AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL
AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tuni MC yafara bayanin abinda yatarasu anan sbd ganin AK da riyan sun zauna ga abokansa abayansa" yyinda Abba da manyan mutane ke zaune gefe da sauran jamaa ,byn annatsu aka Kira AK yazo sbd ya yanka farin k'yalle"tashi yyi tsaye had'e da mik'awa riyan hannunsa ta kama ta tashi ,saita noke kafad'a alamar shagwaba.... azuciyarsa yace nafi iyawa"rank'wafowa yyi da kansa yace inhar kikbari nabar nan Baki biniba zanbaki mamaki"murmushi tasaki had'e da kama hannunsa ta tashi tsaye....tafi da sowa mutane suketayi sbd kowa azatonsa suna son juna ne,yyinda Abba keta murmushi sbd yazata ko Abdallah yafara son matarsa ganin yaduk'a azatonsa rarrashinta yake...
Ahankali riyan ta aza hannun ta kan na Abdallah byn sun isa Gurin ,nan ya yanka aka hau tafi sannan aka hau ciye ciye da Shan abin sha ,gefe guda kuwa music ketashi,riyan kuwa bataci komaiba ba” saidai Abdallah yasha drink kawai”byn duk su Abba sun fice akayita matsowa kusada su ana musu ALLAH yasa alkhairi !Koda riyan ta lura da mutane sunyi yawa saita sulale ta fito ta nufi Gurin motar dasuka zo” da sauri wani guard yabude Mata tashiga”saidai hafis duk Yana lura da ita da sauri yabiyota yaga Ina zata tafi” Koda yaga tashiga mota ,gun motar yanufa…turus yayi sbd ganin tana kuka harda shashsheka….da sauri yace riyan lfy kuwa?miye abdallah yyimki kike kuka haka?”
Yakusa minti5 tsaye Yana Shirin tafiya ma sbd ganin Taki kulasa…yaji tace yah Hafiz meyasa Abdallah besan darajan d’an adam ba?
Ajiyar zuciya Hafiz yyi had’e da cewa Mike faruwa ne Dan ALLAH?
Cikin kuka tasanar da shi kalaman da Abdallah yaga yamata”ta kare da fad’ar to Mike nufinsa?ko yaan zargina ne kome?”
Ya isa Dan ALLAH riyan’kiyi hkri kibarwa ALLAH bkinji sannan kada kikoma nuna Masa ranki na b’aci inyayimiki Abu ,kinuna ko inkula insha ALLAH zai bari Kuma Dan kicigaba da addua had’e da hakuri ni inaji ajikina akwai wani babban al’amari dazaifaru gaba kad’an riyan kinji….
Shiru tayi tana nazarinsa”ajiyar zuciya tayi had’e da cewa nagode sosai yah Hafiz”
“Murmushi Hafiz yyi yace ba komai ki goge hawayenki ki nutsu kada yagane kinyi kuka kinji bara na koma gurinsu sbd Kinga anata fitowa da alama antashi….
Abdallah kuwa be lura da tashintaba “sai gaisawa d jama’a yake harsuka rage kafin yalura Bata nan”
Tab’e baki yyi alamar ko ajikinsa ,tashi yyi ma Yana neman Hafiz be gansaba, sallama yadunga yi mutane yyinda yaketa yan waige waige ko yaga riyan Amma be gantaba Kuma gashi bega hafis shimaba,tsaki yaja had’e da cewa ita tasani matsalar ta”
Fitowa yyi su CPT SULEIMAN da SIR ALIYU abayansa suna cewa Wai AK Ina sahibar takane?”tabarka Kai kadai…cikin kak’aro karya yace eh tana mota “waya take sbd ciki bbu network… yafad’a yanajin haushin yau yyi k’arya sbd wata can bacin yatsani yin k’arya ko mak’aryaci arayuwarsa… adedenan Hafiz ya iso gunsu Yana cewa AK ga riyan canfa amota tana jiranka…
Ajiyar zuciya yyi sbd jin maganar Hafiz tazo daidai da karyarsa.
Bece komaiba ya yimusu godiya had’e da sallama kowa yashige motarsa…
Bud’e masa mota akayi yashiga cikin isa had’e da kasaita, yyinda riyan ko inda yake Bata kallaba,shima haka sai latsa wayarsa yyita yi har suka iso gd..
Ana gama parking riyan ta bud’e kofar kusada da ita ta fito ,tanajin Abdallah nacewa ke jirani…tayi Masa banxa.
Afusace yafito ,Amma tayi Masa nisa,kamar ance ta juyo taga yabiyo bynta sbd azatonta part d’in mom zai nufa.
Da sauri ta nufi part d’in su,tayi saurin shigewa bed room d’in ta ta saka key,ta jingina da kofar tana
Sakin ajiyar zuciya….
Bam !bam!!bam!!!
Abdallah kedukan kofar kamar zai balle kofar…
Riyannnnnnnn!
Nace ki bud’e kofar nan ko”
Inkika bari na kirga ukku Baki budeba wlh saikin sani kinji na rantse…..
One!twoo!!!thre…..
Share
BY MMN FAREESA
????????????????????????????????????????
????AUREN WATA SHIDDA????
????????????????????????????????????????
Story & written by
mmn fareesa
p23
One !two!!three!!!kafin yarufe bakinsa ta bud’e kofar tana kallonsa Bata ce komai ba”afusace yace gsky kin ceci kanki Dan wlh dabaki bud’e ba nidake ne agdn nan”oya kije kiyi magrib “inkin idar kije bed room d’ina kayan wanki na nan adaure ki wankesu,hukuncin sani dakon k’azamin jikin ki….. murmushi tayi had’e da cewa to shikenan”tafad’a tamkar bataji haushin sakata wankinba”
Cike da mamaki take dubanta harta juya ta koma cikin d’akin”tab’e baki yyi had’e da nufar bed room nasa yyo arwalal magrib yanufi masjeed”
Bedawoba ba sai byn isha’i yawuce part d’in mom”
Zaune take tana kallon TV, murmushi tayi had’e da amsa sallamar sa”byn sun gaisa ta Masa fatan alkhairi kafin ta gabatar Masa da abinci”
Byn yagama dinner d’in suna fira da mom Abba yashigo rik’e da jarida a hannunsa ya zauna gefen mom suka cigaba da fira da shi har kusan 9:35pm kafin AK yyi musu sallama yafito, yanaso ya kwanta da wuri sbd gobe karfe 8:am zaifita office”
B'angaren riyan kuwa byn ta idar da sallar ta je ta duba tulin kayan wankin sunkai set 16 ,danba basuda datti"wani kunci taji da bak'in ciki aranta amma data tuna INNAL LAHA MA'ASSABIRIN da Kuma INNA MA'AL USRU ISRAH...sai taji zuciyarta tarage zafi"wani tunani tayi da sauri ta koma gefen dayake motsa jikinsa ta dakko washing machine ta saka kayan ya wanke su tas Bata sha wahala ba"duk da atsorace take gudun kada yazo yatarar,Bata idarba sai 8:52 pm ta nufi Gurin hanger ta shanyasu byn ta maida washing machine d'in gunda ta d'auka.
Bed room nata ta koma ta yi isha’i had’e da sha’fa’i da wuturi “taci abinci ta kwanta cike da kewar ummanta…
Abdallah kuwa be shiga bed room nasa ba Saida yaje yaduba yaga ta wanke kayan tukum…saikuma yaji tausayinta,wata zuciyar tace yanzun in y’arka ce aka yima haka zakaji dad’i?”
Shiru yyi Yana tunanin tunda riyan ta zo gdn yake mata rashin kyautatawa,sai yaga be kyautaba duk da wani Time din ita keja ana Mata hakan.amma insha ALLAH zai Dena takurata har lokaci yyi yarabu da ita ya huta, kafin yyi ajiyar zuciya ya koma bed room nasa “ya wuce toilet ,da kansa yahad’a ruwan wanka kafin yyi…
Bayn ya fito yashirya ya kwanta….
Washe gari tunda wuri riyan ta tashi taje ta gyare masa ko Ina ta had’a Masa ruwan wanka kafin ta fito dg toilet d’in”ta dubi agogon dake jikin bango taga 7:14 am “afili tace anya ba8:am bane zai fita office?”
Nufar gadon tayi ta dubesa Yana kwance atsakkiyar gadon ya rufe jikinsa da bilencat,fuskarsa ce kawai ake gani”k’uri da ido tayimasa azuciyarta tace Masha ALLAH mutumin nan badai kyauba”matsalar sa girman Kai… ahankali ta Kai hannunta kan pillow tad’an bubbuga tana cewa katashi kada ka makara”
Yakai kusan 2 minit kafin yasoma motsa golden eyes nasa,harya waresu akan agogan bangon d’akin”tsaki yaja had’e da dubar riyan wacce kanta ke duk’e tanajiran yafara Mata masifa”shine Dan wulakanci sai yanzun Zaki tayar Dani?”yaushe harnayi wanka na gaidasu mom har natafi office?”
Bata dubesa ba tace kayi hakuri ,yanzun ma nayi kasadar tadakaine Amma kaje kayi wanka lokaci na tafiya”harara ya gallamata dukda ba ta kallon sa,jin motsin zai tashi yasata saurin juyawa da nufin fita”oh bazama kijira kitayani shiryawa ba ko?”shine Zaki give”baat juyoba ta tsaya sbd batason ganinsa help nercat”suit Zaki fito mun dasu “to saika fito”banza yyi Mata yadauki towel yashige bathroom d’in….
Ajiyar zuciya tayi had’e da nufar wardrobe ta fito Masa da suit red ta feshe su day design na performance nasa,ta curo Masa takalmi da agogo bak’a k’e ta duk’a tana goge takalmin sbd gudn masifarsa duk basuda k’ura to tasan shi mai tsabtane sosai… adedenan yafito daga toilet d’in”sai yaji ta kyauta sbd yanason tsabta”fuska bbu yabo bbu fallasa ya ce fitomun da brief case d’ina!to tace byn ta aje takalmin gefen mirro, yyinda yacigaba da sha mansa,harta kawo Masa”had’e da laptop nasa”ahankali tace gashi…tsaki yaja had’e da cewa Wai miyasa bazaki iya kiran sunana ba ne?”saikace Baki saniba “karki Bari nakoma Miki mgn”kayi hakuri bara najiraka aparlou kasaka kayan !Bata jira amsarsaba ta fice dg bed room d’in..
Cire towel din yyi, sannan ya ida shafe jikinsa yadauki kayan cike da mamaki yadubesu jin suna k’amshi wato ita tasaka turaren kenan”afili yace bbu laifi ta fara wayewa! Kafin yasaka kayan agaggauce yagyara sumarsa yafito da agogo ahanunsa”tana ganinsa ta shi vta karb’i agogon ta d’aura masa Yana duba wayarsa harta idar,kallonta yyi up& down yaga doguwar riga ce fited gownt maroon ajikinta,da wata huta baka tayi acuci…dagowa tayi suka had’a ido…saurin kauda kansa yyi cikeda basarwa, ahankali tace amma ko tea ne zakasha ko?