AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

AUREN WATA SHIDDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallonta ta maida akan riyan dake hawaye”cikin hantara da tab’e baki tace to ke asuwa kike kuka?”

Girgiza Kai riyan tayi,sbd yau taji kwata kwata yau bbu tsoron mom atare da ita.

Kai tsaye tace ,Ina kuka sbd Ina tausayinsane dakuma tausayin wasu mutane na cikin duniya dake zalinci da cin Amana basa tuna ranar da ALLAH zai kamasu ,yyi musu hukunci,wato a…..ke dallah rufemin baki!dak’kiya!uwar me kika sani,dazakice zakiyawa wani waazi….hmmm kiyi hakuri hjy Ni bance Miki inawa wani waazi ba… mittsss mom taja tsaki hade da cewa kikulamun da yaro na canxo kaya mutafi asibiti ta fad’a had’e da shafa kan Abdallah ta fice…

Abdallah kuwa duk abinda sukeyi yanajinsu da tambayar mom data Masa, sannan da amsar da riyan ta Bata yatsaya Masa arai yakuma yiwa amsar tata fassarori da yawa,saidai Kash bazai iya mgn ba ,balle ya tambayeta dalilin bawa mom wanna amsa…

Mom na fita”da hanxari riyan ta d’auki d’aya dg cikin wayoyin Abdallah dake kan bed side dirowa” talalubo number in Hafiz sbd tasanar Masa”aganinta Hafiz be kamata ace besan meke faruwa ba” tasaka Kira bugu2 yad’aga Yana cewa my man….bashi bane riyan ce…nan tashiga sanar dashi abinda yafaru…cikin tashin hankali Hafiz ke ta salati had’e da cewa dama Ina hanya bara na k’araso….ah ah yah Hafiz kabarshi,yyi saurin cewa meyasa?
Kallon Abdallah tayi haryanzun idonsa arufe…abinda Bata saniba! duk yanajin ta ,yaji dad’in sanarma da Hafiz datayi ” cikin inda inda tace um muhade a hospital sbd can zamu!ok yace had’e da datse Kiran domin yagane cewa cikin2 dole guda ko mom ta hana asanar Masa ko Kuma tana Gurin ta nuna bataso yazo…
Riyan kuwa tak’i fad’a Masa mom ce taha na sbd ganin Abdallah k’ila yanaji tasan Kuma bazaiji dadiba….saurin aje wayar tayi sbd jin motsin za’a shigo.,,,,,,

Mom ce da Abba,abayansu ya'u direba ne,cike da tausayawa suka Kama Abdallah suka fito da shi sbd asakashi mota,juyawa riyan tayi sbd taje ta sako hijab tabisu"mom ta dubeta had'e da cewa Ina zuwa?"

“Xanje nasaka hijab be”ta fad’a atakaice.

Baza kijeba , sbd zuwanki beda wani amfani agaresa ko agaremu,Bata jira amsarta ba ta fice dg d’akin”

Shiru riyan tayi had’e da Zama ,tana mamakin halin mom”kafin ta d’auki wayar Abdallah tasaka number in umma ta Kira.

sallama umma tayi ,muryar riyan taji”murmushi tayi tace oh riyan kwana2 ya gdn?nan suka gaisa cike da alhini riyan ke sanar da umma lalurar datashafi Abdallah..

Cikin tausaya had’e da damuwa ,umma ta jajanta Mata had’e da cewa insha ALLAH acikin satin nan zatazo taga Abdallah d ajikin,nan suka Yi sallama umma nata kwantar Mata da hankali.

**** **** ****
Hafiz byn sun gama waya da riyan,Kai tsaye asibitin da amminsa ke aiki ne yanufa sbd yasan da wuya Suki zuwa can sbd tafi kusa dasu Kuma asibiti ce maitsada da kula.

Office din ammin yanufa ,tana duba patient,amatsayinta na babbar likita k’wararra”da mamaki ta amsa sallamar sbd basudade da rabuwaba yazo gaisheta”saidai yanayin data gansa tasan tabbasa bbu lfy! agaggauce ta sallami patient d’in”kafin ta dubesa tace lfy dai ko Hafiz?”

Cikin damuwa had’e da tausaya wa ,yashiga yimata bayanin matsalar Abdallah.

Kafin tayi mgn anyi Knocking”

Yes “kawai tace,wata nurse ta shigo had’e da cewa Dr kije emergency da gaggawa anason ganinki sbd ankawo wani patient Kuma doctor’s da yawa akeson sutsaya akansa!

Ok kije ganinan zuwa”cewar ammin (Dr naja’at haruna)ta fad’a had’e da mik’e wa tsaye tasaka farar riga saman hijab nata ,kafin ta dubi Hafiz tace bara naje k’ila Abdallah ne.

Tashi yyi hade da cewa to mom muje nima na gansa”

Atare suka fito har zuwa kofar da zata sadaka da shiga emergency d’in… adedenan suka Sami Abba da mom had’e da ya’u direba, suna Kai komo” kallo d’aya zaka musu ka gano tsantsar tashin hankali acikin idanunsu….

 Gun Abba Hafiz ya nufa , yyinda ammi ta nufi ciki kawai,dukda ta lura da mom na Mata kallon sani ,Amma saita waske ta nunama batasanta,dukda cewar akwai abota mai k'arfi atsakanin yaronsu to Amma basu tab'a ganin junaba,dukda ita ammin tasan mom ce mahaifiyar Abdallah .

Rungume Abba Hafiz yyi Yana kuka tamkar karamin yaro”

Bubbuga bynsa Abba keyi cikeda da rarrahi yace kayi hakuri insha ALLAH abokinka zai Sami lfy “addua zami yimasa ba kukaba”cikin gamsuwa Hafiz ya d’aga Kai.

Gum mom ya isa ,ya gaida ita, had’e da Mata jaje”

Fuska bbu yabo bbu fallasa ta amsa,tana mamakin ya’akayi yasani?”kasna zuciyarta nace wa Anya waccen matar ba naja’at bace?

Da wannan tunanane tunanen takira hjy ikilima ta sanar da ita halin dasuke ciki”
Sannan suka zauna jiran fitowar doctors din dake kan Abdallah.

Hafiz kuwa office d’in ammi ya koma , yafito da wayarsa yakira layin Abdallah da riyan ta kirasa dashi yaji miyasa batazo asibitin ba.

Riyan dake zaune jugudum a parlou..taji wayar na ringing,dubawa tayi,ganin Hafiz ya sakata saurin d’agawa,bbu wani boye boye tasanar dashi mom ta hana, girgiza Kai yyi had’e da kashe wayar”

 #######

Kusan awa3 da wani Abu dashigar da Abdallah ,amma bbu wani Dr daya fito duk sub abba sunyi jigum jigum,tun safe ga shi har 1:saura.
Nan wasu doctors 2 suka fito suna sharce gumi”da hanxari Abba yanufeso har Yana tuntub’e”mom na Mara Masa baya
,Har suna had’a Baki Gurin cewa Yaya jikinsa?meke damun da?”

Girgiza Kai sukayi had’e da cewa ku kwantar da hankalinku,Dan ALLAH!yanxun zamuje muyi Sallah kafin mu ida bincikenmu “

Jiki asanyaye Abba yace to shikenan,kafin Yadubi mom cikin damuwa yace bara naje nayi Sallah,kiyi waya agd akawo wani abun bukata”

To “kawai tace,kafin ya fita”

Tana nan zaune Hafiz ya iso gurinta,Yana cewa mom Yaya dai jikin nasa?”

Cikin yatsina tace da sauk’i, had’e da cewa zaman me kake a hospital d’in nan?

Cike da mamaki azuciyarsa,yake sauraronta,Amma be nuna ba,sai yace na tsaya sbd naji yajikin Abdallah ne..Kuma nima ammina,wato mahaifiya ta anan take aiki..da sauri tace ko itace naja’at Musa ?”
Har zai ce eh ,sai kawai yatsintsi kansa da cewa ah ah itadai Dr naja’at haruna ta ke”

Ajiyar zuciya mom tayi ,wadda basan cewa hafis yajiba,tace ok inaga kamace.

Shikuwa Sarai Hafiz yasan ada da naja’at Musa take bearing ,byn abbansa yarasu ta maida da sunan mahaifinta ,wato naja’at haruna.
Sannan ya boyewa mom ne sbd besan miyasa take son sanin ammice koba amminceba gashi tasaki ajiyar zuciya to meke faruwa ne?Amma in hankali ya kwanta zai tambayi a mmi d’in.

Sallama yyimata akn xeje yyi Sallah.

Bayan awa3,hakan yyi Dede karfe 3:25pm, doctors d’in sufa fito sunata sharce gumi.

Da hanzari su Abba suka taresu,Dr naja’at ta cire eye glass d’in ta tace kusameni a office”Bata jira amsarsuba ta nufi hanyar office d’in ta da wani likita ,da alama ita dashi ne zasuyiwa su Abba bayanin ciwon dake damun Abdallah.

Babu Bata lokaci su Abba suka rufa masu baya zuwa office d’in.

Share

BY
MMM FAREESA
????????????????????????????????????????

???? AUREN WATA SHIDDA????

????????????????????????????????????????

Story & written by mmn fareesa

Wannan shafin nakine halak malak Queen minart???????? kiyi yadda kikeso dashi…

Not edited

P 25

“”Bayan duk sun zauna koya ya nutsu”kafin Dr naja’at ta Fara mgn kamar haka…da farko dai Alh inaso kuyi hakuri ku maida lamarinku ga ALLAH ta hanyar karb’ar k’addararku daya k’addareku da ita! sannan kucigaba da Masa addua sbd shi ciwo lokaci guda yake shiga jikin mutum ,Amma sauk’i ahankali yake zuwa ind….ya isa haka pls kusanar damu Mike damun yaron mune?”cewar mom dake kallon Dr naja’at dake musu bayani”Dr naja’at Bata kalletaba da dubi Abba dake kallon ta tace maganar gsky Alh bazan boye maka ,munyi iya bakin kok’arin mu zurfafa bincike naganin munsan meye ke damun d’anka “Amma amsar guda ce”cikin k’osawa mom tace meye amsar?”
Dr naja’at ta cigaba da cewa binkicenmu yanuna Mana cewa Yana cikin koshin lfy!abad’ini kenan”azahiri kuwa idanunsa kawai ke aiki ajikinsa, sannan abinda muka gane yanxun na damun shine jininsa Yana kok’arin yahau, Kuma zuciyarsa na bugawa.
Hakan Yana nuna alamar cewa yasaka damuwa aransa ne,Kuma munyi kok’arin shawo kan wannan matsalar…salati kawai Abba ke maimaita sbd tashin hankalinsa yakaru akan nada, yyinda mom keta kuka da surutai..
Dr kamar yadora da cewa duk asibitin da zaku kaisa indai tsakani da ALLAH zasu gaya muku to amsar d’aya ce da nan “sannan ayanzun abincinsa yakasance me ruwane sbd be iya motsa bakinsa balle har yatauna abinci”zamu rik’e sa sai zuwa gobe musallamesa”Amma dai yanada iyali ko?”eh yanada Mata ,cewar Abba kafin mom ta yi mgn yarugata.
Dr Kamal yace ok to yakamata tazo kusa dashi sbd Yana bukatar kulawarta amatsayinta na iyalinsa,tunda yanxun komai sai anmasa.,,,,,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button