AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

P2
….Suna zuwa gidan suka haura ta katanga , yyinda yarima yasanar da yaronsa yatsaya tsakar gd shi yashiga dg ciki.
D’akin dake bud’e ya kutsa Kai ciki Yana dariyar mugunta….turus yyi ganin dakin wayam bbu alamar da mutane aciki sbd yahaske ko Ina da fitila”da sauri yafito Yana cewa taf lallai meke Shirin faruwane?”
Yallab’ai lfy dai ko?”
Cikin takaici yace tabbas akwai Wanda yasanar da ita da iyayenta zuwa na “amma muddin Ina raye akuma garinnan take to dole burina yacika…
Fuuuuu suka fice dg gidan rai bace.
Zuwa safiya gari yakarad’e riyanatu sun gudu da ummanta,wasu na tausayinsu wasu na tsinewa yarima sbd dalilinsa suka gudu…
Koda baffan riyanatu yaji wanna an lbari da kanin ummanta hankalinsu yatshi matuka sunyi nadamar zamansu garin da me garin garin baya adalciko kad’an, D’ansa na bata d’iyan jamaa amma baya mishi mgn ko tsawatar Masa…
#
K’amshine daddad’a ke tashi a parlourn na turarukan wuta dna air freshener”kallo daya zakama parlourn kasan mamallakansa naira tana kuka agurinsu yahadu ya k’awatu.
Wasu masu aikine suka shigo da warmers ahannunsu suna jerawa akan dining table din dkae cikin parlourn…wata hamshakiyar mace ce ta fito cikin shiga ta alfarma tana yauki had’e da takun izza,Yar kimanin shekara45 xuwa 47 .”
Cikin girmama had’e da rawar jiki sukace ranki yadad’e ankammala! Cikin bada order ta yatsina fuska tace Ina fatan komai very need sbd kunsan my son akwai k’yankyami,Dan munyi waya yanxun yace sun kusa k’arasowa.
Wacce ake Kira da hassu tace insha ALLAH komai yyi lfy yadda kikeso hjy…kafin tayi mgn sunji karar motoci da alamar Wanda ake ma liyafar ya iso, da sauri ta sallamesu, sannan ta nufi kofar fita dg waiting parlou tana wani murmushi Wanda bansan ma’anarsaba..
Gaba d’aya body guard d’insane suka Fara fitowa,shikuwa ogan nasu be fitoba.wata haddiyar motace dake tsakkiyar motocin ita aka bude gidan baya…wani fitinan nan kamshi me saka nishadi yafara gauraye Gurin, kafin santala santalan kafafunsa su bayyana sanye da takalmi sawu ciki . ahankali ya ida fitowa…
Wow Masha ALLAH nafad’a azuciya ta sbd ganin guy din hmmm ALLAH yyi baiwar halitta agun kyakykwa wane ajin farko dogo fari…suit ne bak’ak’e ajikinsa Wanda suka haska farar fatarsa da agogo baka daure atsintsiyar hannunsa ,yyinda kansa yasha gyara sai salk’i yake lolx..
Fuska bbu walwala yarika amsa gaisuwar ma’aikatan gdn,daketa aikin gaidasa,sannan cikin takunsa na isa yake tafiya tamkar bayason taka qasa..tuni guard’s d’insa suka Fara kokarin binsa .
da hannu yyi musu alamar ah ah hakan yasasu dakatawa dg binsa..
Adede step din da zai sadasa da waiting parlou yahadu da momynsa… murmushi yyi hade da nufarta Yana cewa i miss you my lovely mom..
Dariya tayi ta rungumesa suka shige cikin parlourn.;;;
Kan 2 seater yazauna Yana k’arewa parlourn kallon yaushe gamo”kafin su gaisa da mom Yana tambayarta abbansa.
“Tace Yana hanyar isowa gdn”
Tamkar wani yaro ya shagwabe fuska had’e da cewa gsky Abba yadena ji Dani gsky mom ,sbd ai dayazo tarata ko yajira zuwana agd in bezo air port ba”
Murmushi tayi hade da cewa hmmm my son yanxunfa ka girma sai Shirin aje iyali kake amma kak’i barin shagwaba ko ?” To ai munatare dashi jiranka ,akamasa Kiran gaggawa a office shiyasa.
Had’e rai yyi hade da cewa Ni gsky mom Adena maganar na wani aje iyali dududu shekarata nawa daza’amun aure ne?” bacin kinsan ma zeenat din da kikeso ki auramun sai nan da sheraka 2 zata gama skul Kuma ake tada mgnar yanxun .
Girgiza Masa Kai tayi tace hakane ALLAH yakaimu lokacin ,yanxun tashi muje kayi lunch ko.
Agogon hannunsa ya duba yace NO mom bara nayi wanka tukum”Ina fatan komai yyi mun ?”kinsan bansan kazanta.
“Ahankali ta ce oh me hali baya barin halinsa”ABDALLAH komai yyi need kaje kaduba , shiyasa ma nasaka harira ta nemomun mai aikin dazata ruk’a kulamun dakai kafin kayi aure tunda ni Ina office…kafin yyi mgn abbansa yyi sallama.
Da sauri yatashi Yana murmushi ya rungumesa, yyinda abban ke dariya Yana d’anbuga bayansa Yana cewa my son Kai baka girma ko?”
Shima dariyar yyi yace eh Mana tunda banida kani ko yayaba, yafad’a yana sakin abban ,yyinda mom tayi tamkar bata parlourn.
Abban ne yakalleta Kai Duke yace hjy nadawo ,cikin ko inkula tace ok Ni zanshiga ciki kafin yarona yayi wanka ,akwai inners dina dake a toilet ka wankesu su fita kasan na jiyama basu fitaba ….fuska asake Abba yace to ,bacin wanki bbu aikin dazanmiki?”
Iya nan ABDALLAH yaji yabar parlourn Yana huci.
Tunanani yake azuciyarsa ,dama har yanxun momynsa Bata Dena juya abbansaba ke nan?” Sbd tsawon shekara4 kenan baya k’asar Yana ingila,Ashe bata bariba…wani mugun tsaki yaja afili yace bazan iyaba saina Miki mgn harda abban shima.
Wai meke faruwa ne,miyasa take Masa haka??”shikuma Yana binta tamkar shine matar itace mijin ,cikin bacin rai ya isa part nasa.
Duk yadda ma aikatan suka yi kok’arin gyara part d’in Amma shi be masaba sai ma yaja tsaki rai bbu Dadi yyi wankan yasaka jallafiyya Fara had’e da feshe jikinsa turarukan sa .yanufi masjeed sbd time din sallar azuhur yyi…
Su riyanatu kuwa byn sun sauka dg acab’an dayakaisu Tasha ,bbu bata lokaci suka hau motar kaduna.saida sukayi tafiyar awa6 amota tukum sannan suka iso kasancewar dg garinsu zuwa nan da nisa sosai.
Tun a Tasha suke raba ido abunka da Wanda ke bako, riyanatu ta tambayi wasu dattijai inane unguwar kawo?” Su bak’i ne….
Nan akasamu mai adaidai aka fad’a Masa inda zai kaisu .
Har kofar gidan zuwaira me abinci aka aje su,sbd tayi suna agarin duk asanta shiyasa basu wahalaba.
Amatukar gajiye da yunwa suka yi sallama asoron gidan da jamaa keta cin abincin Rana da alokacin befi karfe3 ba na Rana.
Sai kallon su ake ganinsu da gana d buhu ansan matafiya nesu , sannan Kuma kauyawa dukda ba irin kauyawannan neba sosai sbd riyanatu tayi boko akauyen su.
Cikin sakin fuska suka ida shiga ciki da sallama .
Ko da zuwaira tagansu tuni taganesu ta amsa da faraa tana musu maraba.
Nan taimusu iso ciki suka ci abinci sukasha ruwa , sannan suka yi Sallah.
Zuwaira tabasu wani daki karami agdn tace su saka kayansu suyi wanka su huta ,inta gama sallamar customers sunyi mgn .
Amsawa sukayi suna mata godiya da wannan karamcin data musu..,,,,
Ana idar da sallar yanufi gd.
Part d’in mom yanufa fuska bbu walwala yyi sallama can ciki ciki.
Mom ta amsa…..
Share pls
BY MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
???? AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
Mmn fareesa
P3
“””Mom ta amsa tana kallonsa had’e da mik’ewa tsaye tana cewa kada womy son?”
Muje ko kaci abinci,fuska bbu yabo bbu fallasa ya amsa da to mom muje.. dining area suka nufa a tare.
Zama sukayi kafin tafara serving nasa.
Haka yake cin abincin suna fira da mom jefi jefi yake mgn dan shi mutum ne dabaya son yawan surutu da mgn,saidai fa ta lura D’an nata na cikin damuwa Amma taki tambayarsa damuwarsa .
da haka ya ida cin abincin ya Mike had’e da cewa mom bara naje part dina munyi da Hafiz zaizo yanxun…katse sa tayi dacewa atsawace hmmm kana nufin Hafiz yafini k’ima a gurinka ,Ina matsayin mahaifiyar ka har wani banxa yafini daraja agunka ,shekara4 bamu haduba Amma baza ka zauna mu gaisa muyi firar yaushe gamo…iye?”nifa banason abotarku da shegen yaron nan Yana fama da tsawo uwa daran Sallah mitss taja tsaki hade da yin kwafa..
Mamaki abdallah keyi azuciyarsa ,shidai yasan Hafiz bashida wani aibu ko wani mugu hali ,hasalima tun tuni Hafiz naba shi shawarar kwarai da fad’a Masa gsky Amma yalura mom batason abotarsu… K’arara take nunawa Hafiz k’ii.. Wai badakai nakeba ?” Kamun shiru!
Kafin yyi mgn abbansa yashigo parlourn da sallama, Abdallah y amsa Yana murmushi had’e d hugging abbansa Yana cewa Abba bara naje part d’ina nadawo mu sake gaisawa.
Sannan ya juyo Yana kallon mom ke musu wani kallo mai wuyar fassara yace pls mom i am really very sorry! bejira amsartaba yafice Yana tambayar kansa miyasa yafison abbansa da tausayinsa akan mom bacin ance duk d’a yafison uwarsa akan ubansa..