon ALLAH Ashe alkhairi ne ya maidoku garin nan,ai dama matar mutum kabarinsa ALLAH yasa hakan shiyafi alkhairi.
Umma tace ameen, Amma nifa gsky inajin tsoron ta auresa mufa talakawane gara dai ta auri talaka daidai mu. Kuma bamusan halinsaba….ah ah bintu addua yaka Mata kiyi, maganar hali Kuma gsky dukda ba Wai hudda nikedasu ba to Alh Kabir girma Yana mutunci sosai akwai temakon talakawa wlh ga yadda naji ,Kuma shi Abdallah bama nan yyi karatu ba ,bedade d dawowaba ,Amma inbaki yardaba bara nasaka harira dake hudd’a su dakuma salisu mak’ocinmu dake dreban gdn su Miki binkice akansu..
Ajiyar zuciya umma tayi tace ai bama wannan ba ,sai tazo naji abakinta tukum kinsan Dan yau ,kahaifesa baka haifi halinsaba.
Zuwaira tace hakane tana dariya , yyinda Fatima dake sauraronsu tanad’aki taita murmushi tana tuna yau zata tsokani Riyanatu….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button