AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Acikin hole d’in kuwa sai hayaniya ke tashi da suruttai da yawa nata yiwa zeenat dariya da irin tozarcin da Abdallah yyi Mata suna cewa ALLAH ya k’ara da ya tsink’ata aiyafi dacewa da wadda yazo…
Cike da jin kunya had’e da k’unar rai, zeenat tabar gurin”
Hafiz kuwa girgiza Kai yyi cike da tausayin abokin nasa yace ALLAH shi kyauta.,,,,,,
********
Kuka kawai Riyanatu ke yi,tana danasanin yadda da wannan aure”gashi anata ci Mata mutunci harda cewa za’a kasheta…. dallah malama rufemin baki ,matsora ciyar banza miyasa kika nuna kinajin tsoronta?”Koda k’wanji kuka gwada da ita me zata iya yimki?” Mittsss yaja tsaki hade da rufe idonsa…
Shiru riyanatu tayi tana tunanin magan ganunsa “tabbas bazata sake nunawa zeenat tsoroba tunda ta lura ba son zeenat d’in yakeba mom ce ta tura mishi ita,Kuma tana k’yaleta ne sbd masifar mom da Abdallah…inbaza ki fitaba mumutafi kin yi wani shiru kina tunani” cewar Abdallah yana yatsina fuska….da sauri ta yi ajiyar zuciya had’e da cewa dakai da ita duk banyafe muku ba ,tayi saurin fita dg motar sbd sauri harta mance pos d’in ta.
Cike da mamakin ta Abdallah yace afili lallai yarinyar nan kin gama rainani wlh ,zankuwa yimiki mugunta son Raina saikiji dadin cewa Baki yafeba…
#
b’angaren zeenat kuwa cikin bak’in ciki ta isa gd.ko parking batayi daidai ba ,ta fice ta shiga parlourn mominta hjy ikilima tana kuka mai sauti…afirgice hjy ikilima ta mik’e tayo kanta had’e da rungume ta,tana cewa lfy auta na ? wanene yabata Miki rai ?”shima nasa yab’aci… ABDALLAH Mana !ta fad’a cikin kuka.
Hjy ikilima tace hmmm narasa miyasa kika mak’alewa matsiyacin yaron nan?”shin dolene kibarsu Mana! dashi da hjy hafsatu wlh zasu gane banida mutunci…..Wai momy daga fa naje gdnsu nemansa sai mom tacemun Yana Gurin party na hafis friend d’in sa,tace naje can nabisa tayima zaton yasanar da ni,nace ah ah,saitamun kwatance.
naje nasameshi da y’ar iskar yarinyar nan…..ta sanar da ita komai….
Whattttttttt?” kina nufin sbd ita yamareki shi Dan iska to wlh yadobo ruwan dafa kansa saina dauki mummunan mataki akansa sbd duk Wanda yaci tuwo Dani miya yasha ,Kuma kema sai kinje da bakinki kin gaya Masa mgn komai Daren dadewa ai hafsatu shashasha ce “iza mai kantu ruwa Zan Mata wlh ,kadama ki sake ki nuna Mata abinda yafaru,kinajina?”
Cikin jin dad’i zeenat tace to momi.,,,,,,,,
????????????????
Masha ALLAH anyi dinner d’in Hafiz lfy inda uban gayyar yaje Amma banda riyanatu”Hafiz kuwa beji dad’i ba..
Washe gari aka d’aura auren sa da fiddausi Ahmed…. Abdallah ya wanku tamkar shine angon,haka akayi hidima lfy akagama lfy , amarya ta tare ad’akinta sai muce ALLAH yabada zaman lfy……
Kamar yadda Abdallah yyi alkawari azuciyarsa zai siyawa su riyanatu gd.cikin ikon ALLAH yacika “komai anxuba aciki d’aki,2 ne sai sitting room d kicin bbu laifi komai yyi daidai mai rufin asiri , sannan yaje da ya’u direba gdnsu RIYAN,sai akayi rashin saa da umma da riyanatu basanan suna wajen sunan k’anwar zuwaira,Kuma atime d’in zuwaira ta shirya itama zata tafi can,ta tsayane sbd masu siyan abinci ,shine tace su umma suyi gaba.
Cikin mutunci d girmamawa suka gaisa da Abdallah sannan ya bata takardar gd yakuma sanar da ita gobe ya’u direba zaizo yakaisu riyanatu gdn,nan zuwaira tayi ta Masa godiya da saka Masa albarka….
Lokacin da su umma sukaji labari tayi murna da godiya ta kumaji dadin zuwansa Bata nan sbd ita Wai kunya. Riyanatu ma taji dad’i sosai saidai fargabanta Yaya umma da dangin mahaifinta zasuji insunji bayan wata shidda Abdallah yasaketa inya aureta?”””
Zaune mom take tana tunanin maganar dasukayi da hjy ikilima jiya... Abdallah ya shigo ya aza kansa akan cinyarta yana wani shagwabe fuska... murmushi tayi tace oh my son me Kuma yafaru ne?"
Kallonta yyi yace gsky mom ni gyaran da akayi bemunba kinsan ba d’aki d’aya zamu zauna da itaba gsky”
Yo dama ai dakinta daban na Gefen naka ko?” Ok mom”
yauwa my son abinda nikeso dakai kaga yau sauka 12 days auren nan Kuma da anyisa da 2days za’ayi bikin bud’e campanin ka.
Cikin k’osawa yace eh”tace yauwa to kada ka yadda in yarinyar nan ta zo wani Abu yashiga tsakaninku da ita ..maana kada ka kusanceta….b’ata fuska yyi hade d cewa habamom! ALLAH ya kiyaye nayi….saikuma yyi shiru cike da jin kunya yana sosa kai” murmushi mom tayi sbd tasan duk miskilancin sa akwai kunya.
Canza topic d’in yyi da cewa yauwa momi kin sanar da su Uncle Suraj kuwa d hajjo ne(mahaifiyar momi) had’e rai tayi had’e da cewa ah ah sbd kasan acikin sirri za’ayi auren ko?”amma su mom ai baidace ace basu saniba tunda shak’ikankine kum….rufemin baki nace bazasu jiba!shiru Abdallah yyi Yana tunanin kan mom d’aya kuwa..muryarta ta katse Masa tunani gun cewa ada nace bazayi lefeba to sai nayi tunanin hakan xaisa agane koba sonta”to yanzun na karb’i kud’i gun abbanka anmata set6 na trolley, bbu laifi ansaka kaya masu tsada kala40 ne andinka 20 .sai dogayen riguna sun isheta sakawa har ku rabu” gobe nema zanbawa hjy ikilima da harira sukaimusu da 50K tayi kunshi ….cikin k’osawa yace hakan yyi had’e da tashi yace mom saina dawo”adawo lfy my son,yace amin had’e da ficewa…
Riyanatu zaune a parlourn su tana kallo tunani take na wannan aure gashi ita rabonta da Abdallah tun ranar da sukaje Gurin arebiant night tamasa rashin kunya k’ila be mantaba yarik’e abun intazo gdnsa yahukuntata…yauwa riyanatu naceba gsky inkinyi aure Zan cewa baffanki ya maidomin bilkisu sbd bbu Dadi Zama ni kadai gsky.
Murmushi tayi had’e da cewa hakane umma,Zama tayi had’e da cewa gsky bbu abinda zancewa yaron nan sai ALLAH yasa yagama da duniya lfy Dan ALLAH kimasa biyayya riyanatu kina gani yasiya mana ya zuba komai na bukata hardasu kayan abinci da fridge gashi inayin sana’a komai yimuke bamu neman taimakon kowa sai ALLAH!
Murmushi riyanatu tayi had’e da cewa hakane umma ,Kuma Kinga yace agdnsu zamu zauna kafin yagama namu Kuma be bukatar akaini da komai sai kayan sawa”umma tace eh haka alh bukar yafad’awa dangin babanki yaudai saura kwana 13 ALLAH yasa alkhairi yakaimu lokacin ameen,Amma Wai lfy naga ko sau d’aya baya zuwa fira gunki?” cikin dakiya hade da lalibo abinda zata fad’a tace
Lfy lau umma yyi tafiyane gashi bbu waya guna balle na kirasa, amma yace inyadawo zai siyamun waya.
ALLAH ya maidosa lfy ,tace ameen.
byn kwana 10
Abdallah na part d’in sa agefen inda yake motsa jiki,Hafiz ya shigo kamar anje hosa yyi wuri wuri dashi.
kallon sa Abdallah yyi had’e da cewa my man lfy dai ko?”
naga kamar baka lfy ko kuwa angoncin ne yazo da haka?”
Ajiyar zuciya Hafiz yyi had’e da cewa hmmm inafa lfy?”
Fiddausi tunda aka kamun ita Sam tak’i yarda Dani!
Hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh????????
Harda rik’e ciki Abdallah sbd dariya bakuma k’amin kyau tamsaba”yyinda Hafiz ya k’ulu iya k’uluwa da iskancin Abdallah.
Abdallah Saida yatsagai ta da dariyar sa tukum yace haba mazaje !yakake haka,yau bbu my feedo sai fiddausi atsaye?
Ina soyayyar dasu bbu d’aga k’afa?kazauna tausayinta kome yasa ka kasa biyan bukatarka gaka da fitina ,aini nazata an rugada an wuce wuri….dallah dakata ba dariya nazo kamunba “zaka wani tasani gaba kanayi harda rik’e ciki ,kabani shawara ya zanyi pls?”
Tabe baki Abdallah yyi had’e da cewa abinda zakayi yawuce ka yi Mata ta k’arfi ko kasa Mata k’wayoyi a drink feeling yataso Mata….
Girgiza Kai Hafiz yyi had’e da cewa duka bazan iya ko d’aya ba.