AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Jin ana knock yasa tayi saurin daukan post nata ta fice.
Ahankali take tafiya har ta iso waiting parlour inda Abdallah yakeda zugar abokansa”wadanda sukayiwa riyan k’uri da ido “yyinda gogan be kalli inda takeba dukda yanajin sautin Karan takalminta,hankalinsa nagun waya”
Masha ALLAH Hafiz ke cewa a zuciyarsa sbd da ace banan yagantaba to wlh bazai ganetaba inba muryarta yajiba.
Da k’afa ya zunguri Abdallah dashima yyi masifar kyau cikin dark blue na suit da takalmi da agogo duk dark blue ,sumarsa Tasha gyara sai salk’i take…
Cikin kak’aro murmushi yad’ago sbd bayason friend nasa su fahimci wani Abu,in ancire amininsa Hafiz”Dan sake ware ido yyi sbd ganin wata shuwa Arab din yarinya,yyi saurin dubar Hafiz,shikuwa yad’aga Masa gira”alamar eh itace”cike da basarwa yamike tsaye Yana wani shu’umin murmushi… adedenan cpt suleiman yace wow AK ka iya zabe’ ammafa batafi iftihal d’ina ba komai(INA TARE DA ITA ) kallonsa AK yyi had’e da cewa dubadai”sannan ya dubi riyan data ida isowa”cikin murmushi yace gsky baby kin shanyamu da yawa”cikin dakiya riyan ta shagwab’e fuska tace to bana ce muje basai ammun make up d’in ba kace sai anyi….hmmm kincika rigima wlh ai in ammiki zakifi kyau ko?”yafad’a Yana murmushi had’e da mik’a Mata hannunsa”yace ga friends nawa ku ki gaidasu,cike da tsoro ta aza hannunta kan nasa, sannan tace hii!sannunku da zuwa!gsky Ina fushi daku tunda sai yau kuka tab’a visiting namu”
Baki bud’e Hafiz ke kallon wannan dirama ta riyan da Abdallah sbd tayi bala’in basa mamaki riyan.
Duk murmushi sukayi ,kafin Hafiz yace laifin mijinkine dabe gaiyaci wasuba a bikin naku saidai sukaji labari yyi aure…
Harararsa Abdallah yyi had’e da cewa “laifinka daiko”muje kada muyi latti”shagwab’e fuska riyan tayi had’e da cewa nidai gsky da nisa kafin mu isa get kadaukeni….. hhhhhhhhhhhhhhhhhhh???????????????? duk suka saka dariya” sir Aliyu (nida d’alibata) yace gsky AK kuna lokaci kaida madam, wannan irin shagwaba da kayi Mata…cikin dariyar yak’e Abdallah yace to badole na shagwabata ba”yafad’a Yana muntsinin Riyan….da k’yar da daure batayi ihuba.
Ahankali Hafiz yace to ai tunda kashagwabata ko kunyarmu bakwayi saika dauketa ko”kallon gargadi Abdallah yyi Hafiz da riyan,saima Hafiz yyi tamkar bejiba.
Mlm riyan kuwa sai ta turje ita adole sai ya dauketa,yyinda hafis keta danne dariyarsa sbd yasan mutumin ya k’ulu”
Janyota yyi jikinsa suna kokarin ida fita dg cikin parlourn….wani yarrrrrrrrrrrr!yaji ajikinsa Amma sai yadaure,yakai bakinsa daidai saitin kunnenta”wata irin kasala riyan taji ajikinta”cikin masifa yace ke wlh ko yi tafiya da kanki ko ki kwana yau Gurin karnuka nizaki saka nayi dakon wannan k’azamin jikin naki.
Ita kuwa shiru tayi sbd ta k’udurta aranta saifa ya dauketa kodan zeenat da mom suji haushi sbd tasan suna a compound din gdn jiran fitowarsa.
Saurin janye jikinta tayi dg nasa tace shikenan nibazan jeba”Hafiz dake bynsu yace haba AK miye aciki?
Duk yadda kke sonta sbd ganin mu kak’i daukanta”
Abdallah jiyake kamar yarufe Hafiz da suka Amma bbu hali.
Yarima Ashman datun d’azun beyi mgn ba sbd kasaita “ahankali yace towai miyasa baza ka dauketa ?immune munyi gaba a mota mujiraku sai muwuce ko”
Hafiz yace hakane ai zai dauketa ma sbd aishi yashagwaba ta”
Cikin bak’in ciki Abdallah ya Suri riyan Yana murmushin yake,yyinda ita Kuma ta aza hannuwanta ta zagaye wuyansa dasu,tana murmushi…. adedenan Hafiz yyita musu pics .
Abdallah yyi mamakin jinta sakwab,azatonshi zatayi nauyi,sai hararan Hafiz yake yana Masa alama da ido yabari”
Amma yaki bari,shikuwa Abdallah shikadai yasan hukuncin dazai yankewa riyan .
Haka yasabeta har suka iso campaund din gdn….atare mom d zeenat suka tashi tsaye…
Da sauri mom ta nufi gurunsu.
Tun dg nesa….
Share pls
BY
MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
????AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by mmn
Fareesa
Dedicate to all my fans????????
Kuyi hakuri narashin posting d’ina inada uzurirrikane ,masu kirana dan jin lfy ta nagode sosai wad’an da banma reply ba a what’s app pls kuyi hakuri”banida time nagode sosai…
p 22
“”Tun dg nesa riyan ta hango su mom sunmike tsaye itada zeenat kowacce fuska da mamaki… duk’ar da Kai tayi ,tana dariya kafin ta d’ago taga mom gab dasu fuskarta daure,yyinda friends nasu AK ke kallonta”
Tana isowa tace kai
Abdallah meye haka nake gan….kallon da Abdallah yyi Mata da ido had’e da nuna Mata abokansa yasata yin shiru,ta k’akaro murmushn takaici d bak’in ciki”
Ita kuwa riyan Yana sauketa ta juya bayanta ta Dena kallon mom tana sauraronta taji dame tazo?”sai taji tayi shiru”
Mom kuwa dubar riyan data juya baya take , azuciyarta kamarta rufeta da duka ,ta daure tace y’ata yayadai kin juya baya?” Kushiga mota Mana”
Murmushi riyan tayi had'e da juyowa tace ok mom sai mundawo "ta fad'a had'e da dagawa mom hannu "sannan ta fakaici idon kowa ta yiwa zeenat gwalo wadda dg nesa tana kallonsu..
Hannunta Abdallah yakama yabude wata mota me kyau yasakata,kafin yashige sauron abokansa surufa Masu baya”
Mom ta bisu da kallo har suka b’acewa ganinta”ahankali tace hmmmm ALLAH yasa ayi taron lfy kafin komai yazo karshe kilama bazaki Kai WATA SHIDDA ba zansaka yasakeki….ah ah kada kiyi haka kawata ai plain namu bazai tafi daidaiba kibarta kawai cewar hjy ikilima tana dafa kafad’ar mom, yyinda zeenat ke kusada da ita tana hawaye…
Inmukayi hakan tana gdn bbu komai kuwa?” Cewar mom tana kallon hjy ikilima.
Yo eh Mana”
Bara kiji kawo kunnenki”nan ta rad’awa mom wata mgn suka shek’e da dariya.
Kafin mom ta dubi zeenat da mamaki tace lfy dai ko kike,Kuma miyasa bakije gun taron ba??”
Hmmm hjy hafsat rabu da marrar tunani wahalallar banza,ita a haukanta kishi take shiyasa take kuka ko”dubarta mom tayi had’e da kashewa hjy ikilima ido tace sorry kinji y’ata kidai Bari yarabu da ita dolensa ma ya aureki… murmushi zeenat tayi had’e da cewa yauwa mom amma Dan ALLAH kada kuyiwa abdl….ke rufemin baki wuce muje….shiru zeenat tayi had’e da bin byn hjy ikilima dkewa mom sallama.,,,,,
Bangaren Abdallah da riyan kuwa, byn sun shiga mota riyan ta matsa tayi nesa dashi" Abdallah kuwa yaso yyi Mata rashin m amma ganin driver najinsu sai ya k'yaleta kawai Yana murmushin yake had'e da matsawa gab da ita yakama hannunta ya matse cikin nasa gam Yana Mata mugunta...ita kuwa daurewa kawai take tamkar tasaki ihu sbd azaba"
Matsowa yyi da kansa kusada fuskarta”cikin sweet voice insa yace hii baby! akwai zafi?” ko nakara ?” banza tayi dashi tama rufe ido”murya k’asa k’asa yace zanbaki mamaki yarinya sbd kin sakani yin dakon wannan k’azamin jikin naki ….niwai Zaki ce nayi dakonki ko?”sbd gaki jarababbiya kina son had’a jiki Dani to kibari innarabu dake saiki auri jarababbe D”an uwanki kutaru kuyita jarabarku” “hmmm inhar mukashiga Gurin nan kikamun iyayi wlh muka koma gd Zaki gane bakida wayo….saurin janye fuskarsa yyi sbd ganin anyi parking….
Driver nayin parking yafice dg motar”
AK Yadubi riyan da idanunta ke rufe”
Yace keeeeeeeeeee!
Bud’e idanunta dasukayi jajir tayi ,sbd bak’in cikin kalaman da Abdallah yagaya Mata San ranshi..
Batace komaiba ba tana sauraronsa”
Cikin ko inkula da yanayinta yace abinda zan fad’a Miki”shine kikama kanki kada kisake kimana hausa ko body language,kinji ko bakijiba?”
To “ta fad’a atakaice”
Fitowa yyi ganin anbude Masa motar”Hafiz ne ke murmushi Yana cewa haba abokina wannan soyewa haka ,kamar ba gida d’aya zaku kwanaba “ai yakamata kufito hakan!yo wannan kana ma iya zuwa office kuwa?”sbd soyayya,ainas…mugun kallon da Abdallah yyi masane had’e da take Masa k’afa yasashi yin shiru Yana dariyar tsokana….saidai fa dariyar tasa ta tsaya sbd ganin fuskar riyan wata iri ba kamar d’azunba…. azuciyarsa yace AK ne kuwa yayimata wani Abu”
Hannun riyan yakama had’e da rungumota tuni camera ta Fara haskasu ,kowa na Gurin cewa yake Masha ALLAH sbd ganin couples d’in “ita kuwa riyan binsa take suna tafiya cikin nutsuwa Amma ranta fal bak’in ciki ta dau alwashin duk radda yasake yanemi wata alfarma gunsa zata basa mamaki…