AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kamar yadda ta Saba haka ta gyare ko Ina “sannan ta had’a Masa ruwan wanka kafin ta fito a parlou tayi jiran fitowarsa .
Shiru tayi tana tunanin kada Abdallah yyi zaton sbd taja hankalinsa tayi kwalli haka !Kai kodai ta gogene…salamu alaikum, sallamar Hafiz ta katse Mata tunani… murmushi tayi had’e da amsawa suka gaisa, sannan tace oh Yaya hafis kwana2 nabar ganinka”y’ar dariya yyi yace wlh RIYAN kinsan bikina yakusa befi 10 days ba shiyasa naje Kuma kano sbd ammi na anmata transfer a hospital tadawo anan garin da aiki ,jiya muka sauka,shine nazo gun ogan naki nakawo gaisuwa sbd jiya naga 2miss call nasa,nakira be d’agaba nasan fushi yyi.tabe Baki riyanatu tayi had’e da cewa to ALLAH yasa alkhairi”
Yyi saurin cewa amin,Zama yyi Yana murmushi sbd ganin kyawun datayi har cikin ransa yanama abokinsa fatan mallakarta har abada.”
Ahankali tace to a Ina amaryar tamu takene?”murmushi yyi yace y’ar nan garince ai,Kuma nan zamu zauna duk fg Ni har ammina aiki yakamu nan garin. “ajiyar zuciya tayi had’e da cewa to ai yanxun ka Zama Dan gari ai.
Kofar bed room d’in yakalla sannan yace hakane,amma zakije bikina ko ,ma’ana kiyi attending d’in duk event na bikin?”
Kafin tayi mgn Abdallah ya murd’a kofar yashigo parlourn…tuni k’amshinsa ya mamaye parlourn”fuska murtuk ya gallawa hafis harara had’e da cewa parrot kazo ka cikawa mutane parlour da mgn ” yafad’a had’e da Zama gefen hafis dake dariya”
Ahankali tace barka da fitowa!
dagowa yyi sukayi 4eyes…k’uri yyimata sbd son gano shin itace ko ba ita bace sbd yadda tayi kyau na ban mamaki…yanxun zakayi break ne?”muryarta ta katse masa tunani,saurin barin kalleta yyi cike d basarwa ,yawani yamutsa fuska tamkar yaga abin k’ii yace eh akan labb’ansa…
Hafis da tunda yaga Abdallah yad’ago zai kalleta yakafesa d ido… murmushi kawai yake mai sauti,”ahankali yace AK dakai fa take yakamata kadawo hayyacinka… mittsss Abdallah ya ja doguwar tsuka had’e da cewa dallah mlm miye haka?”kamar ya nadawo hayyavina ,daba a hayyacina nakeba ko me??””
nidai bance hakaba maida wukar…cewar Hafiz Yana dariya.
Yyinda riyanatu ke saurarensu Amma Bata kallonsu.

Keeeee! Kije ki kamun break kinyiwa mutane wani zaune sai kace kina gaban sa’anninki.. mitttsss yaja tsaki hade da makawa Hafiz harara ganin zaiyi mgn.

Ahankali ta tashi ta fice”

Hafiz yace haba mutumin kana yadda kakeso wlh wannan iko haka ai kabari abiya sadakin ko, sannan da alama wannan kwalliyar tata ,tatafi d imaninka….stop it !inkasan wannan surutun yakawoka guna zaka iya tafiya “wato namalura sokake da gske na auri wannan yarinyar ko?”

Hmmm friend kenan abar maganar kawai,dama naga Miss call naka jiya ,nakira kak’i dagawa sorry kasan jiya muka dawo tare d ammi bana kusa da wayar , sannan my feedo ta dameni da rigima tanason kuje kuga k’awayenta abasu abinda zaa basu ,kasan in tanamun wannan rigimar wlh jinake tamkar nacika aiki kaima ka gane?”yafad’a Yana daga gira had’e da murmushi,tsaki abdallah yaja had’e da cewa aikin banza jarababbe ai garadai da ammi zata maka aure wlh, sannan batun ganin k’awayenta zamu iya zuwa Amma kasan banason surutu da hayaniya Mata 2 sun isa muyi mgn da su…. murmushi Hafiz yyi had’e da cewa relax Mana ai nafad’a musu anbadakai???? dud da nasan abokin nawa da farin jini dole wata ta k’yasa, shiyasa nafison kuje da babynka RIYAN kawai “itama nafad’a Mata tare zuje takuma amince….

Iya k’uluwa Abdallah ya k’ulu da iskancin da Hafiz ke Masa”murmushn takaici yyi Yana kokarin mgn… riyanatu tayi sallama had’e da ajiye musu tray din a gabansu “

Kok’arin had’ama Abdallah tea takeyi ,yyi saurin dakatar da ita ,cikin mugun tsare gd yace ke wakikayiwa kwalliya?”

Mamaki sosae tayi da tambayar sa, azuciyarta tace zanyi maganinka kuwa….

“Ko bakya jine?”

da sauri tace saurayina nayiwa!Wanda in Zan aura in mun rabu!

atsawace yace keee nikike gayawa saurayinki?”hhhhhhh yyi dariyar rainin hankalin sannan yadubeta off & down yace ai Ni banga wani Abu ajikinki da wani zai gani har ya burgesaba and last nakoma Miki mgn ko tambaya kina bani amsa agadarance Zan nunamiki ainahin calour d’ina….

Bata ce komai ba “tea din ta mik’a Masa hade plate datayi serving nasa , sannan ta fice dg parlourn Dan tajira awaje su gama.

Hafiz ya girgiza Kai beyi mgn ba,saidai yasha alwashin duk ranar da Abdallah yakamu dason riyanatu bazai taimakesa akan yashawo kantaba Kuma zai gayamasa managar dayake so son ransa…

#

Abdallah sunje da sauran friends nasu sunga k’awayen fiddausi(feedo)sun basu abinda suka bukata ,acewar Abdallah ai in suntaya akan abinda suka bukata sunyi k’aranta ,da kud’insa yabasu.
Yyinda duk yawancin Yan matan sun rude da ganin Abdallah duk da sun lura yanada Shan k’amshi had’e da izzah”

Shire Shire kawai ake duka b’angaren 2 Dana Abdallah Dana Hafiz, yyinda Abdallah iyayensa sun je kauye antsaida mgn akan Nanda sati3 za’ayi bikin, sannan riyanatu umma tace ta Dena aiki yau kwanta 3 rabon ta da gdn,mom ta tura harira taji ko lfy”
Sai umma tace lfy lau ta Dena ne in ALLAH yasa tazama matarsa ta Masa komai..
Tabe baki mom tayi dataji bayanin umma gun harira, azuciyarta tace hmmm danbakisan auren yarjejeniya bane shiyasa….

Ayau yakama laraba Kuma yau ake arebiant night nasu hafis,ga Abdallah ne babban abokin ango , sannan Hafiz yace inhar bada RIYAN zashiba to baya bukatar sa ,da farko yyi fushi yace eh bazashiba tunda Saida ita.
amma dayayi tunanin yadda yakeda Hafiz saiyaji bazai iyaba gashi besan gdnsu RIYAN ba.

Wata arebiant gown ce me masifar kyau da tsada yasiya yakira ya’u direba, kasancewar yasan gdn sbd ganin Yana maida ita gd.

Yabasa yace yabata ,Kuma yasanar da ita anjima Gurin 5:00 pm zaizo ta shirya tasaka wannan rigai…,,,

Zaune take tana tunanin wannan k’addararran aure da za’amata” umma ta shigo dakin had’e da kallon ta tace kije soro kinada bak’o Abdallah ya aikosa…..

“Wani mugun faduwa gaban ta yyi sbd jin ankira Abdallah”

Cike da mamakin Wai ya aiko wani ta fice zuwa soro.

byn sun gaisa da ya’u direba ,ya mik’o Mata ledar had’e da sanar da ita abinda Abdallah yace….

Cikin k’arfin hali tace to shikenan, sannan sukayi sallama.

Tunani take to Ina zasu insun saka kayan be?” Itafa gsky tanajin tsoro k…har bakon yatafi?” cewar umma dake dubanta.

Murmushi ta k’akaro had’e da cewa eh wlh Wai kayane ya aiko zaizo da karfe5 nasaka zamuje anguwa…

Umma tace to ALLAH yakawosa lfy kidai kula da kanki dukda ansa muku Rana ni banson yawan nan bbu aure atsakani…

da misalin karfe 4:30 riyanatu ta gama Shirin ta ,sbd gudun masifar Abdallah kada yazo bata shiryaba.

Masha ALLAH tayi masifar kyau tamkar balarabiyar abinka da bafulatana.”
Sai kamshi ketashi ajikinta,byn ta gama shiryawa ta zauna jiran zuwan sa…

Batafi minti12 ba da Zama yaro yashigo da sallama Wai wasu masu motoci sunce RIYAN tazo…

Tana dg cikin daki ta juyo…umma ta k’walo Mata Kira had’e da cewa ta fito.

mama zuwaira ta dubeta tace Masha ALLAH y’ata kinyi kyau”toshi sirikin namu bazai shigo yagaidamuba”

Cikin kak’aro murmushi tace uhmmm mama kunyafa yakeji”umma tace Ni kaina bana ma son yazo wlh… murmushi mama zuwaira ta yi tace oh bintu kunyarku ta Fulani na nan ajininki.

Kallon su riyanatu tayi had’e da cewa bara naje naji ina zamuje ne Wai.

To sukace sannan ta fice……

Yawan comments yawan typing ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button